huxubobin jumu’ah - home - wrapa jihohin arewa maso yamma guda bakwai (jigawa, kaduna, kano,...
TRANSCRIPT
Huxubobin Jumu’ah Game Da Zamantakewar Aure A Shari’ar
Musulunci
Qungiyar Kare Haqqoqin Mata Da Tabbatar Da yi Musu Adalci
Mai Laqabin (WRAPA) Nigeria Ce Ta Samar da wannan Littafi
A Qarkashin Shirin Inganta Dokokin Zamantakewar Iyali A Musulunci (IFL)
Talifin
Goni Muhammad Sa’ad Ngamdu
Shirin Tabbatar da Adalci ga Kowa (J4A) Ya Bada Tallafin Buga Waxannan
Huxubobi da Aiwatar da Gwajinsu
Maris 2016
ii
©Women’s Rights Advancement and Protection Alternative (WRAPA)
Nigeria, 2016
All Rights Reserved
No part of this publication may be reproduced or transmitted in any form or by
any means electronic or mechanical, including photocopying, recording or any
information storage and retrieval system, without permission in writing from
the copyright owner.
ISBN: 978-978-54653-4-1
Ahmadu Bello University Press Limited, Zaria,
Kaduna State, Nigeria.
Tel.: 08065949711.
E-mail: [email protected];
Website: www.abupress.org
iii
Qumshiya
Muqaddima...................................................................................
Godiya...........................................................................................
Gabatarwa......................................................................................
Rayuwar Mace Qarqashin Inuwar Musulunci...............................
Aure Da Gina Rayuwar Iyali A Musulunci...................................
Aure Shine Tsarin Da Allah Ya Yarda Da Shi..............................
Waliyan Aure.................................................................................
Waxansu Daga Haqqoqin Miji Da Mata A Musulunci................
Yiwa Wacce Aka Saki Kyautar Jin Daxi Da Xaukar
Nauyin Matar Aure.....................................................................
Reno Da Sharuxan Da Suka Kevanta Da Shi................................
Haqqoqin Mace Akan Waliyyinta.................................................
Ni’imar Da Ke Cikin Aure............................................................
Haqqoqin ‘Ya’ya Akan Iyayensu..................................................
Maza Da Mata...............................................................................
Saki Shine Ke Rushe Gidajen Aure..............................................
Yawaitar Saki Ce Take Lalata Rayuwar Aure..............................
Waliccin Mahaifi Nau’i Biyu Ne Na Yin Dole Da Na Izini.........
Savani Tsakanin Ma’aurata Da Hukuncin Adalai.......................
Shar'anta Aika Masu Hukunci Biyu..............................................
Hukuncin Cutar Da Mace Da yin Saki Asanadiyyar Cutarwa......
Rabon Kwana Da Adalci Tsakanini Ma’aurata.............................
Kyautar Kwana Da Sayar Da Shi...................................................
Bin Iyaye........................................................................................
Aikin Mace Da Matsayinta A Musulunci......................................
iv
Muqaddima
Kalmar ijbari da Malaman fiqihu (Malikiyya) suka yi amfani da ita
wajen ayyana mahaifi da ikon da yake dashi na aurar da 'yarsa qarama
kan dole, ta jawo mabambantan fahimta tsakanin malumma. Wasu na
fahimtar ijbari na nufin tilastawa; inda wasu ke fahimtar akasin haka.
Bisa wannan da la’akari da Hadisai na Manzon Allah (SAW) Malamai
suka karawa juna sani cewa, wasu ba su goyi bayan auren dole ba,
wasu kuma na cewa mahaifi na da Ijbar kan 'yarsa.
Bincike da tuntubar al’umma da Kungiyar WRAPA ta gudanar
a jihohin arewa maso yamma guda bakwai (Jigawa, Kaduna, Kano,
Katsina, Kebbi, Sokoto, Zamfara) sun tabbatar da cewa iyaye na
fakewa da damar uba mahaifi ta Ijbari su tursasawa ’ya’yan su mata ta
hanyar aurar dasu ga duk wanda su iyayen suka ga dama. A lokuta da
dama; ba tare da la'akari da cewa shi aure wani muhimmin abu ne
wanda xorewarshi ko wargajewarshi al’amari ne da yake shafar
ma’auratan fiye da kowa ba. Da kuma fahimtar cewa illolin dake tare
da wargajewar shi abubuwa ne dake shafar iyayen da ma'aurata,
harma da al’umma baki daya.
A gefe guda kuma, masana da masu bincike da mahalarta
tarurruka sunyi savani. Wani vangaren na ingantar da Ijbari bisa
dogara da ra’ayin wasu Malaman mazahib; bugu da kari suna kafa
hujja da cewar wannan matsaya yayi dai dai da koyarwar Mazhabar
Malikiyya wadda ita ake bi a Najeriya. Wani bangare kuma na ganin
cewa Ijbari bashi da tushe a Qur'ani ko a Hadisan Manzo (S.A.W) sai
dai ra'ayin Magabata (Fuqaha'u).
A cikin wannan yanayi muna fata za'a faxaxa bincike da nufin
cimma matsaya akan wannan al'amari. Tare da fatar za’a lura da
waxannan abubuwa: Na xaya cewar Shariar Musulinci an gina ta akan
manufofi da suka haxa da nufin gusar da barna daga al’umma da
kuma kawo musu fa'ida (Maslaha). Na biyu amincewa da abinda ke
gudana a tsakanin al’umma a yayin da muka tsinchi kammu a yadda
xaukaka anfani da damar Ijbari sau da yawa kan zama ana kare
v
maslahar xaixai ku ne savanin akasarin al’umma; koda kuwa hakan
zai cutar da yarinyar da akayi wa aure bisa wannan damar. Kungiyar
WRAPA tana murna da ci gaba da tattaunawa da karfafa bincike mai
zurfi akan wannan maudu’i tare da fatan nan zuwa gaba masana zasu
kai ga matsaya mai kara karfafa hakkin ma’aurata a zaman aure a
musulunci.
Bisanin haka Kungiyar WRAPA na nuni ga bukatar samar da
matsaya ta gaugawa da la’akari da halin da ‘ya’ya mata suke fadawa.
Saboda haka mu lura yayin xaukan ko wane irin mataki, kasancewar
’ya’ya amanar Allah ce a hannun mu. Iyayen ’ya’ya, malamai,
shugabannin al’umma da hukumomin xabbaqa addinin Musulunci na
da haqqin ganin an bi duk wata hanya da zata samar da mafita da
maslaha a kan wannan al’amari. Mussamman saboda la’akari da
rayuwar yara mata waxanda kan tsinci kansu a halaye masu muni a
yayin da aka aurar dasu a karanchin shekaru ko aka tilasta aurar dasu
ga wanda basu so. Allahu a’alamu.
vi
Godiya
Godiya ta tabbata ga Allah mai rahama mai jinqai. tsira da aminci su
tabbata ga fiyayyen halitta da iyalan gidansa da sahabbansa da
waxanda suka biyo bayansu da kyautatawa har zuwan ranar
sakamako.
Bayan haka, muna miqa godiya ta musamman da jinjina ga
asusun (Marc Arthur) wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa
tahanyar tallafi da taimako waxanda suka dace ga qungiyar cigaban
mata da kare haqqoqinsu, babu shakka wannan qungiya da haxin
gwiwar jihohin Arewa maso yamma guda bakwai sun cancanci yabo
da jinjina bisa ga gudunmawar da suka bayar don ganin aiwatar da
shirin nan na dokokin zamantakewar aure. Ba shakka wannan tallafi
ya haxa da xaukar nauyin samar da kayan aiki da qarfafa gwiwa
wanda hakan ba qaramar gudunmawa ya bayar ba wajen samun
cikakkiyar nasarar shirin ba, tsawon shekaru goma da suka wuce.
Haka nan wannan qungiya ta sami nasarar shirya taron
ilimantarwa a yankin Bwari a babban birnin Tarayyar Najeriya Abuja,
wannan taro an shafe tsawon kwanaki bakwai ana aiwatar da shi
(daga 2-9 ga watan Nuwamba 2014) tare da haxin gwiwar cibiyar
kare haqqoqin xan adam a musulunci mai taken“Ra’ayoyin qwararru da masana fiqihun zamantakewar iyali, don bunqasa hanyoyi da qudurce-qudurcen siyasa da suka shafi al-adun aure da saki’” kamar
yadda aka rairayo batutuwan da za’a tattauna akansu daga batutuwa
da aikace-aikace daban-daban na wannan qungiya tare da goyon
bayan Jihohin da aka ambata na Arewa maso yammacin Najeriya
guda bakwai wato Jigawa da Katsina da Kaduna da Kano da Kebbi da
Sokoto da kuma Zamfara. Haqiqa waxannan taruka sun sami
baquncin mahalarta masu xumbin yawa da suka haxa da malamai, da
wakilan cibiyoyin ilimi, da na shari’ah da malaman addinin musulunci
da hukumomin yaxa labarai.
Daga cikin sakamakon qarshe da mahalarta tarukan suka
amince akansu sun haxa da wajabcin samar da tsare-tsare da sababbin
vii
dabaru na bunqasa matakin ilimi na al’umma tare da wayar da kan
al’umma akan matsalolin da ke da mummunan tasiri ga haqqoqin
mata a qarqashi abubuwan da dokokin zamantakewar iyali suka qunsa
gwargwadon al’adun aure da kyakkyawar zamantakewa tsakanin iyali.
Kamar yadda an haxu akan cewa hanya guda xaya tilo ta aiwatar da
waxannan wasiyyoyi a aikace itace ta gabatar da su ta hanyar
huxubobi akan mimbari a masallatan Juma’ah.
Haka nan zavar mimbarin huxuba don isar da saqon da ke
qunshe cikin waxannan takardu yunquri ne da zai yi matuqar tasiri
wajen yaqar nau’oi daban-daban na ta’addanci da musgunawa da ake
yiwa mata da yara a cikin wannan al’umma ta mu kamar yadda
nazarce-nazarce na dokokin zamantakewa suka tabbatar. Ba shakka
yin hakan zai tabbatar da adalci ga kowa musamman ma waxanda
suke cikin barazanar musgunawa a waxannan jihohi na Arewa maso
gabas da muke magana akansu, kamar yadda kuma hakan zai qara
xaukaka martabar musulunci da musulmi a wannan qasa
viii
Gabatarwa
Da sunan Allah Mai rahama Mai Jinqai.
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin
Allah su tabbata ga fiyayyen manzanni shugabanmu annabi
Muhammad da alayensa da sahabbansa da waxanda suka yi kira irin
kiransa har zuwa ranar sakamako.
Bayan haka: Haqiqa qungiyar kare haqqoqin mata da tabbatar da yi
musu Adalci (WRAPA) Najeriya ta yi namijin qoqari wajen kare
haqqoqin mata dai-dai da tanade-tanaden shari’ar musulunci na loqaci
mai tsawo wanda ya wuce shekaru goma. kamar yadda kuma bata yin
qasa a gwiwa wajen gayyato malamai da alqalai da malaman jami’o’i
don su haxu su tattauna akan al’amuran da suka shafi zamantakewar
iyali a mahangar Shari’ar Musulunci da nufin wayar da kan musulmi
akan haqqoqin mata. wannan qungiya ta shirya taruka wanda daga
cikinsu akwai wanda akayi a watan Agustar shekara ta 2009 da aka
gudanar a jihar Jigawa wanda mahalarta fiye da sittin da suka haxa da
malamai da alqalai da lauyoyi da malaman jami’ah suka halarta suka
kuma tattauna batutuwa kamar haka:
1. Ginshiqan walicci.
2. Mutuwar aure da abubuwa masu alaqa da shi.
3. Xaukar nauyin wacce aka saka da daxaxa mata.
3. Shayarwa bayan saki ko mutuwa.
5. Takardar registar aure a hukumance.
Ba shakka mahalarta sun tattauna waxannan batutuwa yadda ya
kamata, suka kuma kai ga matsaya wacce ta cancanci yabawa a
waxansu daga cikinsu, duk da cewa sun kaucewa magana akan
registar aure da hukunce-hukuncen damar da waliyyi ke da ita ta
auren dole.
A waxansu daga cikin irin waxannan taruka da aka yi na
tattaunawa waxansu sun nemi in rubuta littafi da harshen Hausa
ix
wanda zai yi qarin haske akan waxannan batutuwa da aka ambata
wanda kuma zai fayyacewa mutane irin abubuwan da suka shafi
rayuwarsu ta aure, kai da ma ta zamantakewa, ya kuma mayar da su
kan qa’idaojin addini da dokokinsa, ya kuma nuna musu hikimomin
da suke cikin zamantakewar iyali da hukunce-hukuncen su, wanda
hakan tasa na rubuta musu littafi mai taken “kundin zamantakewar iyali”. Haka nan a taron da mukayi a watan Satumba na shekarar
2015, mahalarta wannan taro sun amince da a rubuta huxubobi na
minbari da za su dace da abubuwan da littafin ya kunsa, a cewar su
lalle mai huxuba dai-dai yake da mai wa’azi wajen irin babbar
gudunmawa da tasirin da yake da shi matuqa a cikin al’ummarsa da
masu sauraronsa, da jama’arsa, kamar yadda yake kuma xan uwa ne
na mai bayar da tarbiyya da malami, wajen samun matsayi a zukatan
mutane gwargwadon kyautatawarsa da yin sa tsakani da Allah. Kamar
yadda a waxansu lokuta ma Allah kan bashi matsayi na musamman
wanda manyan mutane masu muqamin ba sa iya kaiwa ko kusa da shi.
Dukkan waxannan abubuwa sukan samo asali ne daga
kyakkyawan lafazi da ingantacciyar hanyar fa’idantarwa da qwarewa
wajen yin tasiri ga mutane ta hanyar siffantuwa dajin tsoron Allah da
yin abu tsakani da Allah tare da tsantsani. Bisa wannan ne na ga
dacewar in amsa wannan kira na samar da huxubobi da za su taimaka
wajen inganta al’amuran aure da qara samar da haxin kai tsakanin
ma’aurata, kamar yadda kuma na yi musu alqawarin cewa zan rubuta
wannan abu da aka nemi in rubuta, haka nan kuma waxansu daga
cikin mahalarta sun taimakeni ta hanyar aiko da waxansu ayoyi da
hadisai da zasu taimaka min wajen yin hakan, ina yi musu godiya
qwarai bisa wannan taimako.
Daga cikin waxannan bayin Allah akwai mai girma alqalin
kotun shari’ah a matakin farko dake jihar Jigawa mai girma Alqali
Bashir Birnin kudu, da ‘yar uwa malama Murjanatu Ibrahim daga
Katsina da sauransu. Ba shakka babban malamin nan mai suna Khairi
Sa’id yana faxa a mashahurin littafin nan nasa cewa“ba shakka mai huxuba a masallaci da mai wa’azin a taron jama’a sun fi tasiri a cikin zukatan jama’a fiye da duk wata kafa ta jan hankali ko ta hukuma ta
x
al’umma da jagorori da sojoji da jami’an tsaro. Domin sau da yawa jama’a kan ji tsoron waxannan da muka ambata, to amma fa ba sa son su. Shi kuwa mai huxuba a sanadiyyar nuna tausayinsa da kuvutarsa daga dukkan wani abin suka, ya kan iya samun damar tunvuke tushen sharri da ke dashe acikin zukatan masu aikata laifuka, ya kuma cusa musu jin tsoron Allah, da son gaskiya da amincewa da adalci da taimakon mutane a zukatansu. Ba shakka aikin mai huxuba shine gyara zukata, da farfaxo da kyawawan halaye a zukatan mutane, tare da inganta rayayyun zukata da tarbiya maxaukakiya don yin aiyuka tsarkakakku da aiki tuquru ba don kome ba saidon neman lada a wajen Allah Maxaukakin Sarki da manufar amfanar da mutane, don haka in anyi la’akari da wannan za’a ga cewa matuqar mai huxuba ya aiwatar da aikinsa akan doron abin da aka ambata fuskarsa za ta yi qwarjini, da annashuwa ya kuma kaishi ga wani matsayi maxaukai a wajen mutane.” Daga Khairi Sa’id
Wajen tattara waxannan huxubobi na yi amfani da littattafan
mazahabar Malikiyya irinsu“al-fiqhhul Maliki fi thaubihi al-jadid” na
Dakta Muhammad Bashir Shaqfah da littafin “Mudawwanatu al-fiqhi al-maliki wa adillatuhu” na Dakta As-sadiq Abdur-Rahman al-Firyani
daga cikin littattafan huxuba kuma akwai “al-mufid lil khuxaba, wa al-murshidin” na Imam Nasir Adam da“mausu’atu a immati al-haramain ash-Sharifain” wanda Khairi Sa’id ya tattara da sauransu.
Muna roqon Allah Maxaukain Sarki ya sanya wannan aiki ya zama
tsarkakakke don neman yardarsa, ya kuma zamo mai amfani ga
musulmai baki xaya, haqiqa shi mai iko ne akan haka, madalla da
wanda muka dogara da shi kuma madalla da wanda muke fatan ya
bamu nasara.
Goni Muhammad Sa’ad Ngamdu.
1
1
Rayuwar Mace Qarqashin Inuwar Musulunci
Da sunan Allah Mai rahama Mai jinqai.
Godiya ta tabbata ga Allah wanda yayi mace da namiji daga xigon
maniyyi a lokacin da aka tofa shi cikin mahaifa, ya kuma fifita
sashinsu wajen halitta.”Kuma namiji bai zamo kamar mace ba”. (Al-
Imran: 36). Ina qara yi masa godiya bisa ni’imominsa waxanda ba za
a iya qididdige su ba. Ina shedawa babu abin bautawa da gaskiya sai
Allah, shi kaxai yake bashi da abokin tarayya, sunaye kyawawa nasa
ne, da siffofi maxaukaka, ina kuma shedawa lalle shugabanmu
Annabi Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne wanda shine abin
yarda, ma’abocin ceto babba, da daraja mafi girma. Allah yayi daxin
tsira a gare shi da alayensa da sahabbansa ma’abota falala da kaifin
hankali, Allah yayi daxin aminci a gareshi aminci mai yawa.
Bayan haka, “ya ku mutane ku bi Ubangijinku da taqawa, wanda ya halicce ku daga rai guda, kuma ya halitta daga gare shi ma’auransa, kuma ya watsa daga garesu masu yawa maza da mata. Kuma kubi Allah da taqawa wanda kuke roqon juna da (sunan) Shi, da kuma zumunta lalle ne Allah ya kasance akanku Mai tsaro ne.
(Nisa’i:1).
Ya ku musulmai! ya kamata ku sani cewa an xauki lokaci mai
matuqar tsawo. Kuma an shafe dubunnan shekaru mace tana zaune
cikin wani irin yanayi mara daxi kafin zuwan addinin Musulunci, ba
shakka, mace ta kasance abar wasa da ita a hannun azzalumai tana
fuskantar nau’oi daban-daban na azaba da tozartawa, kamar yadda ta
sha fama da qasqanci da wulaqanci, a kwana a tashi a kullum ba abin
da take qara fuskanta sai zalunci da rashin kwanciyar hankali, tsawon
2
waxannan lokuta, haka nan aka kasa samun koda mutum xaya
shiryayyeda zai ji tausayinta ko dai a matsayin ta na uwa, ko ‘ya ko
matar aure, musamman ma wacce mijinta ya mutu da marainiya a
cikinsu ko ma kowacce mai rauni.
Mace ta kasance acikin al’ummomin Girkawa ana sayen ta, a
kuma sayar a kasuwanni kamar yadda ake sayar da dabbobi da bayi,
kai har ta kai ga cewa ma suna yi mata laqabi da najasa daga aikin
shexan dukkan wannan fa yana faruwa a yankin gabashin Turai.
Dangane kuwa da yammacin Turai an samu cewa har wani taro aka
gudanar a shekara ta 756 Miladiyya don lalubo ko ana iya sa mace
cikin jinsin bil-adama? to koma dai menene ita ba komai bace in
banda mai yin hidima ga namiji, sannan kuma a wancen lokacin ne
aka fitar da wani qudiri da shugabannin addini suka rattabawa hannu a
qasashen Turai cewa haramun ne ga mace ta karanta littafi mai tsarki
a domin kasancewarta ummul-aba’isin duk wani bala’i da jinsin bil-
adama ke fama dashi a wannan duniya a rayuwarsu.
Haqiqa wannan mataki nasu na qasqantar da mace har ta kai an
sami waxansu daga cikinsu da su ke iqirarin cewa lalle mace sharri ce
da ya zamo tilas ayi amfani da shi, kuma wani bala’i ne da zukata
suka shaqu da shi, kuma masifa ce wacce ba ta yadda za a iya guje
mata, kamar yadda ake ganinta holoqo hadarin kaka da kuma ciwon
da ba ya jin magani.
Su kuwa al’ummomin qasar Sin a zamanin dasun kasance
acikinsu idan mijin mace ya mutu sai itama a qone ta domin cigaba da
rayuwarta bashi da wani amfani, a rashin tausayi irin na su da halayya
irin ta dabbobi masu matuqar mugunta. A zamanin Jahiliyya kuwa
mace ta kasance a yankin tsibirin larabawa a na binne ta a rairayi tun
tana yarinya qarama, kamar yadda duk wanda aka yi masa bushara da
cewa matarsa ta haifi ‘ya mace sai ya rinqa tsanar fitowa jama’a su
ganshi saboda munin abin da aka yi masa bushara da shi, ba shakka
wannan wauta da girma take, baya ga kafircewa kyautar Allah, don in
ba domin haka ba mene ne na murtuke fuska da hautsinewarta da
zama cikin xaure fuska? ba don kome ba sai don abokiyar rayuwarsa
ta haifi mace, Allah Maxaukakin Sarki yana cewa “kuma idan aka
3
yiwa xayansu bushara da mace sai fuskarsa ta wuni baqa qirin, alhali kuwa yana mai cike da baqin ciki yana voyewa daga mutane domin munin abinda aka yi masa bushara da shi. Shin zai riqe shi ne akan wulaqanci, ko ko zai turbuxe shi a cikin turvaya? To abin da suke hukuntawa ya munana” (Nahl: 58-59). To hakanan dai mace ta shafe
loqaci mai tsawo tana rayuwa mara xaxi qarqashin hukunci na
zalunci mai muni da kama karya da ta zamo ruwan dare, yadda ake
amfani da mace kamar wata na’ura da ake amfani da ita ba tare da
tausayawa ba ko kaxan. Mace tana cikin irin wannan yanayi na baqin
ciki ne kwatsam sai hasken musulunci ya keto, hasken rahamarsa da
addininsa ya mamaye ko ina, duniya ta fahimci irin laifukan da ta
tafka dangane da mace.
Mace a mahangar musulunci ba ta gaza a kasancewarta warin
namiji ba (shi kuma na ta warin) domin kuwa annabi tsira da amincin
Allah su tabbata a gareshi yace: “mata tsagi ne na maza”1 to a wannan
loqaci aka wayi gari duniya ta amince za ta bawa mace waxansu daga
cikin haqqoqinta.
Ba ta yadda za ayi mace ta sami dukkan haqqoqinta cikakku
har sai in ta yi rayuwa a qarqashin inuwar addinin Musulunci. Domin
kuwa duk wani tanadi ko tsari da za'ayi wa rayuwar mace Musulma
abune mai iyaka da karancin falala. Wasu dokoki da haqqoqin da
qasashen Turai na wannan zamani waxanda ba ruwansu da addinin
Musulunci suka tsara ba nata bane. Domin kuwa addinin musulunci
shine ya shar'antawa mace haqqoqinta cikakku yayi bayaninsu dalla-
dalla; haqqoqin da take da su da nauyin da ya hau kanta. Ya tabbatar
mata da alkhairai masu yawa da abubuwa na kamala.
Musulunci ya lullube rayuwarta mai rauni da nau’i daban daban
na karamci da girmamawa. Ya kuma yiwa mutuncinta tanade-tanade
na kare shi da kulawa da shi a wani irin yanayi da bata tava
1 Ahmad da Abu Dawud da Bukhari
4
mafarkinsa ba kafin zuwan hasken Musulunci, ballantana kuma tayi
kwaxayin samunsa ko ta wacce irin hanya.
Don haka ya ke 'yar uwa musulma, abin nema gareki shine ki
tsare kanki a duk halin da zaki samu kanki a ciki. Haka kuma su
waxanda suka xauki nauyin sauke haqqoqinki ke mace musulma
lallai ne suyi adalci a fili da boye.
Haka nan addinin musulunci cikin hikimarsa ya kevance mace
da waxansu aiyuka da suka dace da ita don bayar da gudunmawarta
wajen gina al’umma bisa la’akari da siffofinta na musamman. Ya
ware mata waxansu ayyuka da ba mai iya aiwatar da su sai ita; da
suka haxa da xaukar ciki da haihuwa da shayarwa da tarbiyyar yara da
hidimar iyali da basu kulawa da wasu sauran ayyuka da suka dace da
irin yanayinta na musamman. A dukkan irin waxannan aiyuka da
mace za ta yi a ciki da wajen gida za ta yi sune cikin sutura da kulawa
da karewa da tsare mutunci da kykkyawan xabi’a da kyawawan
xabi’u na bil adama.
Ba shakka waxannan aiyuka na da matuqar muhimmanci
wanda bai gazana waxanda maza suke yi a fagage daban-daban ba.
Shugaban mawaqa (Ahmad Shauqi) Yana cewa:
“Ku reni ‘ya’yanku mata bisa kyawawan xabi’u, don
hakan babbar garkuwa ce a garesu daga masu
wulaqantasu, uwa makarantace in har ka bata horo, to ka
bada horo ga al’umma ingantacciya, uwa dausayi ce
matuqar an kula da ba shi ruwa sai yayi ta yin yabanya
matuqa”.
Haka nan manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata gare
shi yana cewa: “duk wanda yake da ‘ya’ya uku mata sai ya rene su, ya tausaya musu, ya xauki nauyinsu Aljannah ta tabbata gareshi1” sai aka
1 Bukhari aadab al-mufrad daibn Majah
6
Huxuba Ta Biyu
Godiya ta tabbata ga Allah wanda yake alqalanci da hukuncin
gaskiya, kuma shine mafiyin dukkan wani mai hikima, ya yi hukunci
na adalci ya kuma yi umurni da shi, ya kuma haramtawa kansa
zalunci, ya haramta shi ga bayinsa, kuma shine mafi tausayin masu
tausayi, ina shedawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah wanda
shine Ubangijin na farko da na qarshe, ina kuma shedawa
shugabanmu annabi Muhammad bawansa ne kuma manzonsa, kuma
shine wanda ya fifita akan duk halittunsa, tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi da alayensa tsarkaka da sahabbansa masu iklasi da
duk wanda ya bi tafarkinsa har zuwa ranar sakamako.
Bayan haka:
Ya ku mutane; ina yiwa kai na da ku wasiyya da jin
tsoron Allah ina kuma tunatar da ku cewa ba shakka
musulunci yayi umarni da girmama mata a matsayinsu na
iyaye ko ‘ya’ya ko matan aure, kamar yadda yayi umarni
da girmama su a loqacin da suka kasance ‘yan uwan
mahaifa maza ko mata, haka nan ya qarfafa tausaya musu
a loqacin da mazajensu suka rasu da loqacin da su ka
zamo marayu. Mace a mahangar musulunci itace mai
renon mazaje kuma tushen kowanne gwarzon namiji,
kuma ita ce uwa ga kowanne babban mutum kamar
yadda take makaranta da take yaye kowanne jagora abin
koyi. Don haka idan ta gyaru to gaba xayan al’umma ta
gyaru haka nan in ta karkace daga hanya to kowanne
tubali na ginin al’umma zai yi rauni, daga qarshe gininta
ya rushe. Don haka duk wani mai karamci zai karramata
kuma ba mai wulaqanta haqqinta sai wulaqantacce,
kamar yadda ba shakka tana iya yin galaba akan duk
wani mai girma, ita kuwa ba mai yin galaba a kanta sai
mai mummunan hali, kamar yadda ma’aikin Allah tsira
7
da amincin Allah su tabbata a gare shi yake cewa: “ina yi
muku wasiyya da kyautatawa mata bisa alheri, don
haqiqa ita mace an halicce ta ne daga qashin haqarqari
karkatacce, kuma mafi karkacewa a qashin haqarqari
shine samansa, idan kayi qoqarin miqar dashi sai ka
karyashi in kuma ka barshi ba zai gushe ba yana karkace
ba”1. Allah Maxaukakin Sarki yana cewa: “kuma Allah
ya sanya muku matan aure daga kawunanku, kuma ya
sanya muku daga matan aurenku xiya da jikoki, kuma ya
azurtaku daga abubuwa masu daxi, shin fa, da qarya suke
yin imani, kuma da ni‘imar Allah suke kafirta? (Nahl:
72). Wannan shine tubali na farko da musulunci ya xora
harsashin ginin karrama mace da ‘yanto ta daga
waxancan tsare-tsare na kama-karya waxanda ta shafe
lokaci mai tsawo tana rayuwa a qarqashinsu, ya kuma
ceto rayuwarta daga waccan guguwa da ka iya mayar da
rayuwarta ta zama mara amfani. Kuma manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa:
“lalle Allah ya haramta muku savawa iyaye mata da
binne ‘ya’ya mata kuma mafi alherin cikinku shine mafi
alheri ga iyalansa kuma nine mafi alherinku ga iyalina”2
yaku “yan uwa” waxannan misalai hujjoji ne da ke
tabbatar da cewa mace tana da matuqar qima da matsayi
a musulunci, kamar yadda duk wani abu da ta aikata za ta
sami kyakkyawan sakamakonsa, haka nan duk abinda ta
aikata za ta xauki nauyin alhakinsa.
Allah Maxaukakin Sarki Yana cewa: “kuma wani rai baya yin tsirfa face domin kansa, kuma mai xaukar nauyi baya xaukar nauyin wani, sa’annan ya baku labari ga abin da kuka kasance a cikinsa kuna savawa juna” (An-Nam1 :64). Kamar yadda kuma yake cewa:
1 Bukhari ya ruwaito
2 An hadu akansa
8
Kuma su matan suna da kamar abinda yake akansu yadda
aka sani kuma maza suna da wata daraja akansu, (Baqara
228).
Kuma ba shakka wannan daraja da aka ambata ba zata tava bawa
namiji damar tauye wani haqqi na mace koda daidai da qwayar
tsakiya ne ba ko yayi watsi da martabarta, abin da ake nufi da darajar
shine tsayuwa da zai yi wajen sauke nauyin da ke kansa da kuma
jagoranci da aka bashi bisa abin da Allah cikin hikimarsa ya sanyawa
maza na qarfin jiki da na hali da kaifin hankali waxanda bai sanya su
ga mace ba.
Kamar yadda Allah Maxaukain Sarki yake cewa:
Maza masu tsayuwa ne akan mata, saboda abinda Allah ya fifita sashensu da shi akan sashe, kuma saboda abinda suka ciyar daga dukiyoyinsu” (Nisa’i: 34) don haka in
har mace tana son daidaito tsakanin ta da namiji to ba
laifi Allah ya share mata hanyar yin hakan bisa abinda ya
dace da ita wato yin aiyuka na qwarai, saboda faxin
Allah Maxaukakin Sarki: “saboda haka Ubangiji ya
karva musu da cewa “Lalle ne ni ba zan tozartar da aikin wani mai aiki ba daga gareku, namiji ko kuwa mace sashenku daga sashe” (al-Imran: 195), haka nan kuma
yana cewa: “wanda ya aikata aiki na qwarai daga namiji ko mace alhali yana mumini, to haqiqa muna rayar da shi rayuwa mai daxi. Kuma haqiqa muna saka musu ladansu da mafi kyawun abinda suka kasance suna aikatawa.
(Nahl: 97).
Hakanan duk wanda ya cewa mace za ta iya yin dai-dai da namiji a
kowanne fage na rayuwa, to ba shakka ya yaudare ta, ya kuma gajiyar
da ita, saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki:
Halittar Allah da ya halicci mutane a kanta, babu
musanyawa ga halittar Allah. wannan shine addini
9
madaidaici, kuma amma mafi yawan mutane basu sani
ba” (Rum: 30) yana kuma cewa: “hanyar Allah wacce ta
shuxe daga gabanin wannan, kuma ba zaka sami
musanya ba ga hanyar Allah (Fath: 23).
Ya Allah kada ka bar wani zunubi namu a wanna wuri da muke face
ka gafartashi, haka nan wani baqin ciki face ka yaye mana shi, haka
nan wanda ya yi nesa da iyalinsa face ka mayar da shi, haka nan mara
lafiya face ka warkar da shi, haka nan mai bashi face ka hore masa
abin biya, haka nan wanda yake cikin wata damuwa face ka fitar
dashi, hakan duk wata buqata daga cikin buqatu na duniya da lahira
wacce a cikinta akwai masalaharmu ka kuma yarda da ita face ka biya
mana ita, ka sauqaqeta ya Ubangijin talikai.
Yaku bayin Allah! “Haqiqa Allah yana yin umarni da adalci da kyautatawa ma’abocin zumunta, kuma yana hani ga alfasha da abin da aka qi da rarrabe jama’a, yana yi muku gargaxi tsammanin ku kuna tunawa (Nahl: 90) ku tuna Allah sai ya tuna ku, ku kuma yi masa
godiya bisa ga ni’imominsa sai ya qara muku.1
1 Daga littafin Al-mufid lii khutaba’ wal murshidin, na Imam Muhammad Nasir Adam
10
2
Aure Da Gina Rayuwar Iyali A Musulunci.
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya halalta aure, ya haramta lalata,
wanda ya sanya mala’iku su zamo ma’abota fukafukai biyu-biyu da
uku-uku da huxu-huxu, wanda Allah yake cewa: “ku auri abinda yayi muku daxi daga mata, biyu-biyu da uku-uku da huxu-huxu. (an Nisa’:
3).
Godiya ta tabbata ga wanda ya halicci ma’aurata biyu namiji da
mace daga xigon maniyyi a loqacin da yake shiga cikin mahaifa, ina
shedawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, wanda yake shi
kaxai ne mai samarwa, bai Haifa ba, ba’a haife shi ba, kuma babu
xaya da ya kasance tamka a gareshi, kuma ina shedawa cewa
Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne, ma’abocin kyawawan
halaye, tsira da amincin Allah su qara tabbata ga qololuwar abin koyi
na qwarai kuma babban tsani na kaiwa ga Allah, shugabanmu
Muhammad fiyayyen waxanda suka aura suka aurar ya kuma ba aure
cikakken haqqoqinsa a bayyane da voye wanda ke cewa:
To amma ni na kan yi azumi in kuma sha in kuma
kwanta in yi barci, ina kuma aurar mata, kuma duk
wanda ya kaucewa tafarkin Sunnah ta to baya tare da ni”1
da alayensa tsarkaka da sahabbansa shiryayyu da duk
wanda ya bi tafarkinsu bisa kyautatawa har zuwa ranar
sakamako, “yinin da mutane ke tashi zuwa ga Ubangijin
halitta (Muxaffifin: 6).
1 Bukhar da Ahmad
11
Bayan haka:
ya ku mutane ku bi Ubangijinku da taqawa, wanda ya
halicce ku daga rai guda, kuma ya halitta daga gare shi
ma’auransa, kuma ya watsa daga garesu masu yawa maza
da mata. Kuma kubi Allah da taqawa wanda kuke roqon
juna da (sunan) Shi, da kuma zumunta lalle ne Allah ya
kasance akanku Mai tsaro ne. (an-Nisa’i: 1) “ya ku
waxanda suka yi imani ku bi Allah da taqawa, kuma ku
faxi magana madaidaiciya. Ya kyautata muku ayyukan
ku, kuma ya gafarta muku zunubanku. Kuma wanda yayi
xa’a ga Allah da manzonsa to lalle ya rabauta babban
rabo mai girma (Ahzab 70-71).
Lalle mu mun gitta amana ga sammai da qassai da
duwatsu, sai suka qi xaukarta kuma suka ji tsoro daga
gareta, kuma mutum ya xauketa, lalle shi (mutum) ya
kasance mai yawan zalunci, kuma mai yawan jahilci
(Ahzab: 72).
Haka nanAllah bai nufi cewa xan Adam zai yi rayuwa kamar sauran
dabbobi da sauran ‘yan uwansa a halitta na halittu daban-daban ba,
wato ya zamo sha’awararsa a sake take ba tare da an yi mata wani
linzami ba, ta yadda mu’amala tsakanin mace da namiji za ta wayi
gari sakaka ba abin da yake saita ta. A maimakon haka sai ya sanya
wani tsari wanda zai dace da xan adam na auratayya wanda shine zai
kare masa darajarsa, ya tsare masa mutuncinsa da karamcinsa ya
kuma yi masa sakamako akan hakan.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana
cewa: “hakama acikin saduwar da xayan ku zai yi da matarsa akwai ladan sadaka” sai su ka ce: “ya manzon Allah shin xayan mu ya biya buqatarsa, sannan kuma ya kasance ya na da lada? Sai yace: shin kuna ganin cewa da ya sanya ta cikin haramun zai kasance yana da zunubi?
12
To hakama idan ya sanya ta cikin halal zai kasance ya na da lada1”,
wato sai ya sanya haxuwar namiji da mace haxuwa ce mai karamci da
aka gina ta akan yardarsu ta kuma zamo haxuwa ce ta cuxe-ni-in cuxe
ka bayan kowannensu ya bayyana yardarsa a fili, sannan kuma da
shedawa cewa kowanne daga cikinsu ya zamo wani sashe ne na xan
uwansa, wanda da hakane ya xora sha’awa bisa amintacciyar hanya
ya kuma kare dangantaka daga vacewa, ya kuma ba mace kariya daga
zamowa wata gona ta biyan buqatar kowanne shashasha. Don haka sai
ya sanya wani tubali mai qarfi na ginin zamantakewar iyali wacce aka
kewaye ta qauna irin ta uwa da son mahaifi ta yadda zamantakewar za
ta haifar da wani tsiro mai kyau, tare da samar da zuri’a abar ala-san-
barka. Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:
Kuma Allah ya sanya muku matan aure daga kawunanku,
kuma ya sanya muku daga matan auren ku xiya da jikoki
kuma ya azurta ku da abubuwa masu daxi, shin fa da
qarya suke yin imani, kuma da ni‘imar Allah suke
kafirta? (Nahl: 72)
Kamar yadda matsayin mace bai tsaya ga kasancewarta abokiyar
zaman namiji a duniya kaxai ba, a maimakon haka itace za ta samar
masa natsuwa da kwanciyar hankali, baya ga babban nauyi da ke
wuyan mace, wanda ya fara tun daga haihuwa har zuwa ga duk wani
abu da bai wuce ikonta na xabi’a da na halitta ba. Allah Maxaukakin
Sarki yana cewa:
Kuma akwai daga ayoyinsa ya halalta muku matan aure
daga kanku domin ku natsu zuwa gareta, kuma ya sanya
soyayya da rahama a tsakaninku. lalle ne daga cikin
wancan akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani” (Rum:
21). Haqiqa aure yana kare ma’abocinsa daga munanan
halaye da sha’awa ke iya jawowa, ya kuma bashi dama
1 Muslim da Ahmad suka ruwaito
13
tayin rayuwa iri biyu, mai qarewa da dauwamammiya (ta
hanyar barin zuri’a). Domin idan ba don aure ba da ba’a
sami wanzuwar jinsin xan-adam a doron bayan qasa ba.
don haka shi aure shi ne abin da ke da dawwamar da
ambato ya kuma xaukaka darajar wanda ya yi shi.
Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi
yace: “idan mutum yayi aure to ya cika rabin addininsa
don haka sai yaji tsoron Allah a sauran rabin”.1 “duk
wanda ke da wadatar da zai yi aure bai yi ba, baya tare da
ni”2 “duniya wani xan jin daxi ne, mafi alherin jin
daxinta it ace mace ta gari”3 kamar yadda kuma manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yake
cewa: “yaku taron matasa duk wanda yake da ikon
xaukar nauyin aure a cikinku to yayi aure domin ya fi
komai kawo runtse ido (daga kallon haram) ya fi komai
tsare farji (daga zina) wanda kuma ba zai iya ba to ya
lazimci azumi domin shi garkuwa ne a gareshi”4 ya kuma
ce: “ku auri matan da kuke qauna kuma masu haihuwa
domin al’umma ta, tafi sauran al’ummomi yawa a ranar
alqiyama5.
Haka nan yana da matuqar muhimmanci musan cewa mace rabin
tsagin namiji ce domin ya zo a wata ruwaya: “mata tsagi xaya ne na maza” Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:
“Kuma su matan suna da kamar abin da yake akansu yadda aka sani kuma maza suna da wata daraja akansu” (Baqara: 228) bisa wannan
ne ya wajaba akan kowanne namiji ya san cewa, tsayawa tsayin daka
wajen ganin ya sauke nauyin amanar mace da ke wuyansa abu ne da
1 Baihaqi da Alhakim
2 Tabarani ya ruwaito
3 Ibn Majah da Tabarani
4 ABu Dawud da Ibn Majah
5 A hmad da Abu Dawud da Bukhari
14
ya zama wajibi gwargwadon ikonsa, wannan kuwa ya samo asali ne
kasancewar ita mace tana da yanayi na musamman da ya kevantu da
ita, kuma mace ba kamar namiji ta ke ba a halittar ta da xabi’unta, don
bincike ya nuna hatta qwayoyin halittar qwaqwalwarta an yi ta ne da
xabi’ar riqe abin da aka aika mata, ita kuwa ta namiji dawo da shi
take yi, wannan yazo dai-dai da faxin Allah Maxaukakin Sarki:
idan basu zama maza biyu ba, to namiji guda da mata
biyu, daga waxanda kuka yarda da su daga shedu”
(Baqara: 282), hakan yana daga cikin al’adar mata su
kafircewa kyautatawa wanda hakan ya na daga cikin
tauyayar addininsu da hankalinsu Allah Maxaukakin
Sarki yana cewa: “kuma kuyi zamantakewa da su ta
alheri. sannan idan kun qisu, to akwai tsammanin kuqi
wani abu Allah ya sanya wani alheri mai yawa a cikinsa”
(Nisa: 19), haka nan a dunqule kuma Allah Maxaukakin
Sarki yana cewa: “kuma kada ku manta da falalla a
tsakaninku, lalle ne Allah ga abin da ku ke aikatawa shi
mai gani ne. (Baqara 23).
Ya ku‘yan uwa na musulmi! Haqiqa mata masu taimakawa ne da aka
damqa a hannunku, kun karve su da amanar Allah ku ka halalta
farjinsu da kalmar Allah da amincewar iyayensu don haka kuji tsoron
Allah a cikin al’amarinsu. manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gareshi yana cewa:
Ka da wani mumini ya quntatawa wata mumina, in har
ya tsani wani hali nata zai yarda da wani na daban1.
Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:
1 Imam Ahmad
15
Maza masu tsayuwa ne akan mata saboda abin da Allah
ya fifita sashensu da shi akan sashe, kuma saboda abin
da suka ciyar daga dukiyoyinsu. To salihan mata masu
xa’a ne masu tsarewa ga gaibi saboda abin da Allah ya
tsare. kuma waxanda kuke tsoron bijirewarsu to ku yi
musu gargaxi kuma ku qaurace musu a cikin wuraren
kwanciya, kuma ku doke su. sannan kuma idan sun yi
muku xa’a, to kada ku nemi wata hanya a kansu..”
(Nisa’i: 35). Haka nan yana da muhimanci mu ambata
cewa, lalle rayuwar zamantakewar aure ta sava kacokan
da sauran nau’oi na zamantakewa waxanda ba ita ba,
waxanda ka iya haxa tsakanin mace da namiji, kamar
yadda zamantakewar aure ta fita daban da kowacce a
shari’ar musulunci kasancewarta rayuwa ce ta
dundundun har zuwa rasuwar xaya daga cikin ma’aurata
ko kuma in rabuwa ta zo a rabu cikin kyautatawa, don
haka ba alaqa ce ta xan wani loqaci ba, kamar yadda take
alaqa ce da komai na ta yake a bayyane babu yaudara ko
ha’inci cikinta, kuma rayuwa ce ta gwargwadon iko da
babu takurawa ko gazawa a cikinta. Allah Maxaukakin
Sarki yana cewa: “sai mawadaci ya ciyar daga wadatarsa
kuma wanda ake quntata masa arziqinsa to sai ya ciyar
daga abinda Allah ya bashi. Allah zai sanya sauqi a
bayan tsanani (Xalak: 7), haka nan rayuwar aure rayuwa
ce da ke tafiya bisa qa’idar nan ta “ba cutaba cutarwa”1
kamar yadda manzon Allah tsira da amincin Allah
sutabbata gare shi ya kasance yana yin umarni da haka a
cikin hadisansa.
Ba shakka aure ibada ce zalla, ciyarwa a cikinsa kuma sadaka ce,
kamar yadda matar aure ba baiwa ba ce, ba mai hidima ba ce, haka
nan rayuwar aure ba zamantakewa ce kawai ta abota ko sabo da juna
1 Muslim da Shafi’i da Ibn Majah
16
ba. Allah Maxaukakin Sarki yana cewa: “kuma kada kuyi gurin abinda Allah ya fifita sashenku da shi akan sashe, maza suna da rabo daga abin da suka tsirfanta, kuma mata suna da rabo daga abin da suka tsirfanta. Ku roqi Allah daga falalarsa. Lalle ne Allah ya kasance ga dukkan kome masani. (Nisa’i: 32).
Kuma yadda ya zama tilas kada maza su manta da cewa an
halicce ta ne daga qashin haqarqari, kuma mafi karkacewa a qashin
haqarqari shine samansa, duk irin qoqarin da za kayi don miqar dashi
ba zai miqe ba sai dai ka karyashi kamar yadda babu mai karya shi sai
mugu. don haka kyautata musu yafi munana musu, kuma manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa:
An cusawa zukata xabi’ar qaunar wanda ya kyautata
musu da qin wanda ya munana musu”1 haka nan wani
mawaqi yana cewa:
Kyautatawa mutane in har kana son bautar da zukatansu,
don sau da dama kyautatawa kan bautar da xan-adam
Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad
da alayensa da sahabbansa kayi xaxin tsira mai yawa a gareshi.
1 Abu alfaraj al asfihani, hilyat al awliya’
17
Huxubata Biyu
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya sanya halittar mutum daga ruwa,
ya kuma sanya masa dangantaka da surukantaka haqiqa Ubangijin ku
ya kasance mai cikakken iko, ina shedawa babu abin bautawa da
gaskiya sai Allah shi kaxai yake ba shi da abokin tarayya, madalla da
mai shiryawa da mai ba da nasara, ina sheda cewa shugabanmu annabi
Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne kuma ya kasance ga
muminai mai tausayi ne mai jinqai, tsira da aminci su tabbata ga
wanda aka aiko ga mutane gaba xayansu a matsayin mai bushara da
mai gargaxi, shugaban mu Muhammad shugaban waxanda suka yi
jihadi don xaukaka addinin Allah jihadi mafi girma, da alayensa masu
tsarki masu albarka da sahabbansa masu jihadi waxanda suka haifawa
musulunci masu kira da shiryawa, da waxanda suka suka biyo
bayansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako, ranar da dukiya da
‘ya’ya ba za suyi amfani ba, sai wanda ya zowa Allah da zuciya
kuvutacciya. “Ya Ubangijinmu! Ka bamu sanyin idanu daga
matanmu, da zuriyarmu kuma ka sanya mu shugabanni gamasu
taqawa.”
Bayan haka, “ya ku mutane ku bi Ubangijinku da taqawa, wanda ya halicce ku daga rai guda, kuma ya halitta daga gare shi ma’auransa, kuma ya watsa daga garesu masu yawa maza da mata. Kuma kubi Allah da taqawa wanda kuke roqon juna da (sunan) Shi, da kuma zumunta lalle ne Allah ya kasance akanku Mai tsaro ne. (an-
Nisa’i:1)
Ba shakka miji da mata sune ginshiqin zamantakewar iyali ta
gari, kamar yadda nauyin kulawa da iyali yana wuyansu haka nan
alhakin tabbatar da nagarta da kuvutarta daga kowacce barazana ita
ma tana wuyansu. Kuma mace ta gari a qarqashin koyarwar
musulunci itace tushen kowanne hali na kamala, mai tarbiyyar mazaje
da jarumai don haka in har tasowarta ta kasance ta qwarai, mai
xaukakar matsayi mai girman muqami domin kasancewarta
18
masana’antar mazaje. kamar yadda ake cewa duk loqacin da ka ga
jarumi namiji to ba shakka akwai mace a gefensa.
Uwa makaranta ce idan aka kula da ita, an kula da
al’umma mai qwarin tushe
Haka nan idan xabi’unta suka tavarvare halayenta suka karkace to
xaukacin al’umma sai ta wargaje, al’umma ta lalace, zamantakewar
iyali ta tavarvare, ruxani ya mamaye tsarin zamantakewar al‘umma,
fitina ta watsu ko’ina. Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi yana cewa: “ban bar wata fitina a baya na mafi cutarwa ga maza kamar mata ba”1
Kamar yadda aure shine mataki na farko na xaukar nauyin jagoranci
da shugabanci kamar yadda manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi yake cewa: “kowannenku mai kiwo ne kuma abin tausatawa akan abinda ake bashi kiwon”2
don haka Allah maxauakakin
sarki yake cewa:
Ya ku waxanda su ka yi imani, ku karewa kanku da
iyalinku wata wuta makamashinta mutane da duwatsu ne,
akanta akwai waxansu mala’iku masu kauri, masu qarfi.
Ba su savawa Allah ga abin da ya umurce su, kuma suna
aikata abin da ake umurninsu.” (Tahrim: 6). Kuma abu
mafi muhimmanci wanda addinin musulunci ya kula da
shi ga masu riqo da shi bayan imani da Allah da
kyakyawar niyya shine yiwa kai garkuwa domin kuwa
shi kansa imanin da Allah da manzanninsa yiwa kai
garkuwa ne daga halaka ta har abada.
1 An hadu akansa
2 An ruwaito shi a muwatta an kuma hadu akansa
19
Haka nan yiwa kai garkuwa ya game komai na rayuwa, kamar yadda
ya qunshi bin dukkan umarni da nisantar faxawa cikin abubuwan da
Allah Maxaukakin Sarki ya hana.
Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:
Ka cewa muminai maza su runtse daga ganinsu, kuma su
tsare farjojinsu. Wannan shine mafi tsarki a gare su. Lalle
ne Allah mai qididdigewa ne ga abin da suke
sana’antawa. Kuma ka cewa muminai mata su runtse
daga ganninsu, kuma su tsare farjojinsu, kuma kada su
bayyana qawarsu face abin da ya bayyana daga gare ta…
(Nur: 30-31).
Haka nan Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:
Kuma ku tabbata a cikin gidajenku, kuma kada ku yi fitar
gaye-gaye irin fitar gaye-gaye ta jahiliyyar fako. Kuma
ku tsaida salla, kuma ku bayar da zakka, ku yi xa’a ga
Allah da manzonsa (Ahzab: 33).
Kamar yadda akwai ayoyin alqur’ani masu yawa da hadisan manzon
Allah tsira da amincin Allah sutabbata a gare shi da suke yin nuni da
kamewar maza da mata gaba xayansu, haka nan ya zama tilas su haxa
gwiwa wajen tarbiyyar abin da Allah ya azurta su da shi na ‘ya’ya
maza da mata tarbiyya ta musulunci, kamar yadda ya zama wajibi
akan kowannensu ya taimaki xayan wajen bayar da gudummawarsa
da sauke nauyin da ke kansa na nauyin kula da iyali.
A koda yaushe manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata
a gare shi yana magana ne da masu ingantaccen hankali. Don Allah
xan uwa bani labarin kana ganin akwai wanda zai amince a ce wanda
yake qarqashinsa ya tozarta ko da kuwa mai yi masa hidima ne ko
kuma dabbarsa? Ballantana kuma a ce ‘yarsa. Don haka manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: “ku yi aure kuma ku
20
hayayyafa don lalle ni zan fi sauran al’ummomi yawan jama’a a ranar alqiyama”1 domin mu san cewa lalle mu iyaye maza da mata tilas ne
mu sauke nauyin abin da musulunci ya wajabtawa kowanne daga
cikinmu wanda idan ba muyi hakan ba to mun ci amana. Allah
Maxaukakin Sarki yace:
Ya ku waxanda suka yi imani! kada ku yaudari Allah da
manzonsa, kuma ku yaudari amanoninku, alhali kuwa
kuna sane. (Anfal: 27) Haka nan kuma yana cewa;
Ka ce lalle masu hasara sune, waxanda su kayi hasarar
rayukansu da iyalansu, a ranar qiyama. To waccan fa
itace asara bayyananna (Zumar: 15)
Wani mawaqi yana cewa:
Maraya ba shine, wanda iyayensa su ka yi bankwana da
baqin cikin rayuwa suka barshi a wulaqance ba. Lalle
maraya shine wanda zaka iske yana da ballagazar uwa
ko uba wanda bashi da loqacin kula da shi.
Ya Ubangiji ka da ka bar wani zunubi namu a wannan guri ba tare da
ka gafartashi ba, haka nan duk wata damuwa face ka yaye ta, haka nan
mai bashi face ka bashi abin biya, haka nan kada ka bar wata buqata
tamu wacce a cikinta akwai yardarka mu kuma muna da maslaha a
cikinta face ka biya mana ita ka kuma sauqaqe ta ya Ubangijin
halittu.
Yaku bayin Allah! “Haqiqa Allah yana yin umarni da
adalci da kyautatawa ma’abocin zumunta, kuma yana
hani ga alfasha da abin da aka qi da rarrabe jama’a, yana
yi muku gargaxi tsammanin ku kuna tunawa (Nahl: 90)
1 Abdur Razzaq as-san’ani
21
3
Aure Shine Tsarin Da Allah Ya Yarda Da Shi.
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya halalta aure ya haramta zina, ya
kuma sharxantawa musulmi aure a matsayin hanyar mu’amala
tsakanin namiji da mace, ya kuma sanya aure ya zamo xaya daga
cikin sunnonin Allah a halittunsa da tsarinsa. ya kuma sanya shi gama
gari ta yadda ba wani jinsi da zai kauce daga gare shi a xaukacin
halittun da suka haxa da ta bil-adama da dabbobi da duniyar tsirrai,
Allah mafi xaukaka mai faxa yana cewa: “kuma daga komai mun halitta nau’i biyu wata qila zaku yi tunani” (Dhari’at: 49) Kamar
yadda shine wanda ya sanya aure ya zamo tsarin da Allah ya zava don
hayayyafa da yaxuwa da xorewar rayuwa, bayan ya yiwa kowanne
daga cikin ma’aurata tanadin gudunmawar da zai bayar wajen cimma
manufar auren, Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:
Yaku mutane lalle mu mun halicce ku daga namiji da
mace, kuma muka sanya ku da ga qabiloli, domin kusan
juna. lalle mafificin daraja a wurin Allah, (shine) wanda
shine mafificinku a taqawa. Lalle ne Allah Masani ne
Mai qididdigewa” (Hujrat: 13) a wani wurin kuma yana
cewa: “ya ku mutane ku bi Ubangijinku da taqawa,
wanda ya halicce ku daga rai guda, kuma ya halitta daga
gare shi ma’auransa, kuma ya watsa daga garesu masu
yawa maza da mata. Kuma kubi Allah da taqawa wanda
kuke roqon juna da (sunan) Shi, da kuma zumunta lalle
ne Allah ya kasance akanku Mai tsaro ne. (Nisa’i:1)
Ina kuma shedawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai
yake bashi da abokin tarayya kuma ina shedawa Muhammad bawansa
22
ne kuma manzonsa ne tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
wanda yake cewa:
Yaku taron matasa duk wanda zai iya xaukar xawainiya a
cikinku to yayi aure domin shine mafi bayarda kariya ga
runtse ido mafi bayar da garkuwa ga farji, wanda kuwa
ba zai iya ba to ya lazimci azumi domin shi garkuwa ne
gareshi” Imam Ahmad da abu Dawud suka ruwaito.
Wanda kuma yace:
Idan bawa yayi aure to rabin addininsa ya cika sai yaji
tsoron Allah a sauran rabin” Baihaqi da Hakim suka
ruwaito. Shine kuma yace: “duk wanda ke da wadatar yin
aure bai yi ba to baya tare da ni1
Allah yayi daxin tsira a gare shi da alayensa da sahabbansa, da
waxanda suka biyo bayansu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
Bayan haka,
Ya ku mutane! Ku sani cewa Allah bai yi nufin barin xan adam yayi
rayuwa irinta sauran nau’oin halittu ta hanyar barin sha’awarsa
sauqaqaqqiya ba tare da linzami ba ta yadda mu’amala tsakanin mace
da namiji za ta zamo cikin hayaniya ba. A maimakon haka sai ya
sanya masa tsarin da ya dace da shugabanci da aka xora masa. Haka
nan ya sanya haxuwar namiji da mace haxuwa ce ta karamci da aka
gina ta bisa yardarsu da yardar waliyyansu, aka kuma xora ta akan
nema da amincewa a matsayin alamomi guda biyu na amincewa tare
da shedawar shedu akan cewa kowannensu ya zama halal ga abokin
zamansa.
To da hakane kuma musulunci ya sanyawa sha’awa tafarki
amintacce ya kuma tsare zuri’a daga vacewa, ya kare mace daga
1 tabarani
23
kasancewarta abar kwaxayin kowanne mavarnaci, ya kuma sanya
tubalin zamantakewar iyali a kewaye da xabi’ar qauna ta uwa, wacce
tausayin uba ya bata kulawa ta yadda za ta samar da shuka mai
yabanya da matuqar ban sha’awa. Ba shakka irin wannan tsari shine
Allah ya yarda da shi ya kuma xora musulunci akansa ya kuma rushe
duk wani tsari da ya savawa wannan. Haka kuma aure shine hanya
mafi kyau ta haihuwar ‘ya’ya da yawaita zuri’a da xorewar rayuwa da
ba zuciya kariya da kulawa matuqa. Haka nan, aure ibada ne don haka
ya zama wajibi ga duk wanda zai yi aure ya koye shi kamar yadda
yake koyar sauran nauo’i na ibada. Babban malamin wannanal’umma
wato Abdullah bin abbas Allah ya yarda da shi yana cewa: “ibadar mai yawan ibada ba ta cika har sai yayi aure”1
Yaku bayin Allah! haqiqa neman izinin aure na daga cikin
matakan farko na aure, domin kuwa Allah ya shar’anta shi kafin qulla
alaqar aure, domin kowanne daga cikin ma’aurata ya san abokin
zamansa na nan gaba, haka nan ya sami damar fuskantar auren bisa
ilimi da basira. Haka nan sharaxi ne ga mace ta kasance ta kuvuta
daga dukkan abubuwan da za su sa shari’a ta hana aurensa da ita a
wannan loqaci. Ya kuma kasance babu wanda ya rigashi ta hanyar
neman aure wandashari’a ta amince da shi, kamar yadda aka haramta
neman auren mai yiwa waninsa idda, ba banbanci tsakanin iddar
mutuwa da saki, haka nan ba banbanci tsakanin saki mai kome da
marar kome. Kamar yadda babu laifi ayi jirwaye mai kamar wanka
wato ya halalta ayi jirwaye da bayar da kyauta ga mai idda idan har
sakin ba mai kome ba ne.
Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:
kuma babu laifi akan ku a cikin abin da kuka gitta da shi
daga neman auren mata ko kuwa kuka voye a cikin
zukatanku Allah ya san cewa lalle ne ku za ku ambata
musu (shi). kuma amma kada ku yiwa juna alqawari da
shi a voye, face dai ku faxi magana sananniya. kuma
1 Musnad Abi Shaibah
24
kada ku qulla niyyar xaurin aure sai littafin (idda) ya kai
ga ajalinsa. kuma ku sani cewa lalle ne, Allah yana sanin
abin da ke cikin zukatanku, saboda haka ku ji tsoronsa.
kuma ku sani cewa Allah mai gafara ne mai haquri.
(Baqara: 235).
Ya ku bayin Allah ku sani cewa, Allah cikin hikimarsa yayi izini ga
mai neman aure ya kalli wacce yake neman aurenta, domin auren ya
zama an yi shi ta fuskar da za’a sami cikakkiyar nutsuwa da
amincewa.
An karvo daga Mughira xan Shu’ubah cewa ya nemi auren
wata mata, sai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi yace da shi: “ko ka kallle ta? Sai yace: a’a, sai yace ka kalle ta domin yin hakan zai qara cusa shaquwa a tsakaninku” An-Nisa’i da
Tirmidhi da Ibn Majah suka ruwaito ya kuma ce hadisi ne mai kyau.
Haka nan an karvo daga Jabir xan Abdullah Allah ya yarda da
shi yace: manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
yace: “idan xayanku zai nemi auren wata mace to in har ya sami ikon ya kalli abinda zai ja hankalinsa to ya aikata hakan”1
.
Abin da aka halalta a gani daga wacce ake neman aurenta
shine fuska da tafukan hannu kawai, ana kallon fuska ne don sanin
haske da kyau, tafukan hannu kuwa don sanin laushin jiki da
kaushinsa. Kuma baya halalta ga mai neman aure ya nufi jin xaxi da
kallon wacce yake neman aurenta in har kuwa yayi hakan to ya aikata
zunubi.
Kamar yadda ya halalta mai neman aure ya wakiltawani ko
namiji ko mace ya dubo masa fuskar wacce zai aura da tafukanta,
haka nan kuma ya halalta wacce aka wakilta mace ta ga abin da ya
wuce fuska da tafukan hannu. A cikin hadisin anas manzon Allah tsira
da amincin Allah su tabbbata a gare shi ya aika ummu salma ta gano
1 Almustadrak
25
masa wata baiwa sai yace: “ki shinshina kumatunta ki kuma dubo dugaduganta”1
.
Haka nan ya zama wajibi ga mai neman auren idan ya nemi
auren mace amma ba ta burgeshi ba ya kame bakinsa, kada ya faxi
wani abu daga cikin abubuwan da za su cutar da ita in an ambace su
domin tana iya yiwuwa abin da bai burgeshi ba, ya burge waninsa.
Haka nan wannan hukuncin baya tsaya ne kawai ga namiji ba, ita ma
mace zata duba mai neman aurenta domin kuwa ita ma akwai abin da
zai iya burgeta na sa kamar yadda shi ma yake da wanda zai burgeshi
na ta.
Kamar yadda kevancewa da wacce ake neman aurenta bai
halalta ba, domin zata cigaba da kasancewa haramun ga mai neman
aurenta har sai an xaura musu aure, domin kuwa ba za’a iya
amincewa kevancewarsu ba, gudun suna iya aukawa cikin abin da
Allah ya hana. Sai dai idan akwai muharrami ana iya kevewa da ita
don ba ta yadda za ayi a sami savon Allah a loqacin da yake nan. An
karvo daga Jabir Allah ya yarda da shi, manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi yace: “duk wanda yayi imani da Allah da ranar qarshe to kada ya sake ya kevance da wata mace ba tare da muharraminta ba, in ko har yayi hakan shexan ne zai zamo na ukunsu”2
. An kuma karvo daga Abdullah xan Umar Allah ya yarda da
shi yace: manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata gare shi
yace: “duniya jin xaxi ce kuma mafi alherin jin xaxin ta mace ta gari”
Muslim ne ya ruwaito, an kuma karvo wani hadisi daga gare shi
“duniya jin xaxi ce, kuma daga cikin mafi alherin jin xaxinta macen da za ta taimaki mijinta dangane da lahira” Zain ya ambace shi.
An kuma karvo daga Abu Umamatu Allah ya yarda da shi, daga
annanbi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: “mumini ba zai amfana da wani abu ba bayan jin tsoron Allah Maxaukakin Sarki da wani abu mafi alheri a gare shi kamar mace ta gari ba, wacce idan
1 Albaihaqi da Ahmad da Hakim
2 Imam Ahmad da Bukhari
26
baya nan sai ta riqe masa amanar kanta da dukiyarsa” Ibn Majah ya
ruwaito.
Ina rokon Allah ya yi mana albarka ni da ku, ya kuma amfane
ni ya amfane ku da fahimtar alqur’ani mai girama, ya kuma amfane
mu gaba xaya da abin da ke cikinsa na ayoyi da ambato na hikima
27
Huxuba Ta Biyu:
Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa muna yaba masa muna
neman gafararsa, muna neman taimakonsa, muna tuba a gareshi, muna
dogara da shi, muna kuma neman tsarin Allah daga sharrin
kawunanmu, da miyagun aiyukanmu, muna kuma shedawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah kuma Muhammad bawansa ne kuma
manzonsa, ya riqe amana, yayi nasiha ga al’umma, kuma yace: “mafi alheri a cikinku shine mafi alheri a wurin iyalansa kuma ni ne mafi alherin ku ga iyalina” Allah yayi xaxin tsira a gare shi da aminci mai
yawa.
Bayan haka:
Ya ku mutane ina yiwa kaina wasiyya da ku da jin tsoron Allah
a mu’amalarmu ga matanmu da iyalanmu haka nan a wajen
mu’amalarmu da sauran hulxoxinmu da su, a matsayinmu na bil-
adama. Ku sani ya zama wajibi a kanmu mu ciyar da su mu tufatar da
su, kamar yadda aka sani a shari’ance Allah Maxaukakin Sarki yana
cewa:
Kuma ciyar da su da tufatar da su yana kan wanda aka
haifar masa da alheri, ba a qallafawa rai face iyawarsa.
Ba’a cutar da uwa game da xanta, kuma ba’a cutar da
uba game da xansa, kuma akan magaji akwai misalin
wancan. to idan su kayi nufin yaye akan yardatayya daga
garesu, da shawartar juna, to babu laifi akansu. kuma
idan kun yi nufin bayar da xiyanku shayarwa to babu
laifi akanku, idan kun miqa abin da ku ka zo da shi bisa
al’ada, kuma ku bi Allah da taqawa, kuma ku sani cewa
lalle Allah daga abin da kuke aikatawa shi mai gani ne.
(Baqara: 233).
28
A wani wurin kuma Allah Maxaukakin Sarki yace:
Ku zaunar da su daga inda kuka zauna da gwargwadon
samunku, kuma kada ku cuce su domin ku quntata a
kansu kuma idan sun kasance ma’abota ciki ku ciyar da
su har su haife cikinsu. sannnan idan sun shayar da mama
saboda ku sai ku ba su tsadodinsu. kuma ku yi shawara a
tsakaninku bisa abin da aka sani. kuma idan kun nuna
talauci yo wata mace zata shayar da mama saboda shi
(mijin) (Xalaq: 6).
Ya ku bayin Allah lalle yaqi da zuciya da horar da ita akan kulawa
jajircewa wajen sauke nauyi da haqqoqin iyali da haquri da
halayensu, da jurewa cutarwarsu, da qoqarin gyara su, da shiryar da
su bisa hanyar addini, da qoqarin neman halal dominsu, da tarbiyyar
da kowanne mutum zai ba ‘ya’yansa duk abubuwa ne da suka zamo
tilas a kawunanku! Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi yana cewa:
Rana xaya ta shugaba mai adalci tafi daraja wurin Allah
fiye da shekaru saba’in1.
Don haka wahalhalun kula da iyali da ‘ya’ya dai-dai suke da na jihadi
don xaukaka kalmar Allah Maxaukakin Sarki, saboda haka ne Bishir
yake cewa:
Ahmad bin Hambal ya fini abubuwa guda uku: yana
neman halal don kansa da kuma don waninsa” kuma
manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata gare shi
yace: “abinda mutum zai ciyar da iyalinsa da shi sadaka
ne2
1 Tabarani
2 Musnad Shihab al qada’i
29
Kuma haqiqa akan bawa mutum lada bisa lomar da yakai bakin
matarsa.
Ina roqon Allah ya yi mana albarka, ni da ku baki xaya wajen
fahimtar Alqur’ani mai girma ya kuma amfane mu ni da ku da abin da
yake cikinsa na ayoyi da Ambato mai hikima, ya kuma karva mana ni
da ku domin shi mai ji ne kuma masani. Ina roqon Allah ya gafarta
min, ya gafarta muku.
Ku yi salati da salllama ga shugabanmu annabi Muhammad,
wanda shine mafi alherinmu ga iyalinsa, da alayensa da sahabbansa
masu yin aiki da ikhlasi, da waxanda suka biyosu da kyautatawa har
zuwa ranar sakamako. Ya Allah ka yarda da shugabanmu Abubakar
da Umar da Usman da Ali da sauran sahabbai baki xaya.Ya Allah
kada ka bar wani zunubi namu a wannan wuri da muke face ka
gafartashi, haka nan wani baqin ciki face ka yaye mana shi, haka nan
mara lafiya face ka warkar da shi, haka nan mai bashi face ka hore
masa abin biya, haka nan wanda yake cikin wata damuwa face ka
fitar dashi, hakan nan duk wata buqata daga cikin buqatu na duniya da
lahira wacce a cikinta akwai masalaharmu kuma akwai yardaka face
ka biya mana ita, ka sauqaqeta, ya Ubangijin talikai.
Ya ku bayin Allah! “Haqiqa Allah yana yin umarni da
adalci da kyautatawa ma’abocin zumunta, kuma yana
hani ga alfasha da abin da aka qi da rarrabe jama’a, yana
yi muku gargaxi tsammanin ku kuna tunawa (Nahl: 90)
Ku tuna Allah sai ya tuna ku, ku kuma yi masa godiya bisa ga
ni’imominsa sai ya qara muku, lalle ambaton Allah shine mafi girma.
30
4
Waxansu Daga Haqqoqin Miji Da Mata A Musulunci
Saki da riqo da abin kirki ko saki da kyautatawa.
Godiya ta tabbata ga wanda ya sanya aure a shari’ah yarjejiniya ce
tsakanin namiji da mace, wanda ta hanyarsa ne ya halaltawa kowanne
xaya daga cikinsu ya ji daxi da xayan, kamar yadda kuma ya
bayyanawa kowanne daga cikinsu abin da yake da shi na haqqoqi da
waxanda aka xora masa na wajibin al’umma wanda kuma manufarsa
ita ce tsare jinsin bil adama.
Haka nan ya shar’anta saki idan cigaba da rayuwar aure ta
gagara bisa waxansu dalilai.
Allah Maxaukakin Sarki yace:
Ya kai annabi idan kun saki mata sai, sai ku sake su ga
iddarsu, kuma ku qididdige iddar. Kuma ku bi Allah
Ubangijin ku da taqawa. Kada ku fitar da su daga
gidajensu kuma kada su fita face suna zuwa da wata
alfasha bayyananna, kuma waxancan iyakokin Allah ne,
kuma wanda ya qetare iyakokin Allah to lalle ya zalunci
kansa. Baka sani ba xammanin Allah zai fitar da wani
al’amari a bayan haka. Sannan idan sun isa ajalinsu (na
idda) sai ku riqe su da abin da aka sani ko ku rabu da su
da abin da aka sani (Talaq 1-2)
Ina kuma shedawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai
yake ba shi da abokin tarayya, mulki da godiya duk nasa ne, kuma
makoma zuwa gare shi take. Ina kuma shedawa lalle shugabanmu
31
Annabi Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne, wanda shine ya
xabi’antu da mafi kyawun halaye wanda kuma shine yake cewa:
A cikin abubuwan da Allah ya halalta babu wanda ya fi
yin fushi da shi kamar saki”1 wato duk da cewa an
ambace shi da halal amma abin qi ne wanda ba ya so,
wanda hakan kaxai ta isa ta sa a nisance shi.
Bayan haka, yaku mutane haqiqa ina yi muku wasiyya da ni kaina da
jin tsoron Allah. “Ya ku mutane ku bi Ubangijinku da taqawa, wanda ya halicce ku daga rai guda, kuma ya halitta daga gare shi ma’auransa, kuma ya watsa daga garesu masu yawa maza da mata. Kuma kubi Allah da taqawa wanda kuke roqon juna da (sunan) Shi, da kuma zumunta lalle ne Allah ya kasance akanku Mai tsaro ne. (an-Nisa’i:1)
Ya ku ‘yan uwa na maza da mata ku sani cewa Allah
Maxaukakin Sarki ya shar’anta saki don tausayawa da tausasawa ga
kowanne daga cikin ma’aurata, ta yadda aka ba su dama su warware
abin da suka qulla a tsakaninsu bisa yarda da amincewarsu, da nufin
samun kwanciyar hankali a cikinsa, to amma a maimakon hakan sai
ya jawo musu wahalhalu da rashin kwanciyar hankali ko takura da
rashin samun damar sauke nauyin da Allah ya xora musu. Kamar
yadda ake iya cewa saki maslaha ce ta miji domin kuwa shi aka bawa
wuqa da nama in har ya fahimci cewa matarsa tana da wani abin suka
ko dai na halitta ko na hali, wanda hakan zai jawo mutum ya yi
tambaya da cewa to yaya al’amarin zai kasance in kuma shi mijin ne
yake da wannan tawaya? Ko kuma a lokacin da matar da tsani zama
da shi saboda muninsa na halitta ko na xabi’a? Amsar wannan
tambaya itace, ba shakka Allah Maxaukakin Sarki ya bawa mace ita
ma haqqin neman a warware aurenta da mijinta (khul’i) ta yadda za ta
fanshi kanta ta hanyar ba mijin wani abu don mayar masa da abin da
ya kashe mata don ya sawwaqe mata. Allah maxaukakiin sarki yana
cewa: “idan kun ( danginsu) ji tsoron ba za su tsayar da iyakokin
1 Abu Dawud da Hakim da Baihaki
32
Allah ba, to babu laifi akansu a cikin abin da ta yi fansa da shi” (Baqara: 229)
Haka nan ya zo a cikin hadisi ingantacce cewa matar Thabit
xan Qais tace da manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi “miji na ba na zarginsa ta vangaren halayyarsa ko addininsa sai ni ba na son kafirci bayan musulunci” a wata riwayar kuma “ni dai ba zan iya zama da shi ba ” sai manzon Allah tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi yace: “ shin ko za ki iya mayar masa da gonarsa?” sai tace qwarai kuwa. Sai manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi yace: “karvi gonar ka kuma sake ta”
Bukhari ya ruwaito shi. Daga wannan bayani da ya gabata za mu
fahimci cewa saki abu da Allah Maxaukakin Sarki ya shar’anta a
lokacin da ake ganin cewa ba ta yadda za’a yi a sami haxin kai
tsakanin ma’aurata, aka kuma sami matsananciyar buqata yin hakan to
sai miji ya aiwatar da shi bayan an xau tsawon lokaci na haquri tare
da tunanin abin da zai iya biyo bayan sakin, tare da jimamin aiwatar
da shi a lokacin da dalilan da za su jawo yin sakin suka qi gushewa.
Haka nan Allah Maxaukakin Sarki ba ya shar’anta saki ba ne don
mutane su yi amfani da shi ta mummunr hanya, ko su xauke shi a
matsayin abin rantsuwa a wuraren kasuwancin mutane da sauran
abubuwa na savani da ke faruwa a tsakaninsu, domin kuwa ya zo a
hadisi ingantacce “duk wanda zai yi rantsuwa to ya rantse da Allah1” wannan na nuna cewa yin amfani da saki wajen rantsuwa haramun ne,
kamar yadda ake iya ladabtar da wanda ya aikata hakan. Sannan Allah
Maxaukakin Sarki ya sanya saki ya zamo sau biyu waxanda in har aka
sake samun saki bayansu to babu sauran halaccin kome sai bayan ta yi
wani auren mijin ya tare da ita. To da wannan ne aka yiwa mutane
linzami musamman a lokutan da zukatansu suka harzuqa ko kuma
suka fusata, kamar yadda aka siffanta a cikin bayanin sharuxxan saki
na sunna wanda shi kaxai ne shari’a ta amince da shi, wato saki
wanda yayi dai-dai da sunnah savanin na bidi’a wanda ko dai ya
kasance haramun ko makruhi. Saki na Sunnah shine wanda – in har
1 Ahmad da Imam Bukhari da Muslim
33
akwai buqatar yin hakan – mutum zai saki matarsa saki xaya a lokacin
da take da tsarkin jinin hailar da bai sadu da ita bayansa ba, bai kuma
qara wani sakin akansa ba har zuwa lokacin da za ta kammala idda.
Allah Maxaukakin Sarki yana cewa: “Ya kai annabi idan kun saki mata sai, sai ku sake su ga iddarsu, kuma ku qididdige iddar. Kuma ku bi Allah Ubangijin ku da taqawa. Kada ku fitar da su daga gidajensu kuma kada su fita face suna zuwa da wata alfasha bayyananna, kuma waxancan iyakokin Allah ne, kuma wanda ya qetare iyakokin Allah to lalle ya zalunci kansa. Baka sani ba xammanin Allah zai fitar da wani al’amari a bayan haka. Sannan idan sun isa ajalinsu (na idda) sai ku riqe su da abin da aka sani ko ku rabu da su da abin da aka sani…”
(Talaq 1-2)
Ba shakka wannan aya na nuna cewa sakin da aka bayar da izini
a yi shi shine saki xaya wanda bayan aukuwarsa za’a sami damar
kome a cikin idda. saboda da faxin Allah Maxaukain Sarki: “Kada ku fitar da su daga gidajensu kuma kada su fita face suna zuwa da wata alfasha bayyananna, kuma waxancan iyakokin Allah ne, kuma wanda ya qetare iyakokin Allah to lalle ya zalunci kansa. Baka sani ba xammanin Allah zai fitar da wani al’amari a bayan haka. sannan idan sun isa ajalinsu (na idda) sai ku riqe su da abin da aka sani ko ku rabu da su da abin da aka sani…” (Talaq 2).
Haka nan waxannan ayoyi na yin nuni da cewa, saki wanda
shari’ah ta amince da shi shine wanda aka yi shi a lokacin da mace
take cikin tsarki domin kuwa Allah Maxaukakin Sarki cewa ya yi “ ku sake su ga iddarsu” abin da ake nufi ga iddarsu shine a lokacin da
suke tunkarar iddarsu. Kamar yadda aka hana yin saki cikin jinin haila
domin kuwa hakan zai tsawaitawa mace iddarta ya kuma cutar da ita.
Haka nan kuma an hana miji ya saki matarsa a cikin tsarkin da ya sadu
da ita a cikinsa, domin idan ya yi hakan zai jefa ta cikin shakkun cewa
tana da ciki ko ba ta da shi a sanadiyyar waccan saduwa da ya yi da
ita, ta kuma rasa gane wacce irin idda za ta yi shin ta mai ciki ce da za
ta qarshe da zarar ta haihu ko kuwa ta mai lissafin jini ce?.
Dukkan nau’oin sakin na bidi’ah makaruhi ne banda sakin mace
tana cikin jinin haila wanda shi haramun ne, da shi da wanda aka yi
34
saki fiye da xaya a lokaci guda da wanda aka yi shi a cikin tsarkin da
aka sadu da mace a cikinsa.
Ya ku musulumai! Haqiqa Allah ya yi muku umarni da ku
girmama mata. Haka nan kuma zavavven Allah tsira da amincin Allah
su tabbata a gare shi yana cewa “inayi muku wasiyya da ku riqe mata da kyautatawa donin mace an halicce ta ne daga qashin haqarqari karkatacce, kuma mafi karkacewa daga cikin qashin haqarqari shine na samansu, in ka yi qoqarin miqar da shi sai ka karya shi, in kuma ka barshi a haka ba zai gushe yana kantare ba” Bukhari ya ruwaito shi.
Allah Maxaukain Sarki Yana cewa: “kuma Allah ya sanya muku matan aure daga kawunanku, kuma ya sanya muku daga matan aurenku xiya da jikoki, kuma ya azurta ku da abubuwa daxaxa. Shin fa da qarya suke yin imani, kuma da ni’imar Allah su, suke kafirta? (Nahl: 72)
Ya Allah kada ka bar wani zunubi namu a wanna wuri da muke
face ka gafartashi, haka nan wani baqinciki face ka yaye mana shi,
haka nan wanda ya bar iyalinsa face ka mayar da shi, haka nan mara
lafiya face ka warkar da shi, haka nan mai bashi face ka hore masa
abin biya, haka nan wanda yake cikin wata damuwa face ka fitar
dashi, haka nan duk wata buqata daga cikin buqatu na duniya da
lahira wacce a cikinta akwai maslahar mu face ka biya mana ita, ka
sauqaqeta ya Ubangijin talikai. Yaku bayin Allah! “haqiqa Allah yana yin umarni da adalci da kyautatawa ma’abocin zumunta, kuma yana hani ga alfasha da abin da aka qi da rarrabe jama’ah, yana yi muka gargaxi tsammanin ku kuna tunawa” Nahl: 90). Ku tuna Allah sai ya
tuna ku, kuma ku yi masa godiya bisa ga ni’imominsa sai ya qara
muku.
35
Huxuba ta biyu
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya bayyanawa bayinsa na gari
hanya mafi dacewa, ya horar da su bisa ladubba mafifita, ya kuma
yiwa waxanda ya so dace da yin aure dominsa, shine Ma’abocin
sunaye da siffofi mxaukaka. Ina shedawa babu abin bautawa da
gaskiya sai Allah kuma ina shedawa cewa Annabi Muhammad
bawansa ne kuma manzonsa ne wanda shine mai cewa:
Abubuwa guda uku yinsu da wasa da gaske ne kuma yinsu da gaske; gaske ne, aure da saki da kome”1
wannan
kuma shine abin da ma’abota ilimi suke aiki da shi. Ya
ku bayin Allah! ku sani cewa, kome shine maida auren
mace wacce aka saki da mijinta zai yi a cikin iddarta ba
tare da sake sabon aure ko waliyyi ko sadaki ba. Haka
nan haqqin da miji yake da shi na yin kome baya faxuwa
daga kansa ko kuwa shine da kansa ya sarayar da shi,
domin haqqi ne da Allah ya xamfara shi da saki ya kuma
damqa shi a hannun miji don haka babu wanda yake da
ikon yin wurgi da shi, sannan kuma Allah ya sanya kome
ne don bayar da damar a yi gyara a kuma magance
matsaloli da qarin samun damar gwada yiwuwar a zauna
tare. Allah Maxaukakin Sarki yana cewa: “kuma mazajen aurensu sune mafiya haqqi ga mayar da su a cikin wancan, idan sun yi nufin gyarawa. Kuma su matan suna da kamar abin da ke kansu, yadda aka sani. Kuma maza suna da wata daraja akansu (su matan). Kuma Allah Mabuwayi ne, Mai hikima” (Baqara: 228). Kamar yadda
kuma an halalta kome matuqar tana cikin idda ko da
kuwa xaya daga cikin ma’auratan yana cikin haramin
aikin hajji ko umra haka nan ko da xayansu bashi da
lafiya irin rashin lafiyar da ka iya yin barazana ga
1 Abu Dawud da Tirmidhi suka ruwaito
36
rayuwarsa. Waxannan abubuwa sune banbance banbance
da ke tsakanin aure da kome, shi kome ba sabon xaurin
aure ba ne, a madadin haka kome jaddada aure ne wanda
da ma tun can farko akwai shi.
Kome yana faruwa ta xaya daga cikin waxannan hanyoyin, ko dai
miji yace: “na dawo da matata qarqashin aure na” ko ta hanyar amfani
da wani lafazi da ke nuna yinsa ko da kuwa mijn bai yi niyya ba ya
faxi hakan ne ta hanyar wasa. Domin kuwa manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana cewa kome da wasa
dai-dai yake da yinsa da gaske kamar yadda ya gabata. Waxannan
abubuwa dukkansu suna faruwa ne in an yi la’akari da hukunci na
zahiri, dangane kuwa da ainihin abin da ke cikin zuciyar xan adam shi
da Allah kowanne aiki yana buqatar niyya, in kuwa aka rasa ta to aiki
ya vaci kamar yadda ita kuma niyya ita kaxai ba ta wadatarwa har sai
an haxa ta da aiki wato furtawa ba.
Abu na biyu shine, miji ya cigaba da ma’amala ta aure da
matarsa da niyyar kome wanda kuma yin hakan yakan tabbata ne a
lokacin da ya sadu da ita ko ya shafa ta ko ya sumbance ta. Ya ku
bayin Allah! Ku yiwa annabin rahama salati domin lalle Allah
Maxaukakin Sarki ya yi muku umarni da yin haka a inda yake cewa:
“Lalle Allah da mala’ikunsa suna salati ga annabi. Ya ku waxanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi” (Ahzab: 56).
Ya Allah, ka yi tsira da aminci ga shugabanmuAnnabi
Muhammad, da alayensu da sahabbansa baki xaya, ya Allah ka qara
yarda da shugabanninmu, Abubakar da Umar da Usman da Ali da
sauran sahabbai baki xaya. “Lalle Allah yana yin umarni da adalci da kyautatawa ma’abocin zumunta, kuma yana hani ga alfasha da abin qi da rarrabe jama’ah, yana yi muka gargaxi tsammanin ku kuna tunawa (Nahl: 90). Ina roqon Allah ya yi mana albarka, ni da ku baki xaya
wajen fahimtar Alqur’ani mai girma ya kuma amfane mu ni da ku da
abin da yake cikinsa na ayoyi da Ambato mai hikima, ya kuma karva
38
5
Waliyyan Aure
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya shar’anta hukunce hukunce ya
kuma rarrabe tsakanin halal da haram, ya yi umarni da aikata
nagartattun aiyuka ya kuma yi hani ga aikata munana, ya kuma
girmama ma’abota hankali da tunani ta hanyar shiriyarsu bisa
musulunci. Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:
Kuma akwai daga ayoyinsa ya halitta muku matan aure
daga kanku domin ku natsu zuwa gareta, kuma ya sanya
soyayya da rahama a tsakaninku. lalle ne daga cikin
wancan akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani (Rum:
21).
Haka nan muna yiwa Allah Maxaukakin Sarki godiya bisa ga abin da
ya shar’anta ya kuma sunnanta na aure. Ina shedawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake ba shi da abokin tarayya,
wanda shine ya haramta alfasha ta sarari da ta voye, kuma muna
shedawa shugabanmu Annabi Muhammad bawansa ne kuma
manzonsa ne wanda shine yake cewa:
“Ba aure sai da waliyyi” yana kuma cewa: “duk matar da
ta yi aure ba tare da iznin waliyyinta ba aurenta vatacce
ne1 ya Allah ka yi daxin tsira a agare shi da alayensa da
sahabbansa.
Bayan haka, ya ku mutane! lalle walicci ga mace a lokacin da za ta yi
aure na xaya daga cikin alamomin girmamata da martaba ta, domin
1 Abu Dawud da Tirmidhi
39
kuwa Allah Maxaukakin Sarki ya sanya mata wanda zai tsaya mata ya
kuma kare ta ya kuma tsare mata haqqoqinta tun a wurin xaurin aure,
domin kuwa da ace za ta xauki nauyin abubuwa ita da kanta da sai
kunya ta jawo ta sarayar da haqqoqinta da yawa, na wannan vangare
da ya shafi kayan da ya kamata a yi mata yayin xaurin aure. A xaya
vangaren kuwa wanda shine mafi mahimmanci wanda shine al’amarin
zavar miji mai addini, wanda ya dace wanda zai kwantar mata da
hankali, mai hanakali wanda zai ba ta haqqoqinta, a kowanne daga
cikin waxannan vangarorin waliyyi ya fi ta canacanta domin kuwa a
mafi yawancin lokuta ya fi ta gogayya, kamar yadda zai fi ta hangen
nesa da fahimtar haqiqanin al’amura. Kamar yadda an sa sharaxin
cewa duk wanda zai yiwa mace walicci to ya kasance namiji. Manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: “mace ba ta aurar da mace, haka nan mace ba ta aurar da kanta, mazinaciya itace ta ke aurar da kanta”1
haka nan kuma tilas ne ya kasance baligi mai
hankali kuma ‘yantacce. Don haka walicci yaro baya inganta haka nan
wanda aka tilastawa ko mahaukaci ko bugagge ko kwarkwar. Kamar
yadda an sharxanta cewa ya zamo musulmi don haka waliccin kafiri
ba ya inganta ga ‘yar sa ko ‘yar uwarsa musulma, kamar yadda
waliyyi tilas ne ya kasance baya cikin haramin aikin hajji ko umra,
domin ya zo a hadisi ingantacce “wanda ya yi haramar hajji ko umra ba zai aura ba kuma ba zai aurar ba”2 Idan muka ce Alwali sharaxi ne wajen xaurin aure, to waye ya
cancanta a fara gabatarwa?
Wanda yafi dacewa da ya zamo Alwalin mace shine; mafi kusanci a
gareta ta vangaren mahaifinta, saboda haka Uba yafi cancanta akan
kaka, shi kuma kaka yafi cancanta akan ‘yan uwanta, ‘yan uwa
shaqiqai sunfi ‘yan uwa ta wurin uba cancanta, ‘yan uwa na uba kuma
sunfi Baffanu cancanta, wasu malamai sunce kawunai suma sunfi
baffanu cancanta. 1 Subulussalam juz’I na uku shafi 127 da sunan ibn majah
2 Muwatta malik, Abu Dawud da Muslim
40
Amma anyi savani kan waliccin xa, shin zai zamo waliyin
mahaifiyarshi ko a’a? Imam Shafi’i yace xa bashi da haqqin walicci
akan mahaifiyarshi; domin ba’a dangantashi gareta, ana danganta xa
ne ga mahaifinshi, amma sauran malaman fiqihu sunce yanada haqqin
waliccin mahaifiyarshi, har ma wasu sun gabatar dashi akan Uba.
Waliyyi ya kasu kashi biyu; wato wanda ke da haqqin yin dole da
wanda ba shi haqqin yin dole, waliyyi mai haqqin yin dole shine
wanda ke da damar aurar da ‘ya mace wacce take hannunsa ba tare da
izininta ba, ko da kuwa ga makaho ne, kuma ko da sadaki qasa da na
tsararrakinta, matuqar dai bai tabbata cewa ya yi hakan ne don ya
cutar da ita ba, alal misali ya aurar da ita ga fasiqi ko mai cutar albaras
ko kuturu ko mahaukaci ko dandaqaqqe. A waxannan halaye da aka
ambata ba shi da ikon yin dole saboda abin da ya zo a cikin hadisi:
“ba cutaba cutarwa” waliyyi mai haqqin yin dole ya haxa da mahaifi,
ko wanda ya yi wasiyya ya riqe ‘yarsa ko wanda mutumin da aka
barwa wasiyya ya yi wasiyyar ya kula da ita. Mahaifi yana da ‘yancin
yiwa ‘yarsa auren dole ko da kuwa ba’a sami amincewarta ba in ta
kasance budurwa ko qarama. Ya zo a cikin hadisi daga annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi yace: “bazawara ta fi cancanta (ta yi zavi) da kanta fiye da na waliyyinta, ita kuwa budurwa sai a nemi izininta, kuma alamar izinin na ta shine shirunta” 1. wannan hadisi na
nuna cewa, hukuncin budurwa ya banabanta da na bazawara, a lokacin
da bazawa ta fi canacanta da ta zavawa kanta miji ita kuwa budurwa
za’a nemi izininta ne don a ji ko ta amince a ranta, don da ace duk
hukuncinsu iri xaya ne da hadisin bai banbanta su da cewa bazawar ta
fi cancanta da kanta ita kuwa budurwa sai a nemi izininta ba.
Damar da mahaifi yake da ita ta tilastawa ‘yarsa al’amari ne da
aka kafawa waxansu sharuxa, na farko daga cikinsu shine kasancewar
mahaifin bai yanke hukunci cewa yaba ‘yarsa ‘yancin tasarrufi cikin
al’amuranta ba, a misali yace da ita: na hukunta cewa kin kai
hankalin da za ki iya yiwa kanki zavi ko na damqa damar yin zavi a
hannunki. Sannan kuma ya zama tilas ta kasance budurwa ce da ba ta
1 muslim
41
tava yin aure ba, domin in ta tava aure ta xan daxe a gidan mijin
kamar abin da ya kai shekara xaya, to ikon da yake da shi na yi mata
dole ya faxi. Haka nan idan mijin da ya zava mata bai dace da ita ba,
saboda kasancewarsa fasiqi ko yana da wata nakasa to ya zama dole a
ba ta zavi, haka kuma idan yana da wata cuta bayyananniya to uba ba
shi da ikon yi mata dole kasancewar cutuwa abu ne da aka hana auka
mata a kowanne irin yanayi.
Haka nan kuma wanda mahaifi ya yiwa wasiyya da kula da
‘yarsa yana da haqqi irin na mahaifi wajen yiwa ‘yar da aka bar masa
dole a cikin al’amuran da shi kansa mahaifin yake da ‘yanci a cikinsu
to amma da sharaxin sai mahaifin ya amince masa da ya yi dole ko dai
a bayyane ko kuma a dunqule. Dangane da bazawara kuwa wanda aka
yiwa wasiyya yana da hukunci iri xaya ne da na mahaifi ba zai aurar
da it aba har sai ya nemi izininta da yardarta.
Ya yan uwa! Akwai wata masifa da ta vullo a wannan yanki
namu na qasar Hausa ta yadda za ka iske cewa kowanne waliyyi yana
auren dole, kai ciki ma har da makusanta waxanda ba waliyyai bane,
kai a waxansu lokuta ma zaka iske har da mata waxanda sun xauki
kansu a matsayin suna da haqqin yin dole, irin waxannan za ka iske
suna yiwa mace auren dole ne ta hanyar wakilta wani namiji. Ba
shakka, yin hakan abu da yake haramun bai halalta ba. Kuma haqiqa
yin hakan zalunci ne babba kuma wuce gona da iri ne wajen sauke
nauyin da Allah ya xora muku na ‘ya’yanku kuma ka da mu manta
kowanne mutum za’a yi masa hisabi bisa amanar kansa da ta
‘ya’yansa maza da mata da ‘yan aikinsa da ‘yan uwansa da ma dukkan
waxanda suke qarqashin kulawarsa. “Haqiqa kowannenku mai kiwo ne kuma abin tambaya ne dangane da abin da aka ba shi kiwo”.
““dukiyoyinku da xiyanku fitina xai ne. kuma Allah a wurinsa akwai wani sakamako mai giram: ( Taghabun: 15)
Huxuba Ta Biyu
42
Godiya ta tabbata ga Allah a kowanne yanayi, muna kuma neman
tsarinsa daga halaye irin na vatattu, kuma muna roqonsa afuwa da
lafiya da dawwamammiyar kuvuta daga dukkan sharri a dukiyoyinmu
da iyalanmu, muna kuma neman tsarinsa daga fitinar rayuwa da ta
mutuwa da fitinar Dujjal la’ananne da bijirewar mata daga biyayyar
mazajensu.
Muna godewa Allah Maxaukakin Sarki mai girma da xaukaka
bisa ni’imominsa muna fatan Allah ya tsare mana su daga gushewa.
Kuma muna shedawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi
kaxai yake ba shi da abokin tarayya wanda shine masanin sirri da abin
da yake bayyane, kuma shine wanda halitta da umurni duka suke
hannunsa. Kuma muna shedawa Muhammad bawansa ne kuma
manzonsa ne wanda Allah ya qarfafa da nasara da mu’ujizozi da
alayensa da sahabbansa Allah ya yi daxin tsira a gare su.
Ina roqon Allah ya yi min albarka ni da ku wajen fahimtar
Alqur’ani mai girma ya kuma amfane mu ni da ku da abin da ke
cikinsa na ayoyi da ambato mai hikima, ya kuma karva mana ni da ku
domin shi mai ji ne kuma masani. Allah ya gafarta min ya gafarta
muku. “Lalle Allah da mala’ikunsa suna salati ga annabi, Ya ku waxanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi” (Ahzab: 56) tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa ka yi daxin tsira a gare
su.
Lalle Allah yana yin umarni da adalci da kyautatawa
ma’abocin zumunta, kuma yana hani ga alfasha da abin
qi da rarrabe jama’ah, yana yi muka gargaxi tsammanin
ku kuna tunawa (Nahl: 90). Ina roqon Allah ya gafarta
min ya gafarta muku.
43
6
Yiwa Wacce Aka Saki Kyautar Jin Daxi Da Xaukar Nauyin
Matar Aure.
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya halitta muku mata daga
kawunanku ya kuma sanya qauna a tsakaninku. Allah Maxaukakin
Sarki yana cewa:
kuma akwai daga ayoyinSa Ya halitta muku matan aure
daga kanku, domin ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya
sanya soyayya da rahama a tsakaninku. Lalle a cikin
wancan akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani (Rum:
21)
Ina shedawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma
Muhammad bawansa kuma manzonsa, wanda yake shine ma’abocin
halaye masu girma, tsira da amincin Allah su tabbata a agre shi da
alayensa da sahabbansa, salati mai yawa.
Bayan haka:
Yaku bayin Allah! lalle Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:
Ya ku mutane ku bi Ubangijinku da taqawa, wanda ya
halicce ku daga rai guda, kuma ya halitta daga gare shi
ma’auransa, kuma ya watsa daga garesu masu yawa maza
da mata. Kuma kubi Allah da taqawa wanda kuke roqon
juna da (sunan) Shi, da kuma zumunta lalle ne Allah ya
kasance akanku Mai tsaro ne. (An-Nisa’i:1)
44
Abdullahi xan Umar yana cewa: “duk matar da aka saki tana da haqqi ayi mata kyautar da zata ji xaxi in banda wacce aka saki ba tare da an yanka mata sadaki ba, ba’a kuma kwanta da ita ba”
Daukar nauyin mace:
An karvo daga manzon Allah dangane da matanmu mai ya kamata mu
yi musu me kuma za mu bari? Sai yace “ka zowa gonarka yadda kake so, kuma ciyar da ita matuqar ka ci, ka tufatar da ita idan kayi tufa kada ka muzanta siffarta kar kuma kayi duka” silsilatul ahadith
assahihah.
Ya ku bayin Allah! Lalle ciyarwa wajibi ce akan duk wani miji da
matarsa take yin iddar da za’a iya yin kome domin kuwa matar da
take cikin iddar kome kafin ta kammala hukuncinta iri xaya da na
matar aure a komai in banda saduwa. Haka nan kuma ya zama tilas a
xauki nauyin mai idda matuqar tana da ciki a wannan hukunci babu
banbanci tsakanin iddar saki marar kome da wacce take yin iddar
mutuwa. Haka nan kuma wacce take zaman istibra’i na wani aure
vatacce saboda abin da ya zo a dunqule cikin faxar Allah Maxaukakin
Sarki: “kuma ma’abota cikunna ajalinsu, (shine) cewa su haifi cikinansu” (Talaq: 5). Haka nan an ware wacce aka yi li’ani da ita
wacce ita ba ta da haqqin kulawa kasancewar mijin ya kore cikin nata
ta hanyar li’ani. Kulawa ba ta wajaba ga mace marar ciki wacce take
iddar sakin da ba kome, saboda hadisin Fatimah ‘yar Qais a lokacin da
ta kawo qarar qarancin abin xaukar nauyinta da mijinta ya aiko mata,
sai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace da
ita “baki da haqqin kulawa”1 da kuma abin da za’a iya fahimta daga
faxar Allah Maxaukakin Sarki “ku zaunar da su daga inda kuka zauna daga gwargwadon samunku. Kuma kada ku cuce su domin ku quntata a kansu. Kuma idan sun kasance ma’abota ciki sai ku ciyar da su har su haife cikinsu” (Talaq: 6) ba shakka wannan ayar ta yi umarni da a
zaunar da waxanda aka saki, umarni na gaba xaya, sannan aka yi
1 Sunan Abi Dawud da Muslim
45
umarni da kulawa da masu ciki kaxai, don haka sai ya bayyana daga
abin da za a iya fahimta daga ayar cewa wacce ba mai ciki ba ta da
haqqin kulawa a iddar saki marar kome. Kamar yadda babu haqqin
kulawa ga mai iddar mutuwa saboda ita kulawa ana bayar da ita ne a
sanadiyyar jin daxi da ita ne wanda ya gushe daga yin mutuwa kamar
yadda zamantakewa ta qare. “kuma kace, “ ku yi aiki saannan Allah zai ga aikinku, da manzonsa da muminai, kuma za a mayar da ku zuwa ga masanin voye da bayyane, sannan ya ba ku labari da abin da kuka kasance kuna aikatawa” (Taubah: 105).
Ya ku bayin Allah! lalle kulawa da mace ya qunshi ciyarwa, da
tufatarwa da wurin kwana da sauransu, haka nan kulawar miji da
matarsa ta kasance wajibi ne saboda tsare kanta da take yi ta kula da
maslaharsa ta kula masa da gidansa da ‘yayansa’ a madadinsa, to
kamar yadda aka xora mata nauyin sauke wannan wajibi to shima sai
aka tilasta masa ya sauke wani nauyin nata na wajibi wato shine samar
da kulawa don ta sami damar sauke nauyin da aka xora mata da zarar
an xaura aure wanda kuma ake fatan ta tsayu da ita ta fuska mai kyau,
ba shakka matarka ce take sanya zuciyarka ta huta daga tunanin
tsaftace gida da kula da shi ta xauke maka nauyin girki da shara da
shimfixa da wanke kwanuka da samar da abubuwan jin daxin rayuwa
sannan kuma ta biya maka buqatar saduwa wanda ba don haka ba da
ba ta yadda za a yi mutum ya rayu a gidansa shi kaxai.
Abu Sulaiman ad-darani yana cewa:
Hidimar mace ta gari ba ta tsaya gare ka a al’amuran
duniya kaxai ba dominkuwa ta kan samar maka da
kwanciyar hankali fuskantar aiyukan lahira, wato ta
hanyar kula masa da gida da biyan buqatar sha’awa.
Yaku bayin Allah! daga abin da muka ambata za a fahimci cewa abin
da ake nufi da xaukar nauyi shine samar da buqatu na tilas waxanda
suka zama tilas ga rayuwar xan adam ta yadda ba za ta buqaci wani
abu a wurin wani na daban ba. waxannan buqatu na tilas na rayuwar
xan adam sune: abinci, tufafi da mazauni. dangane da abinci shine
46
wanda rayuwa ba ta yiwuwa sai da shi kamar yadda shine abin da zai
gina masa jikinsa yakuma tsare rayuwar da aka saki cikin jikin.
Su kuwa tufafi suna bayar da kariya ne ga jiki. Shi kuwa gida
shine inda xan adam zai kwana ya huta ya kuma sami tsaro daga
abubuwan da ka iya cutar da shi. Kulawa ta wajibi ba ta wuce
waxannan abubuwa uku da sauran hidimomi da ke xamfare da su,
haka nan kuma ta haxa da duk wani abu da mace za ta iya cutuwa da
barinsa. Da kuma sauran abubuwa da za a bayyana anan gaba. Ya ku
bayyin Allah bari mu yi bayani akan kowanne xayan daga cikin
waxancan abubuwa da muka lissafa. Na farko shine abinci, abincin da
ya zama wajibi miji ya ciyar da matarsa shine wanda zai iya
gwargwadon ikonsa da wadatarsa da kuma wadatar matar da
matsayinta, da yanayin gari da al’adu da zamantakewa da yanayin
rayuwarsu ta fuskar kasancewa mazauna birni ne su ko na qauye, da
yanayin tafiya ko zaman gida da farashin kayan abincin a lokacin da
ciyarwar ta wajaba wato yanayin araha da na tsada, waxannan
abubuwa kuwa za mu ga cewa dukkansu suna da alaqa da al’ada,
kamar yadda ya zama tilas akan miji ya samar da dukkan abin da ya
zama tilas wajen yin abinci bisa al’ada, kamar yadda akan qarawa mai
shayarwa da sauran abubuwan da za ta qara samun qarfi wajen
shayarwa don ya tallafa mata wajen shayar da xan nata.
Abinda ake nufi da al’ada itace al’adar garinta don haka ya
zama tilas a yi la’akari da halinsu su biyun. Babu banbancin
kasancewarsu sun yi dai-dai da juna a wadata abun ne da yake
bayyane to amma a loqacin da suka sava to ya zama dole a yi amfani
da yanayin tsaka-tsaki na yanayin guda biyu kasancewar kulawar
talaka ba ta kai yawan mawadaciya ba kamar yadda Wannan shine
abin da ake dogaro da shi a mazhaba.
Kulawa a gurinmu ba abu ne da za a iyakance shi ba, kamar
yadda ba yanayin mijin kaxai za a kula da shi ba savanin waxanda
suke faxin hakan, ba shakka za a yi la’akari da yanayin ma’auratan
biyu ne ta yadda za a yanke mata abin da zai wadace ta gwargwadon
abin da akan gani nan matsayinta, da matsayin mijin nata na wadata
da qunci saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki yana cewa: “kuma
47
ciyar da su da tufatar da su yana akan wanda aka haifar masa da alheri” .(Baqara 233). Wanda hakan yana nuna kula da yanayinsu
gaba xayansu. Da kuma faxar manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gareshi, ga matar abu Sufyan “ki xauki abin da zai ishe ki da ‘ya’yanki da abin da aka sani”1
Bukahari ya ruwaito shi. sai annnabi
tsira da amincin Allah su tabbbata a gare shi ya xora ta akan abin da
zai ishe ta ba tare da yayi mata iyaka ba, haka nan ita ma kulawa ana
bayar da ita ne gwargwadon abin da zai ishe ta da abin da aka sani.
haka nan ya zama wajini ya wadatar da ita da abin da aka sani.
Ya ku bayin Allah! abu na biyu shine tufatarwa wadda wacce
aka iyakance ta da aqalla sau biyu a shekara xaya loqacin sanyi da
abin da ke biye na loqacin bazara, na biyu kuma loqacin zafi da abin
da ke biye da shi a loqacin damina, kowanne loqaci akwai abin da ya
dace da shi matuqar dai loqutan sun banbanta da juna, in kuwa ansami
cewa loqutan basu da banbanci da juna to xaya ma ta wadatar a
tsawon shekara. Haka nan wasu sunce a kowanne loqacin sanyi da na
zafi za a yi tufafi in har irin tufafin da ake yiwa kowanne loqaci ya
sava da juna ne kawai a shekararsu, wato in har aka sami cewa
shekara ta farko zai wadatar a shekara ta biyu da ta uku, kamar yadda
ya yi a shekara ta farko ko kusa da haka, to za a iya wadatuwa da ita
har zuwa lokacin dsa za ta lalace. wannan hukuncin ya haxa da
lulluvi da mayafi da abin shimfixa da kayan sanyi da zanen lulluva na
lokutan sanyi da na zafi.
Haka nanan lissafa tufatarwa gwargwadon shi kansa kyallen da
nau’insa wajen yawa da qaranci gwargwadon halin mijin da halin
matar da matsayin kowannensu a al’adance. Mafi qarancin sutura
itace wacce za ta suturce jiki da kai ta kuma bayar da kariya daga zafi
da sanyi.
Ku faxaka ya ku ‘yan uwa! Ku yi salati da sallama ga mafi
alherin halittar Allah, Annabi Muhammad kamar yadda Allah da
kansa ya yi masa umarni da yi masa salati da sallama inda yace:
1 Bukhari
48
“Lalle Allah da mala’ikunsa suna salati ga annabi, Ya ku waxanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi” (Ahzab: 56). ya Allah ka yi tsira da aminci a
gare shi da alayensa da sahabbansa kayi aminci garesu mai yawa.
49
Huxuba ta Biyu
Godiya ta tabbata ga Allah Mai girma wanda shine girman ikonsa ya
buwaya, alherin sa da kyautatawarsa suke dawwamammu, wanda
shine ya umarci mace da yin lullubi da lazimtar ladubba waxanda
akansu aka gina ginshiqin kowanne gida. Muna shedawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake ba shi da abokin tarayya,
muna kuma shedawa Muhammad bawansa ne kuma manzonsa wanda
shine yake cewa “Akwai dinarin da zaka kashewa kanka, da wanda za ka kashewa iyalanka, wanda za ka kashewa iyalanka shine ya fi girman lada. " tsira da aminci su tabbata a gare shi da iyalansa da
sahabbansa.
Ya ku bayin Allah! Abu na uku na xawainiyyar iyali shine
wurin kwana, wato ya samar wa matarsa wurin zama wanda ya dace
da ita, ko dai ta hanyar mallaka ko haya ko aro. Haka nan yanayin
mazaunin zai kasance ne wanda ya dace da matsayi da siffa da
darajarta, kamar yadda al’amarin yake wajen ciyarwa gwargwadon
halin miji za ayi la'akari da shi.
Haka nan mace mai girma ma’abociyar matsayi tana da haqqin
kada a zaunar da ita a gidan da za ta zauna tare da ‘yan uwan miji,
waxanda suka haxa har da iyaye, don yin hakan na iya cutar da ita in
an yi la’akari da yanayin da ta taso a ciki, kamar yadda hakan zata iya
kai su ga yi mata shishshigi cikin al’amuranta. To amma idan aka
sharxantawa mace zama da ‘yan uwan miji da makusantansa waxanda
babu aure a tsakanin su da shi, to ba ta da ikon kin amincewa da zama
tare da ‘yan uwa miji a gida xaya sai dai in ta sharxanta hakan ko an
sami wani abu na cuta, idan kuwa ta sharxanta cin gashin kanta daga
yan uwansa ta hanyar rashin zama tare da su a gida xaya tun a wurin
xaurin aure to tana da 'yancin yin hakan.
Hakan nan ko da bata sharxanta hakan ba to amma sai aka
sami cutarta ta hanyar zamanta da su, wato kamar ganin sirrinta ko
sauran al’amuran da ba za ta so a gani ba, ko ma dai suka cutar da ita
50
da wani abin na daban, kamar yawan faxa tsakaninta da su, to tana da
'yancin kin amincewa don kada ta cutu da hakan.
Haka nan xaya daga cikin ma’aurata ba shi da yancin qin
amincewa da zama tare da, 'ya'yan wata ko wani mijin matuqar dai
babu wani mai kula da su na daban, kuma ya/ta san da haka tun kafin
a xaura auren, to ba shi da 'yancin korarsu daga gidansa, amma idan
bai san da hakan kafin daura aure ba, to yana da yancin qin amincewa
ya zauna da su.
Hakan nan wajibi ne akan miji ya xauki xawainiyar nemowa
matarsa magani, wanda hakan ya haxa da samo mata likita, biyan
kuxin magani da abubuwa makamantan haka, a wurin da yawa daga
cikin malamai. Haka nan ya zama wajibi akansa ya biya mai karvar
haihuwar da take karvar haihuwar matarsa, ko da kuwa bayan ya sake
ta ne, hakan nan saye- sayen kayan da ake bayarwa na haihuwa suma
sun wajaba akansa waxanda suka haxa da abinci da abin sha da
alawoyi.
Hakan nan kulawa da kwalliyar mace wacce idan an barta za ta
cutu ta hanyar rashin lafiya ko sukurkucewa, ba tare da banbanci
tsakanin ta yau da kullum da wacce ba ta yau da kullum ba, waxannan
sun haxa da kwalli, da qunshi, da saura, da man da za ta shafa a
jikinta.
Kyautar jin daxi itace duk wani abu da miji zai ba matarsa qari
akan sadaki, don ya rage mata jin raxaxin rabuwar da aka yi da ita, ta
hanyar sakinta, a nan babu banbanci tsakanin wacce aka yi mata saki
mai kome da wacce aka yiwa saki mara kome, kamar yadda kuma
wacce aka saki saki mara kome za a ba ta ne da zarar sakin ya auku,
ita kuwa wacce aka saki saki mai kome za a jira ne har sai ta kammala
iddarta kasancewar ita za ta cigaba da kasancewa a matsayin matar
aure ne har zuwa lokacin da iddarta za ta qare, domin kafin wannan
lokaci tana cikin jiran kome ne ba ta fara jin raxaxin sakin ba tukunna.
Kamar yadda kuma koda wacce aka saki ta mutu ne za a ba
magadanta waccan kyauta ta daxaxawa. Hukuncin kyautar daxaxawa
ga wacce aka saki mustahabbi ne, su kuwa shafi’iyya sun tafi akan
51
cewa wajibi ce kuma dalilan waxanda suke ganin wajibince sun fi
karfi. Allah Maxaukakin Sarki Yana cewa:
kuma waxanda aka saki suna da daxaxawa gwargwadon
hali, wajabci akan masu taqawa (Baqara: 241).
A wani wurin kuma yana cewa:
kuma babu laifi akanku idan kun saki mata, matuqar ba ku
shafe su ba, kuma ba ku yanke musu sadaki ba, ku ba su kyautar
daxaxawa, akan mawadaci gwargwadonsa, kuma akan maquntaci
gwargwadonsa domin daxaxawa da alheri, wajibine akan masu
kyautatawa” (Baqara: 236) haka nan Allah yana cewa: “ya kai annabi
ka cewa matanka, idan kuna nufin rayuwar duniya da qawarta, to ku
zo in yi muku kyautar bankwana in sake ku saki mai kyau” (Ahzab:
28). Haka nan kuma Allah Maxaukakin Sarki yace: “ya ku waxanda
suka yi imani idan kun auri muminai mata, saannan kuka sake su
gabanin ku shafe su, to ba ku da wata idda da za ku lissafa akansu,
kuma ku yi musu kyautar jin daxi, kuma ku sake su saki mai kyau
(Ahzab: 49).
Ya bayin Allah ku ji tsoron Allah, ku kiyaye haqqoqin
matanku, ku yi tsayin daka wajen sauke su, kamar yadda ya kamata,
tare da kiyaye ladubban yin hakan, da kiyaye manufofinsu ba shakka
yin hakan na da lada mai yawa, kamar yadda hakan na qara havaka
alkhairi, da soyayya, tare da qara danqon qauna da tausayi.
Ya Ubangiji ka bamu sanyin idanu daga matanmu da
zuriyarmu, kuma ka sanya mu shugabanni ga masu taqawa. ya Allah
ka karvi tuban masu tuba, ka gafartawa masu zunubi, ka biya bashin
waxanda ake bi bashi, ka warkar da marasa lafiyarmu, da sauran
marasa lafiya musulmai, ya Allah ka gafartawa matattunmu ka gafarta
musu zunubansu, ka karemu ya Ubangijin talikai “Haqiqa Allah yana yin umarni da adalci da kyautatawa ma’abocin zumunta, kuma yana hani ga alfasha da abin da aka qi da rarrabe jama’a, yana yi muku gargaxi tsammanin ku kuna tunawa (Nahl: 90). ina wannan Magana
52
tawa ina nemawa kaina da ku gafarar Allah mai girma, tare da sauran
musulmi daga kowanne zunubi, ina roqonsa ya gafarta musu, domin
shine mai yawan gafara mai yawan rahama.
53
7
Reno Da Sharuxan Da Suka Kevanta Da Shi
Godiya ta tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga
Manzon Allah, bayan haka, godiya ta tabbata ga Allah, muna gode
masa muna kuma neman gafararsa, muna neman tsarin Allah daga
sharrin kawunanmu, da munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya
shiryar babu mai vatar dashi, wanda kuma ya vatar babu mai shiryar
da shi. Kuma ina shedawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah,
kuma ina shedawa Shugabanmu Annabi Muhammadu bawan Allah ne
kuma manzonsa ne, ya isar da saqo ya sauke nauyin amfana, ya yiwa
al’umma nasiha ya yi jihadi wajen xaukaka addinin Allah matuqar
jihadi ya barmu akan hanya mai haske wacce hasken darenta dai-dai
yake da na ranarta, ba wanda zai kauce daga tafarkinta sai hallakakke.
Allah ya yi daxin tsira da albarka bisa alayensa da sahabbansa da
mabiyansa da wanda suka biyo su da kyautatawa har zuwa ranar
sakamako.
Bayan haka:
Allah Maxaukakin Sarki yace: “ya ku waxanda suka yi imani!
Kubi Allah da taqawa akan haqqin binsa da taqawa kuma kada ku
mutu face kuna masu sallamawa’’ (A’li-imran: 102). Haka nan Allah
Maxaukakin Sarki yana cewa:
kuma masu haihuwa (sakakku) suna shayar da abin
haifuwarsu shekara biyu cikakku ga wanda ya yi nufin ya
cika shayarwa. Kuma ciyar da su da tufatar da su yana
kan wanda aka haifar masa da alheri. Ba a kallafawa rai
face iyawarsa. Ba a cutar da uwa game da xanta, kuma ba
a cutar da uba game da xansa, kuma akan magaji akwai
misalin wancan. To idan suka yi nufin yaye, akan
54
yardatayya daga gare su da shawartar juna, to babu laifi
akansu. Kuma idan kun yi nufin ku bayar da xiyanku
shayarwa, to babu laifi akanku, idan kun miqa abin da ku
ka zo da shi bisa al’ada. Kuma ku bi Allah da taqawa.
Kuma ku sani cewa lalle ne Allah, ga abin da ku ke
aikatawa, Mai gani ne (Baqara: 233)
Ya ku mutane! ina yi muku wasiyya da kaina da tsoron Allah, kuma
ku sani cewa, reno shine ba wa yaro kulawa ta fuskar samar masa
makwanci da abincinsa da tufafinsa da tsaftar jikinsa da wurin
kwanansa. Hukuncin reno kuma wajibi ne, domin yin watsi da shi
tozartarwa ce ga yaro da hallaka shi, kamar yadda reno xaya ne daka
cikin abubuwan da Allah ya kimsa a cikin xabi’ar kowanne xan adam,
don haka za ka iske cewa ba ya kevanta ne kaxai da tsarin shari’ar
musulunci ba. Kamar yadda reno yana zama wajibi ne akan kowanne
xaya daga cikin uwa da uba kasancewarsa haqqine na tarayya
tsakanin wacce ta ke renon da wanda ake renon dukkansu suna da
haqqin a ciyar da su a tufatar da su, kamar yadda kuma wanda ake
renon yake da haqqin a dinga zuwa ana ganinsa, a na sa ido akan
yanayin da yake ciki da duba shi da ladabtar da shi, da ilmantar da shi.
Haka nan reno haqqi ne da ke kan shaqiqai mata muharramai,
sannan shaqiqai maza. Ga masu reno kamar haka:
Na farko Uwa domin itace ta fi kowa tausaya masa, kamar yadda an bada
labarin cewa wani mutum da ya saki matarsa, ya kuma yi nufin qwace
xansa daga wurinta sai ta zo wajen manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi tace;
ya Manzon Allah wannnan xana ne wanda cikina ya
kasance shine mazubinsa, kuma mamana shine abin
shansa, kamar yadda cinyata itace wajen hutawarsa, to
gashi mahaifinsa ya sake ni yana kuma son ya qwace min
shi’’ sai Manzon Allah tsira da amicin Allah su tabbata a
55
gare shi yace; “ke ki ka fi kowa haqqin riqe shi matuqar
ba kiyi aureba (Aunul ma’abud)
Sannan kuma abu Dawud da Tirmidhi sun fitar da hadisi daga Ali
Allah ya yarda da shi yace: Zaid dan Haritha ya fita ya nufi Makkah
ya dawo shi da ‘yar Hamza, sai Ja'afar yace: ni zan karveta don ni na
fi haqqin in riqe ta domin ‘yar baffana ce, sannan kuma akwai ‘yar
uwar mahaifiyarta matata, to ga shi kuma ‘yar uwar uwa tana da
hukunci irin na uwane. Shi kuma Ali sai yace: Ni na fi cancanta da
riqe ta don ‘yar baffana ce ga kuma matata ‘yar manzon Allah wacce
tafi kowa cancanta da ta riqe ta. Sai Zaid yace ni na fi cancanta da
renon ta, don ni na fita na nemota na shafe tafiya mai tsawo. Sai ya
ambaci hadisin nan da yake cewa:
Dangane da yarinya kuma na yi hukunci da a bayar da ita
ga Ja'afar ta yadda za ta kasance da yar’uwar
mahaifiyarta domin yar’uwar uwa a matsayin uwa take”
a wata riwayar kuma yace: “Lalle ‘yar uwar uwa, uwa
ce’.
Haka nan reno ya kan kasance ga mata da maza ne kamar kamar
yadda haqqin reno ya ke babu banbanci tsakanin musulmi da kafiri,
da bawa da ‘yantacce matuqar dai duk sharuxansa sun cika garesu,
wannan kuwa ya samo asaline kasancewar reno nauyi ne na
shugabanci da jagoranci don haka ba wanda ya cancanta ya yi shi sai
wanda ya siffantu da siffofi irin waxanda za su tabbatar da
cancantarsa, da cewa zai bawa yaron kariya ya kuma iya tsayawa da
abubuwan da yaron yake buqata to amma asalin waxanda aka sani da
reno sune mata, domin sune suka fi tausayi da jinqai suka fi sanin
hanyoyin tarbiyar qananan yara, sannan kuma sai ya koma hannun
maza kasancewar su ne suka fi ikon bayar da kariya, da kula wa, da
tsayuwa da abubuwan da yaron ke da bukata, to amma kowanne daga
cikin sn yana da sharuxa
56
Hakan nan an shimfixa waxansu sharuxa na tabbatar da haqqin
reno kafin mutum ya cancanci aiwatar da shi a kuma bashi ikon yinsa.
Daga cikin waxannan sharuxa akwai waxanda suka shafi wanda za’a
yiwa reno namiji da kuma waxanda suka shafi mace mai reno sannan
akwai waxanda suke yin tarayya a tsakaninsu:
2. Hankali Ba’a bayar da reno ga mahaukci, ba banbanci tsakanin mahaukacin da
ya haukace gaba xaya da wanda ya kanyi hauka na wani lokaci ya
warke wani lokaci, kamar yadda ba’a bayar da reno ga mai
rangwamen hankali ko kwar-kwar.
3. Ikon tsayawa da shi Wato ikon tsayawa da al’amuran wanda ake reno, don haka ba a bayar
da reno a hannu mai rauni da tsoho, da makaho, da bebe, da kurma, da
gurgu, da sauran ire-iren su maza ne ko mata duk waxannan ba’a basu
reno sai dai idan akwan waxanda za su yi musu renon, domin su
kansu suna da buqatar wanda zai tsaya da al’amuransu ballantana ace
za su xauki nauyin wani. To amma Hanafiyya suna da wata Magana
dangane da renon makaho da suka ce: “Dangane da renon sa indai har yana da ikon bayar da kariya to za’a iya bashi in kuwa ba hakan ba to ba za’a bashi ba” wannan kuma shine ra’ayin Mazhabin Shafi’iyya
3. Shiriya Shiriya xaya ce daga cikin siffofin cancanta, wacce ta haxa da balaga,
da ikon iya kulawa da xawainiya don sau da yawa za ka iske mutum
ya balaga to amma ba shiryayye bane to sai ya zama duk da balagarsa
wawa ne mai al’mubazzaranci ba zai iya kulawa da dukiya ba, sannan
kuma tana iya yiwuwa a sami wanda yake shiryayye amma bai balaga
ba, wannan abune da yake faruwa a kowanne lokaci na rayuwar
mutune.
Don haka sai Malikiyya suka sharxanta shiriya da wannan
ma’anar ta biyu wato suka xauka cewa mai renon ya kasance
shiryayye ne wajen kulawa da dukiya ko da kuwa ba baligi bane,
57
kasancewar daga cikin abubuwan da reno ya qunsa akwai tsare
dukiya, da iya hulxa ta kuxi ta hanya mai kyau don haka bisa wannan
ba’abawa wawa ko al-mubazzari reno don kada ya lalata dukiyar
wanda ake reno.
Addussuqi yace: In har ya tabbata yaro yana iya kulawa
da dukiya to an tabbatar da cewa zai iya renon waninsa,
ta yadda zai kasance shi wancan yaro mai reno shida mai
renonsa suna qarqashin kulawar mai renon yaron na
farko abin nufi sai renon babban ya kasance ta fuskar
rayuwar wanda ake renon shi kuma na yaron ta fuskar
dukiyarsa
1. Kuvuta daga cututtukan da ake iya xauka:
Wannan ya haxa da duk wata cuta da ake jin tsoron yaron zai
kamu da ita koda kuwa shi kansa yaron yana da irinta wannan
ya haxa da kuturta da sauran dangoginta na cututtuka masu
yaxuwa waxanda wani yake iya xauka a sanadiyar cakuxuwa
ko wanda za’a iya cutuwa ta hanyar hakan waxannan sun haxa
da qarzuwa da kirci da kuturta, to amma idan cutar mai sauqi ce
to ba za ta cutar ta fannin cancantar reno ba, wannan ya qunshi
kowacce cuta dake iya yaxuwa ko cutarwa da likitoci za su iya
ganowa a kowannane lokaci a kowacce qasa tana iya shiga
cikin jerin cututtuka da muka ambata.
2. Amana: abin da ake nufi a nan shine mai renon ya
kasance wanda ake iya amincewa da shi ne ta fuskar addinin
wanda ake reno da xabi’unsa da tarbiyyarsa, don haka ba’a
bayar da reno ga wanda ake jin tsoron zai iya gurvata addinin
wanda ake reno ko xabi’unsa ko tarbiyyarsa don haka ba’a
bayar da reno ga fasiqi ko fasiqa waxanda suka haxa da
mashaya giya ko wanda ya shahara da zina ko nau’oin wasanni
da aka haramta kasancewar irin waxannan na iya shagala da
fasiqancinsu da wasanninsu su bar waxanda aka ba reno su
58
tozarta. Haka nan mai reno namiji da mace duk xaya suke ta
fuskar amana
Ibn Abdul Bar yace:
Sabo da haka malamai ba sa ganin dacewar renon fajira
3. Samun muhalli: an sharxanta cewa tilas ne mahallin
mai renon ya kasance killatacce ne ta yadda za a amincewa
wanda ake renon ba zai wulaqanta ba, ko waxansu abubuwa ba
za su same shi ba, kamar shigowar fasiqai gidan ko su yi
mu’amala da yara, kamar gidan ya kasance yana qarshen gari
ne ba shi da tsaro kowa na iya shiga da daddare, haka nan ana
jiyewa ‘ya mace tsoron lalacewa a lokacin da ta kai munzalin za
a iya saduwa da ita. Hakan nan yaro na miji shima akan jiye
masa tsoron hakan.
Don haka za mu fahimci cewa manufar samun mahalli ita ce a
samu abubuwa guda uku: kare rai, da kare dukiya da kuma kare
mutunci daga gurvata.
4. Rashin kakkausan hali: Haka nan an sharxanta cewa
kada a sami kakkausan hali na mai reno ga wanda zai
raina don haka duk wanda aka san cewa yana da qarancin
tausayi da mugunta ko dai tun asali haka halinsa yake ko
kuma a sanadiyyar gabar dake tsakaninsa da mahaifan
wanda zai raina to in dai aka tabbatar da hakan sai a
gabatar da waninsa.
Dangane kuwa da haqqokin da ake yin tarayya akansu a dunqule
Iman Malik yana cewa dangane da mai reno mace:
Idan mace ba ta kasance a wuri killatacce ba, ko kuma ba
amintacciya ce ba, ko mara lafiya, komai rauni, ko
tsohuwa, to ba za a bata reno ba ‘yantacciya ce ita ko
baiwa
59
Albaji yace: “dalilin da yasa aka ce hakan shine; shi dai reno an sharxanta shi ne don tausayawa yaro, don haka idan har za ta gaza wajen tsayuwa da hakan ko bata da tausayi haqiqa zamansa a wurinta tozarta ce a gare shi” kuma waxannan abubuwa da aka faxa dangane
da mai reno mace an sharxanta su ga mai reno namiji. Ya ku bayin!
Allah “Haqiqa Allah yana yin umarni da adalci da kyautatawa ma’abocin zumunta, kuma yana hani ga alfasha da abin da aka qi da rarrabe jama’a, yana yi muku gargaxi tsammanin ku kuna tunawa (Nahl: 90). Ku ambaci Allah zai ambace ku, kuma ku yi masa godiya
bisa ni’imarsa sai ya qara muku, kuma haqiqa ambaton Allah shine
mafi girma kuma Allah yana sane da abin da kuka kasance kuna
aikatawa.
60
Huduba ta Biyu
Godiya ta tabbata ga Allah wanda shine abin nufi da buqata, tsira da
aminci dawamammu su tabbata ga annabin Allah, kuma manzonsa
kuma shugabanmu Annabi Muhammad, tsira wanda yake
dauwamamme da dauwamar mulkin Allah kuma ina shedawa babu
abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake ba shi da abokin
tarayya kuma ina shedawa Muhammad bawansa ne kuma manzonsa
ne Allah yayi daxin tsira a gare shi da alayensa da sahabbansa da duk
wanda yayi aiki da shiriyar sa har zuwa ranar sakamako.Ya ‘yan uwa
cikin imani kuji tsoron Allah haqiqanin jin tsoronsa .
Ba shakka Ahmad ya ruwaito hadisi shi da Hakim ya kuma
inganta shi daga Abu Ayyub al Ansari Khalid xan Yazid Al-ansari
Allah ya yarda da shi annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi yace: “duk wanda ya raba tsakanin yaro da mahaifiyarsa Allah zai raba shi da masoyansa a ranar alqiyama”.
Reno haqqi ne na yaro da yake da shi akan mahaifansa, kuma
xaya daga cikin abubuwa da suka zamo wajibi a kansu matukar dai
akwai alaqar aure a sakaninsu kuma suna zaune tare, to idan kuwa
suka rabu da juna to a wannan lokaci sai a kula da maslahar yaron da
za a rena. dangane kuwa da waxanda suka tafi a kan cewa haqqi ne na
uwa to sun dogara ne da faxar manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi "ke ki ka fi cancanta da riqe shi matukar ba ki yi aure ba” sannan kuma kasancewar za ta cutu a lokacin da aka raba ta
da yaron nata alhali kuwa Allah Maxaukakin Sarki yana cewa: “Ba a cutar da uwa game da xanta” (Bakara: 233). Dangane kuwa da
waxanda suke ganin cewa haqqi ne na yaro sun yi la'akari ne da kare
rayuwar yaron, da kula da shi da maslaharsa ba tare an waiwayi
maslahar mahaifiyarsa ba, wanda a dalilin haka ne ma za ka ga cewa
ana karve shi daga hannunta a lokacin da ta yi aure koda kuwa za ta
cutu a sanadiyyar yin hakan. Haka nan kuma idan mahaifinsa ya yi
tafiya irin tafiyar da za a zauna a can. Kamar yadda akan tilasta mata
61
reno matuqar ba wanda zai yi renon yaron sai ita wanda dukkan
waxannan abubuwa an yi sune don kulawa da yaron.
Haka nan bai kamata al’amarin reno yaci karo dana walicci ba
don haka a lokacin da yaro ya kasance qarqashin renon mahaifiyarsa,
hakan ba zai hana ya rinqa zuwa wurin mahaifinsa yana ilmantar da
shi ya koya masa ladabi, ya kuma damqa shi a hannun wanda zai
koya masa Alkurani da karatu da sana’a ko yadda za a gudanar da
rayuwa ba, wannan ya biyo bayan kasancewar waxannan abubuwa
dukkansu abubuwane da ake samun su daga mahaifi, don haka
mahaifi ya fi cancanta da ya riqe yaro a lokacin da yake buqatar
koyarwa, duk da cewa hakan ba zai hana renonsa ba. Haka nan xaukar
nauyin yaron da za a rena wanda yake talaka ne da nemo masa wanda
ya fi cancanta da renon sa, duk yana kan mahaifinsa mawadaci wanda
shine zai xauki nauyin abin da zai ci, ya sha, da kuma suturar da zai
sa, da sabulun wanka, da duk abin da zai buqata na wanki da sauran
kayan amfani. Kuma abin da za a yi la’akari da shi a dukkan
waxannan abubuwa ita ce al’ada, da wadatar mahaifin ko talaucinsa,
da kuma irin abubuwan da suka dace da sauran yara da ake reno masu
matsayi irin na sa.
Haka nan tilas ne akan mahaifi ko wanda ake yiwa wasiyya ya
xaukewa wacce aka bawa reno abinda za ta xauki nauyin yaron da
suturarsa, da dukkan abubuwa da aka ambata, kamar yadda alkali na
iya rubuta cewa: "wane ya bawa wance kaza da kaza don a yiwa yaronsa kuxin abinci, da yi masa hidima, da kuxin hayar gidansa’’ Kamar yadda kuma haqqi ne na mahaifiya ta ga ‘ya’yanta qanana
kowacce rana sau xaya, idan ba a wurinta suke ba, ta kuma ga
‘ya’yanta manya kowanne sati sau xaya. Khalil a cikin Mukhtasar xinsa yana cewa: “An hukunta haka ga yara qanana sau xaya a kullum, su kuwa manya kowacce ranar Jumuah”
Allah ya yi muku albarka ga fahimtar Alkurani mai girma ya
kuma amfane ku da abin da ke cikinsa na ayoyi da ambato mai
hikima, kuma muna roqon Allah ya tserar da ni da ku daga azaba mai
raxaxi, ya kuma shigar da ni, ya shigar da ku gidan ni’ima ya kuma
amsa muku domin shi Mai jine Masani.
62
Haqiqa Allah yana yin umarni da adalci da kyautatawa
ma’abocin zumunta, kuma yana hani ga alfasha da abin
da aka qi da rarrabe jama’a, yana yi muku gargaxi
tsammanin ku kuna tunawa (Nahl: 90).
Ku miqe zuwa ga sallah, Allah ya yi muku rahama.
63
8
Haqqoqin Mace Akan Waliyyinta
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya yi umurni da aiyuka nagari da
sada zumunta ya yi mana hani ga savawa iyaye ya kuma sanya haqqin
musulmi akan xan uwansa musulmi ya kasance mafi qarfin haqqoqi,
haka nan kuma ya sanyawa mace haqqi akan waliyanta na su aurar da
ita ga wanda ya dace da ita, ta kuma amince da shi. Kuma muna
shedawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah wanda shi kaxai
yake bashi da abokin tarayya kuma wanda yake shine ya yi halitta,
kuma dukkan wanda ba shi ba abin halitta ne, muna kuma shedawa
shugabanmu Annabi Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa ne,
wanda shine mai gaskiya abin gaskatawa ya Allah ka yi daxin tsira da
aminci a gare shi da alayensa da sahabbansa waxanda suka sauke
haqqoqi, da waxanda suka biyo su da kyautatawa cikin waxanda suka
gabata da kuma waxanda suka yi saura.
Ya ku mutane! Ku ji tsoron Allah ku kuma godewa ni’imar da
Allah ya yi muku ta ‘ya’ya a matsayin jarrabawa ko dai su zame muku
abin farin ciki duniya da lahira, ko su zame muku asara da abin
nadama, da wahala duniya da lahira. Kuma lalle yana xaya daga cikin
hanyoyi na godewa ni’imar Allah a cikinsu, ku tsaya da abin da Allah
ya wajabta akan ku na renon su da ladabtar da su bisa mafi kyawun
halaye, ku kuma aurar da su ta hanyar da Allah da Manzonsa suka yi
muku umarni, don haka ya zamo tillas mahaifi ya ji ra’ayin mace ya
sami yardarta kafin ya aurar da ita.
Ya ku bayin Allah! Haqiqa haqqin iyali da jibintar al’amuransu
abu ne da ya tabbata da ayoyi da hadisai, Manzan Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa:
64
lalle wanda ya fi kowa imani daga cikin muminai shine
wanda ya fi kyawawan halaye ya kuma fi su tausasawa
ga iyalinsa1.
Don haka ya zama tilas ga dukkan mai hankali ya yi aiki da
shiryarwar manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
yace dangane da tausayawa mace ko dai a matsayinta na matar aure
ko ‘ya ko ‘yar uwa. Idan ta kasance matarsa to ya kamata ya sani
cewa tana da haqqoqi akansa haka ma idan ta kasance uwa to tana da
haqqoqi, kuma yana daga ciki haqqoqin da ‘yarsa ke da su akansa
akwai gujewa aurar da ita ga wanda ba taso ko ga wanda bai dace da
ita ba.
An karvo daga Khansa’u ‘yar Khidam Al-ansari cewa:
mahaifinta ya aurar da ita a lokacin tana bazawara sai ta ji ba ta son
hakan, sai ta je wajen Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi sai ya warware auren nata (Fathul bari). An karvo kuma
daga Ibn Abbas Allah ya yarda da shi yana cewa: “wata yarinya ta zo wajen Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ta ambata masa cewa mahaifinta ya aurar da ita alhali ba ta so, sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba ta zavi”
Iman Ahmad da Abu Dawud suka ruwaito.
An karvo daga Abdullahi xan Buraidata shi kuma ya karvo
daga mahaiafinsa yace: “wata budurwa ta zo wajen Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi tace: lalle mahaifina ya aurar dani ga xan xan uwansa don ya xaukaka matsayinsa, yace: sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya sanya al’amarinta a hannunta sai ta ce na zartar da abin da mahaifina ya yi dama na yi nufi ne nasanar da mata cewa iyaye maza ba su da haqqi na tilastawa ‘ya’yansu mata. Ibn Majaha ya ruwaito shi kuma maruwaitansa
ingantattu ne.
Ya ku ‘yan uwa! Lalle bayan abin da ake ji a zuciya dangane
da ‘ya’ya da abin da Allah ya sanya a cikin zukatan iyaye na qauna da
1 Imam Ahmad da Tirmidhi
65
tausayi da jinqai da tausayi ga ‘ya’yansu ba za su bari mahaifi ya
aurar da yarsa ga wanda ba ta so ba. Don ba shakka, zukatan iyaye an
cusa musu qaunar ‘ya’yansu an kuma dasa musu tausayi da son bayar
da kulawa gare su, da tausaya musu, da bayar da mahinmanci ga
al’amuransu. Don haka duk wanda ya rasa wannan xabi’a ta tausayi
ya aurar da ‘yarsa ga wanda bai dace ba, ko ga wanda ba ta so batare
da wata maslaha ba, to ba shakka ya siffantu da mugunta ya bi son
zuciya. Kamar yadda xaukar irin wannan mataki baya rasa haifar da
mumman sakamako na fanxarewar yarinyar da aka yiwa auren dole ya
janyo ta gudu daga cikin gidan mijinta ta faxa cikin halaye na qazanta
da bin hanyar rashin arziki wanda mahaifinta ya jefa ta ciki sabo da
jahilci.
Kamar yadda qasashenmu a wannan zamani akwai waxanda
suke yiwa ‘ya’yansu auren dole ba tare da wata hujja ba. Don haka
lalle waliyyai da suka haxa da ‘yan uwa, da mahaifi su ji tsoron Allah.
kamar yadda a yanzu al’amarin har ya kai ga cewa wasu lokuta har da
iyaye mata da kakannin mata waxanda basu da wani haqqi na walicci
ko yin dole to amma sai ka gansu suna yiwa yarinya auren dole su
bayar da ita ga wanda ba taso sabo da masalaharsu ba ta yarinyar ba.
Ya ku bayin Allah! haqiqa mawallafin littafin Fiqhussunnah (Sayyid
Sabiq) a cikin babin wajibcin neman izinin mace kafin aurar da ita
yana cewa:
Duk da irin savani da aka yi dangane da waliccin mace
ya zama wajibi a fara jin ita ra’ayin macen don a sami
amincewarta kafin xaurin aure kasancewar aure
mu’amala ce ta har abada, kamar yadda zama ne na haxin
gwiwa tsakanin namiji da mace, to idan kuwa haka ne, ba
ta yadda za a samu dauwamar haxin kai, kuma soyayya
da danqon kauna su xore matukar ba a sami yarda ba. To
bisa wannan ne shari’a ta hana yiwa mace auren dole
budurwa ko bazawara, ta hanyar tillasta mata ta auri
wanda ba ta so. Kamar yadda shari’ah ta sanya xaura
mata aure kafin neman yardarta xaya daga cikin
66
abubuwan da suke sa aure ya qi inganta, ya kuma ba ta
damar ta nemi a warware shi don yin watsi da nuna fin
qarfi da waliyinta ya yi wajen xaura mata aure.
(Fikhussunnah, juz’i na 2, shafi na 89-90).
Ya ku bayin Allah! lalle tilasta mace akan auren dole haqqine kawai
na waliyyi da ke da ikon yin tillas, to amma duk da haka bai halalta a
qyale shi ya yi amfani da hakan a matsayin wata hanya ta zaluntarta
ba, in har kuwa ya tabbata cewa ya yi nufin cutar da ita kamar aurar
da ita ga fasiki ko mara lafiya kama kuturu ko mahaukaci ko
dandaqaqqe to bai halalta ya tillas ta taba. Haka nan kuma haramun
ne a gare shi ya jingin ta, wato waliyyi ya hana matar da take
karkashin waliccin sa yin aure sabo da takurawa da zalunci ba tare da
wata maslaha ba. Haka kuma Allah Maxaukakin Sarki ya haramta
hakan a inda yake yin kira ga waliyyai da cewa:
To kada ku (waliyyansu) hana su su auri mazansu (da
suka sake su) (Baqarah: 323).
Don haka in har aka samu cewa waliyyi da ke da izinin yin tilas yayi
nufin cutarwa ne ko dai ta hanyar take-takensa da aka gani koya faxa
da bakinsa, kamar kasancewar matar ma’aikaciya ce da yake cinye
albashinta, ko yana amfana da hidimar da take yi masa, ta yadda zai yi
asarar dukkan waxannan da zarar ya aurar da ita, to ba shakka
haqqinsa na yin tilas ya faxi.
Haqiqa abin da yake gudana a yau a wannan qasashe namu ta
yadda za ka iske waxanda ba su da ikon yin tilas suna yin hakan varna
ce babba, domin kuwa yin tilas haqqine kawai na mahaifi da ya cika
sharuxan yin haka.
Haka nan mafi yawa daga cikin malaman fiqhu da suka haxa da
Imam Malik da Shafi’i da Ahmad bin Hambal suna ganin cewa,
yardar waliyyi da amincewarsa na xaya daka cikin sharuxan ingancin
aure, kuma mace wacce take mai hankali kuma baliga in ta kasance
budurwa waliccinta zai zamo na dole ne, ta yadda al’amarin aurar da
67
ita zai kasance ne a hannun waliyyinta shi kaxai in kuwa ta kasance
bazawara ce to waliccinta na tarayya ne a sami yardar waliyyinta da
amincewarta ita kanta. Sun bayar da dalilin yin haka daga Alqur’ani
da sunnar annabi mai martaba.
Dalilin da suka dogara da shi daga littafin Allah shi fadin Allah
Madaukakin Sarki:
To kada ku (waliyyansu) hana su auri mazansu idan sun
yarda da juna a tsakanin su da alheri (Bakara: 232).
Daga sunnah kuma faxinsa tsira da aminci su tabbata a gare shi.
Mace bata aurar da mace, kuma mace bata aurar da
kanta, duk wata mace da ta yi aure ba tare da izinin
waliyinta ba to auren ta vatacce ne, vatacce ne, vatacce
ne, in har ya sadu da ita to tana da sadaki na abin da ya
halalta na farjinta, in kuma aka yi jayayya to shugaba
shine waliyyin wanda bashi da waliyyi”1 haka nan ya zo
a hadisin Abu Musa yana cewa: Annabi tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi yace: “ Ba aure sai da
waliyyi2.
Yaku bayin Allah! Haqiqa walicci ga mace a lokacin aure girmama
mace ne, da martabata ta yadda Allah ya sanya mata wani wakili da
zai kare ta ya kuma tsare mata haqqoqinta yayin xaurin aure, domin
kuwa da ace itace za ta xauki nauyin yin hakan da kanta, da kunya ta
rinjaye ta ta sarayar da da yawa daka cikin haqqoqinta yayin xaurin
aure. wannan fa ta vangaren abin duniya da ya shafi kayan aure
kenan, a xaya vangaren kuma wanda shine mafi muhimmanici wanda
ya zavar miji da ya dace, ma’abocin halaye masu kyau da riqo da
addini, wanda zai faranta mata rai ya kuma kare haqqoqinta ba shakka
1Subulussalam, juz’I na 3 shafi na 128
2 Abu Dawud da Tirmidhi suka ruwaito
68
waliyi ya fi kowa ikon yin hakan kasancewarsa mafi rinjayen lokuta
mutum ne da ya fita gogayya da hango Haqiqanin al’amura. Kamar
yadda son rai na xan wani lokaci na iya fizgar macen da take son aure
ta shaqu da saurayin neman auren ta saboda kwalliyarsa ba tare da
wani zurfin tunani ba, son zuciya da qarancin tunani su vebe ta, ta
hango wata maslaha a matsayinta ta gaske ta hanyar irin shigar da
yake qarya da yaudara. Ba shakka wannan ta tava faruwa a Maiduguri
inda aka samu wani saurayi ya yaudari wata budurwa da ta shaqu da
shi sabo da kwalliyarsa ta fili, duk dacewa mahaifinta ya tanadar mata
miji nagari wanda ya dace da ita, wanda kuma ya yi alqawarin cewa
zai barta ta cigaba da karatu, to amma sai taqi ta bawa mahaifin nata
haxin kai, bayan ‘yan uwanta sun sha fama wajen qoqarin janyo
hankalinta, taqi sai kawai suka aura mata wanda ta zavawa kanta,
bayan sun haifi xa xaya kawai sai ya yi amfani da wannan dama ya
hana ta ci gaba da karatun nata, da kuma aikin da take yi na koyarwa,
aka wayi gari a koda yaushe yana tuhumarta da zina, sannan bayan ta
haifa masa ‘ya’ya biyar cikin wahala da tsanani mahaifinta kuma ya
rasu, aka wayi gari ita da mahaifiyyarta a kullum ba abin da suke fama
dashi in banda talauci, sai ya kama zarginta da cewa shi yana ma
zarginta da shakkar cewa ‘ya’yan nasa ne, duk da cewa kuwa shi
mazinacine wanda har ta kai ga waxansu lokuta takan same shi tare da
matan maqotanta a gidan haya, kamar yadda take faxa, sannan kuma
ya kan fita daga gida don zuwa wajen waxansu matan na daban. Duk
lokacin da ta nemi ya sake ta sai ya yi sauri ya rigata zuwa wajen
alqali, ya yi kararta wajen alkali da cewar yana son ta fanshi kanta.
Hakan nan daga qarshe sai ya zo mata da wata shawara cewa tunda
dai shi yana shakkar kasancewar waxancan ‘ya’yan nata uku ba na sa
ba ne, abin daya fi shine su kashe su gaba xayansu su huta shi da ita,
da dai ya ga taqi amincewa sai yace to shi zai kasheta ya shaqe ta, da
nufin kashe ta, ta yi ta qoqarin qwatar kanta har dai Allah dai ya bata
ikon kuvuta daga gare shi kamar yadda ta bayyana.
A lokacin da ta nemi taimakon mahaifiyarta ita kuwa ta ce ba za
ta iya taimaka mata da komai ba.
69
To anan ne nake cewa wannan shine sakamakon savawa iyaye
Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:
Kuma mun yi wasiyya ga mutum game da mahaifansa
biyu uwarsa ta xauke shi a cikin rauni akan wani rauni,
kuma yayensa a cikin shekara biyu (muka ce masa) ka
gode mini da kuma mahaifanka biyu makoma zuwa
gareni kawai take. Kuma idan mahaifanka suka tsananta
maka ga ka yi shirka dani ga abin da baka da ilimi a gare
shi to kada kayi musu xa’a. Kuma ka aboce su a cikin
duniya gwargwadon shari’ah, kuma ka bi hanyar wanda
ya mai da al’amari zuwa gare ni, sannan zuwa gare ni
makomarku take, sannan in baku labari game da abin da
kuka kasance kuna aikatawa (Lukman 14-15).
Ina roqon Allah ya yi mana albarka ni daku cikin fahimtar Alqur’ani
mai girma, ya kuma amfane ni ya amfane ku da abin dake cikinsa na
ayoyi da anbato mai hikima, Allah ya yi mana gafara ni da ku, lalle
shi Maiji ne kuma Masani.
70
Huduba Ta Biyu:
Godiya ta tabbata ga Allah mai girma, wanda shine mai
dauwamammen iko, da kyautatawa wanda ya umurci mace da suturta
jikinta da lazimtar ladabi, wanda kuma a bisa wannan ne kowanne
gida yake kafuwa kuma ya ginu. Kuma muna shedawa cewa babu
abin bautawa da gaskiya sai Allah, muna kuma shedawa Annabi
Muhammadu bawansa ne kuma Manzonsa ne wanda shine yake cewa:
Akwai dinarin da zaka bayar wajen xaukaka addinin
Allah, da dinarin da za ka bayar don ‘yanta bawa, da
dinarin da za ka yi sadaka da shi ga miskini, da dinarin da
za ka bayar wajen kula da iyalinka, wanda duk ya fi
giman lada a cikinsu shine wanda kabayar ga iyalinka”1
da alayensa da sahabbansa ka yi qarin aminci a gare su.
Ya ku bayin Allah! Iyaye masu haqqin yin dole Haqiqa shari’ah ba ta
ba ku dama ku aurar da ‘ya’yanku mata ba tare da izininsu ba, a
matsayin wata hanya ta cutar da su ba. Domin kuwa wancan haqqi da
aka ba ku na yin dole yana tabbata ne kawai idan bai bayyana cewa,
kuna da nufin cutar da su ta hanyar aurar da su ga fasiqi ko mahaukaci
ko dandaqaqqe, kamar yadda auren dole da mahaifi zai yiwa ‘yarsa an
taqaiceshi da waxansu qa’ijoji waxanda suka haxa da:
Na farko: ya kasance mahaifin bai hukunta cewa ‘yarsa baliga ta yi
hankali ba, in kuwa ya hukunta hakan to bashi da haqqin yi mata dole.
Na biyu: ya kasance buduwar da ba ta tava aure ba. In kuwa ta yi suka
rabu da mijinta to bashi haqqin yi mata dole koda kuwa ba ta gushe
tana budurwa ba, ya kuma kasance mijin ya dace da ita, idan ya
1 Imam Muslim
71
kasance mijin bai dace da ita ba ko kuma akwai cutarwa to mahaifi
bashi da haqqin yi mata dole.
Duk da cewa yana da haqqin yin dole ga waxanda muka ambata a
cikin ‘ya’yansa ana nemansa da ya yi shawara da ‘yarsa budurwa
baliga a cikin al’amarin aurenta, saboda abin da ya zo a cikin hadisi
“bazawara ta fi cancanta da yiwa kanta zavi fiye da waliyinta, buduwa kuwa sai a nemi izininta, izininta shine ta yi shiru” 1 wananan hadisi
yana nuna mana cewa akwai banbancin hukunci tsakanin bazawara
wacce ita ta fi haqqi ta yi zavi da kanta, budurwa kuwa ba ta da zavin
haka abin da za a yi mata kawai shine shawartarta, da neman izininta
yadda za a faranta mata rai, domin da ace budurwa da bazawara duk
hukuncinsu xaya ne da hadisi bai banbanta su da neman izininta ba,
Allah Madaukakin Sarki yana cewa:
Kuma akwai daga ayoyinSa Ya halitta muku matan aure
daga kanku, domin ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya
sanya soyayya da rahama a tsakaninku. Lalle a cikin
wancan akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani (Rum:
21)
Ya ku yan’uwa! Ku yi salati ku yi sallama ga mavuvvugar rahamar
Ubangiji wanda ya kankama akan shimfixar bautar Allah, wanda
kuma shine ya san Allah Haqiqa nin sani ya kuma ji tsoransa
haqiqanin jin tsoro, shugabanmu Annabi Muhammadu annabin
rahama, don Allah ubangijin mu da Mahalincin mu ya yi muku
umarni da hakan a inda yake cewa:
Lalle Allah da mala’ikunsa suna salati ga annabi, Ya ku
waxanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku
yi sallama domin amintarwa a gare shi (Ahzab: 56)
1 Imam Muslim
72
Muna roqon Allah ya yarda da shugabanmu da Abubakar da Umar da
Usman da Ali da sauran sahabbai baki xaya. Ya ubangijin mu kada
kabar wani zunubi namu a wannan wuri face ka gafarta shi, kada
kabar wani baqin ciki face ka yaye shi, ko wata buqata daga cikin
buqatun duniya da na lahira wacce a cikinta akwai yardarka mu kuma
a cikinta akwai maslahar mu face ka biya mana ita ka sauqaqa ta ya
Ubangijin halitta.
Yaku bayin Allah! Lalle Allah yana yin umarni da adalci da kyautatawa ma’abocin zumunta, kuma yana hani ga alfasha da abin qi da rarrabe jama’ah, yana yi muka gargaxi tsammanin ku kuna tunawa (Nahl: 90), ku miqe zuwa sallah Allah ya yi muku rahama.
73
9
Ni’imar Da Ke Cikin Aure
Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa muna yaba masa muna
neman gafararsa, muna neman taimakonsa, muna tuba a gareshi, muna
dogara da shi, muna kuma neman tsarin Allah da daga sharrin
kawunanmu, da miyagun aiyukanmu, muna kuma shedawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammad bawansa ne
kuma manzonsa ne, Allah ya yi daxin tsira a gare shi da alayensa da
sahabbansa har zuwa ranar sakamako.
Bayan haka:
Yaku bayin Allah! Ku ji tsoran Allah kuyi masa godiya
bisa halitta muku matan aure daga kanku, domin ku natsu
zuwa gare ta, kuma Ya sanya soyayya da rahama a
tsakaninku, lalle a cikin wancan akwai ayoyi ga mutane
masu yin tunani.
Ba shakka aure babbar ni’imace da Allah ya yiwa dan Adam maza da
matan su wacce Allah ya halitta musu ko ya yi musu umarni dashi ya
kuma kwaxaitar da su akan yinsa, Allah Maxaukakin Sarki yace:
ku auri abin da ya yi muku daxi daga mata; biyu-biyu, da
uk-uku da huxu-huxu, sannan idan kun ji tsoron ba za ku
yi adalci ba, to (ku auri) guda ko abin da hannayenku na
dama suka mallaka…. (Nisa’i: 3)
Kuma annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: “ya ku jama’a da matasa duk wanda yake da iko a cikin ku to ya yi aure
74
domin shi ne abu mafi sa a runtse ido yafi bayar da kariya ga farji”1
Hakan nan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi
a lokacin da yake maida martani ga waxansu mutane xayansu yace:
Ni zan yi ta sallah har abada”, shi kuma na biyu yace: “ni
zanta yin azumi tsawan rayuwa ba zan sha ba”, shi kuma
na uku yace: “ni kuma zan qauracewa mata ba zan yi
aure ba”, sai manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi yace: “shin kune kuka ce kaza da kaza?
to wallahi ni na fi ku jin tsoron Allah da taqawa a gare
shi, amma ni ina azumi ina kuma sha, sannan ina yin
sallah na kuma inyi barci, kuma ina auran mata, duk
wanda ya savawa sunnah ta ba ya tare dani.
Kuma lalle ne Haqiqa, mun aika waxansu manzanni daga
gabaninka, kuma muka sanya matan aure a garesu da
zuriyya” (Ra’ad: 38).
Don haka yin aure aikine da umarnin Allah, da aiki da da umarnin
manzonsa, da kuma samun jinqai da rabauta duniya da lahira. Kuma
yin aure bin hanya ce ta manzannin Allah, kuma duk wanda ya bi
tafarkin manzannin Allah ba shakka za a tashe shi da su ranar lahira,
kamar yadda a cikin aure akwai biyan buqata da farin ciki, da samun
kwanciyar hankali. Bugu da qari kuma a cikin yin aure akwai bayar
da kariya ga farji da tsare mutunci da runtse idanu, da nisantar fitina.
Kamar yadda a cikin aure akwai yawaita al’ummar musulunci, domin
ta hanyar yawaita ne al’umma za ta yi qarfi a rinqa jin tsoronta a
sauran al’ummomi, ta kuma samu ikon dogara da kanta matukar dai
tayi amfani da kowacce baiwa tata kamar yadda Allah ya umarce ta,
kamar yadda a cikin yin aure akwai tabbatar da alfahari da annabi tsira
da amincin Allah su tabbata a gare shi zai yi da al’ummarsa ranar
1 Imam Ahmad da Abu Dawud
75
alqiyama. Domin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi yace:
Ku auri mata da kuke qauna kuma masu haihuwa, don
zan fi sauran al’ummomi yawan mabiya da ku a ranar
alqiyama1
Hakan nan a cikin yin aure akwai samar da iyali, da kusanto da
mutane da junansu, domin surukunta ‘yar uwar dangantaka ce. Allah
Maxaukin Sarki yace:
Kuma shine ya halicci mutum daga ruwa, sai ya sanya shi
nasaba da surukunta, kuma Ubangijinka ya kasance mai
ikon yi (Alfurqan: 54).
Hakan nan a cikin aure akwai samun lada da kyakkyawan sakamako,
ta hanyar tsayuwa da haqqoqin mata da ‘ya’ya da kula da su.
Kuma aure sanadi ne na samun wadata, da yawaitar arziki, ba
kamar yadda ‘yan jari hajja da masu raunin tawakkali suke riyawa ba,
kamar yadda Allah Maxaukakin Sarki ya faxa:
Kuma ku aurar da gwauraye daga gareku, da salihai daga
bayinku da kuyanginku, idan sun kasance matalauta ne
Allah zai wadatar da su daga falalarsa. Kuma Allah
Mawadacine, Masani (Nur: 32).
Hakan nan ya zo a hadisi da aka karvo daga annabi tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi mutum uku haqqin Allah ne ya taimake su
sai a cikinsu ya ambaci wanda ya yi aure da nufin kamewa (daga barin
zina)2
1 Abu Dawud da Ibn Majah
2 Sunan Albaihaqi
76
Hakan nan an ruwaito sayyidina Abubakar Assiddik yace: “ku yiwa Allah biyayya a cikin abin da ya yi muku umarni da shi na yin aure, shi kuma zai cika muku alqawarin da ya yi muku na wadata ku”. An
Karvo daga Ibn Abbas Allah ya yarda da su “Allah ya kwaxaitar da mutane akan yin aure ya kuma yi muku alqawari wadata dacewa: Idan sun kasance matalauta allah zai wadatar da su” (Nur 32). Haqiqa aure
sanadi ne na gyaruwar kowane mutum, kuma sanadi ne na gyaruwar
al’umma ta fuskar addini da kyawawan xabi’u, a rayuwarsu ta yau da
ta nan gaba. Kamar yadda yake hanyace ta kare fitintinu da ke iya
tasowa sanadiyyar barinsa ko rashin damuwa dashi a sanadiyar
abubuwan da ke iya hana mutum yinsa.
Ba shakka yana da muhimmanci matuqa mu mayar da hankali
wajen nazarin matsololi da ke hana mutane yinsa da nufin kaucewa
mummunan tasiri da rashin yinsa ke jawowa. Waxannan matsaloli za
mu iya cewa guda uku ne muhimmai:
Kauracewar da dama daga cikin matasa maza da mata daga
aure, to da yawa daga cikinsu za ka iske ba sa son aure da hujjar cewa
aure yana hana cigaba da karatu, ba shakka wannan hujja ce mai rauni
kasancewar aure ba shine abin da zai hana cigaba ba da karatu da
samun nasarar samun ilimi ba. Kai a maimakon haka ma yana iya
kasancewar wani taimako ne wajen yin hakan, domin kuwa a duk
lokacin da mutum nagari ya yi dace da mace tagari aka samu danqon
soyayya a tsakaninsu kowanne ya zamo abokin taimakawa abokin
zamansa wajen karatunsa, da magance matsalolin rayuwa, kuma sau
da yawa za ka samu yawancin mutane sunayin dace, kuma sau da
yawa matasa maza da mata Allah yana yi musu baiwa da su samun
hutu da kwanciyar hankali wajen karatun na su wanda hakan yana
taimakawa. Don haka ya kamata da matasan da suka ruxu da waccan
hujja su ake dubawa don su gyara kuskurensu, su kuma tanbayi
abokansu waxanda suka yi aure, suka kuma ga alheri da kwanciyar
hankali a sanadiyyar auren wanda da hakan ne wancan tunani; zai
gushe.
Hakan nan menene zai yiwa mace amfani idan ta kammala
karatun da ba ta da buqatarsa, wanda a sanadiyyarsa kuma sai ta rasa
77
jin daxin aure da rayuwa ba tare da haihuwa ba, ta wayi gari ba ta da
‘ya’yan da za su tuna da ita bayan mutuwar ta.
Matsala ta biyu:
Wacce takan hana aure da samun alfanu mai matuqar yawa da
ke cikinsa, ita ce ta qin aurarwa da waxansu azzaluman waliyyai kan
yiwa ‘ya’yansu da sauran wanda ke da haqqin waliccin aurar da su, ba
shakka irin waxannan waliyyai ba sa jin tsoron Allah, kuma ba su
kiyaye haqqin waxanda suke qarqashinsu ba, irin waxannan waliyyai
suna mayar da walittakar da Allah ya damqa a hannunsu ta zamo abin
neman abin duniya, ba shakka wannan cin dukiyane ta hanyar varna.
Kamar yadda zaka iske cewa a lokacin da wani wanda ya cancanta a
addininsa da mutuncinsa ya zo sai su ba shi uzurin cewa wani ya riga
shi, suna yin wannan qarya ne saboda ko dai wata mugunta a
zuciyarsu ko don neman abin duniya. Ba shakka qin amincewa da
wanda ya cancanta a addini da kyawawan halaye savawa Allah ne da
manzonsa kuma cin amana ne, kuma tozarta quruciyar mace ne, kuma
lalle Allah zai yi musu hisabi akan haka ranar da dukiya da ‘ya’ya ba
za su yi amfani ba sai wanda ya iske Allah da kuvutacciyar zuciya.
Yanzu don Allah ace irin waxannan waliyyai suna da tausayi
kuwa da son addini kuwa? Su yanzu ba za su auna su gani ba da za a
ce sune aka hana aurar waxanda suke so yaya za su yi? Shin wannan
kaxai bai ishe su su yi tunani ba a lokacin da suke hana ‘ya’ya su auri
wanda ya cancanta a addini da kyawawan halaye?
Yanzu ace waxannan irin waliyyai ba za su ji tsoron Allah ba a
irin wannan bala’i da suke jawowa kansu? Da irin bala’in abin da suke
jawowa waxanda suke qarqashinsu. Don haka ma’abota ilimi suka
samar da mafita daga irin wannan matsala inda suka ce: duk lokacin
da waliyyi ya qi amincewa ya aurawa yarinya wanda ya cancanta ta
kuma amince da shi to waliccin zai koma ga mai biye masa. Wato a
misali idan mahaifi ya qi aurar da ‘yarsa ga wanda ya cancanta ta
fuskar addini da kyawawan halaye to haqqin nasa zai koma ga wanda
ya fi kowa cancanta da waliccin bayan shi, don haka sai wanda ya fi
kowa kusanci da shi ya aurar da ita. Waxannan sun haxa da ‘yan
uwansa ko ‘yan uwan mahaifinsa ko ‘ya’yansu.
78
Ba shakka idan mai neman aure ya kasance bai cancanta ba, ko
dai ta fuskar addininsa da xabi’unsa kuma ta ce ta amince da shi, shi
kuma waliyin ya qi amincewa, to yana da haqqin yin hakan, kuma
babu laifi a kansa koda kuwa za ta ci gaba da zama babu aure ne har ta
mutu, domin qin amincewar tasa alfanunta ne da kuma sauke nauyin
amanar da take wuyansa.
Matsala ta uku: wacce take hana aure da samun alfanunsa mai
tarin yawa itace tsadar sadaki da kayan aure, wanda ako da yaushe
suke faman hauhawa har aka wayi gari aure ya zamo kamar wani abu
mai kamar wuya, ko mai matuqar wuya ga masu son yin aure ta yadda
sau da yawa mutum ba zai iya yi ba sai ya ci bashi, ta yadda zai zama
kamar bawan mai binsa bashi: Haqiqa hanyar warware wannan
matsala ita ce masu faxa aji daga cikin waliyyan ma’aurata su fahimci
babban maqasudin aure su kuma san matsayin mace wacce Allah ya
sa su waliyyai a kanta, su fahimci cewa mace ba kadara ba ce da za a
sayar ko aqi sayarwa gwargwadon abin da aka kashe mata kuxi.
Haqiqa aure ba ana yinsa ne da manufar samun dukiya ba, a
maimakon haka shi aure sanadiyya ce ta samun wadata.
Allah muke roqo ya kyautata halayen musulmi duk inda suke,
ya kuma azurta su da fahimtar addini da aiki da basira a cikinsa, ya
kuma sanya su zamo masu tsare koyarwar addininsu su zamo masu
girmama mata, masu tsayar da rukunan addini kamar yadda ya
kamata, lalle shi mai yawan kyautatawa ne mai karamci.
Ina wannan Magana tawa ina neman gafarar Allah tare daku
baki xaya da sauran musulmi maza da mata ku nemi gafararsa lalle shi
mai yawan gafara ne da rahama.
79
Huxuba ta biyu
Godiya ta tabbata ga Allah shi kaxai, ina kuma shedawa Muhammadu
bawansa ne kuma Manzonsa ne Allah ya yi daxin tsira da aminci, da
albarka a gare shi da alayensa da sahabbansa.
Yaku bayin Allah!
Ba shakka mace ba kadara bace, don ba shakka matsayinta ya
wuce na kadara, lalle ita amana ce babba, kamar yadda take wani
bangare na iyalin mutum don haka in muka yi tunani ta wannan
bangaren muka kuma kai ga haqiqanin manufa za mu ga cewa lalle
kuxi ba su da wata qima, don haka cika kuxin sadaki ko kayan aure
abu ne wanda bashi da wata hujja, don haka sai mu koma kamar yada
ake a zamanin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi kamar yadda sayyidina Umar yake cewa:
ya ku jama’a kada kuyi tsada wajen sadaki, domin da ace
hakan wata daraja ce a duniya ko taqawa da manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fi
ku cancanta da yin haka. Manzon Allah tsira da amicin
Allah su tabbata a gare shi bai tava bayar da sadaki ga
xaya daga cikin matansa, kuma ba wacce aka tava bawa
sadaki daga cikin ‘ya’yansa da abin da yawuce auqiya
goma sha biyu ba, kuma ba shakka mutum ba zai gushe
yana biyan sadakin matarsa da tsada ba, har sai hakan ta
kasance dalilin tsanarta a zuciyarsa, har ta kaishi ya rinqa
cewa, lalle an xora min nauyi don har sai da na kusa
gazawa, ya kuma ce, sai da ya qarar da duk abin da ya
mallaka ciki har da igiyar rataya gorarsa.
Ba shakka idan muka koma ga yanayi na magabata na qwarai wajen
qaranta sadaki, al’amuran aure za su yi sauqi, albarkarsa ta yi yawa,
mata da maza kuma su amfana da yin hakan.
80
Kamar yadda tsauwalawa a al’amarin sadaki zai tilastawa maza
da mata da yawa su qauracewa aure ko su yi qoqarin haxuwa da juna
a waje, wanda yin hakan zai jawo masifu da wahalhalu masu yawa
waxanda ka iya kawo a sami sauyi na al’adu da yanayin
zamantakewar al’umma, kai a waxansu lokuta ma har da addini,
domin lalle cuxanya tana da tasiri matuqa wajen sauya waxannan
abubuwa.
Ya ku masulmai! Haqiqa akan sami da yawa daga cikin waliyyai
iyaye da waxansu da suke sharxantawa mai neman aure waxansu kuxi
da zai ba su, baya ga sadakin mace, to ba shakka yin hakan cin dukiya
ne da varna, domin kuwa shi sadaki gaba xayansa na macene. Allah
Maxaukakin Sarki yana cewa; “kuma ku baiwa mata sadakokinsu da saukin bayarwa” (Nisa: 4). sai ya jingina sadaki garesu. Sannan ya zo
a cikin hadisi daga annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi
yace: “Duk matar da ta yi aure bisa wani sadaki, ko alqawari kafin xaurin aure to nata ne, idan kuwa bayan xaurin aurene to na wanda aka bawa ne’’1
. Ku ji tsoron Allah ya ku bayin Allah! Ku bi
umarninsa da yace ku ba mata sadakinsu, kada ku sharxantawa
kawunanku wani abu daga cikinsa, domin yin haka cin dukiyane ba
tare da haqqi ba, kamar yadda kuma wasane da waliccin aure, domin
matuqa waliyyi ya yi haka to zai janyo masa ya aurarwa wanda ya fi
bashi kuxi, ya yi watsi wanda bai ba shi ba don maslaharsa ba ta
wacce za a aurar ba, kuma ba shakka yin hakan cin amana ne da
ha’intar haqqin waliccci, don haka ku yi qoqarin sauke nauyin
amanar da take kanku ku kiyaye haqqin walicci.
Ya ku waxanda su ka yi imani; kada ku yaudari Allah da
manzansa kuma ku yaudari amanoninku, alhali kuwa
kuna sane (Anfal: 27].
Ina faxar wannan magana tawa ina neman gafarar Allah ga kai na da
ku.2
1 Albaihaki
2 Daga kundin hudubobin masallatai masu alfarma biyu, tattarawar Khairi Sa’id
82
10
Haqqoqin ‘Ya’ya Akan Iyayensu
Maza Da Mata
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya yiwa bayinsa baiwa ta dukiya
da ‘ya’ya, ya kuma sanya hakan ta zama jarabawa don ya tantace
waxanda za su tsaya akan sauke nauyin haqqoqinsu, ya kuma ba su
kariya daga lalacewa, ya ware waxanda za su barsu kara zube, su
zame musu asara a nan duniya da kuma ranar da za a halarto da kowa,
ina shedawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake ba
shi da abokin tarayya, mulki na sa ne kuma shine mai mulki da
karamci.
Kuma ina shedawa Annabi Muhammad bawansa ne kuma
manzonsa ne wanda yake shine mai kira zuwa ga gaskiya da shiriya,
tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da alayensa da sahabbansa,
da waxanda suka biyo bayansu da kyaytatawa a magana da aiki da
aqida, Allah ya yi daxin tsira a garesu.
Bayan haka, ya ku mutane! Ku ji tsoron Allah, ku kuma
godewa ni’imar da ya yi muku ta waxannan ‘ya’ya waxanda Allah
ya yi muku da su, ku rene su ku koya musu ladabi bisa kyawawan
halaye, da aiyuka kyawawa, Allah Maxaukakin Sarki yana cewa: ‘’Ya ku waxanda suka yi imani, ku karewa kanku da iyalanku, wata wuta wanda makamashinta mutane da duwatsu ne. a kanta akwai waxansu mala’iku masu kauri, masu qarfi, ba su savawa Allah ga abin da ya umarce su, kuma suna aikata abin da ake umarninsu” (Tahrim: 6)
Ya ku muminai! ku kare iyalanku ta hanyar buxe musu kofofin
alheri da fuskantar da su akansu, tare da qarfafa musu gwiwa akansu,
ku bayyana musu gaskiya da amfanin riqo da ita, ku kuma yi musu
umarni da riqo da ita ku bayyana musu qarya da cutarwar da take yi,
ku kuma tsawatar da su da su qaurace mata. Don ba shakka, ku masu
83
kiwo ne akansu, kuma duk wani mai kiwo za a yi masa tambaya
dangane da abin da aka ba shi kiwo. Ba shakka duk wanda ya kyautata
kulawa da su ya rabauta, duk kuma wanda ya gaza wajen kula da su
haqiqa ya halaka ya tave.
Sannan ku sanarda su ginshiqan imani, waxanda sune imani da
Allah, da mala’ikunsa, da littatafansa, da manzanninsa, da imani da
ranar qarshe, da qaddara alherinta da sharrinta, ku kuma ladabtar da
su akan lazimtar rukunan musulunci, waxanda su ne shedawa babu
abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma lalle Muhammad manzon
Allah ne, da tsayar da sallah da bayar da zakka, da azumin watan
Ramadan, da zuwa Hajji xakin Allah mai alfarma. Haka nan ku yi
musu umarni da sallah tun suna da shekara bakwai, ku dokesu in suka
qi yinta idan sun kai shekara goma.
Kamar yadda ya zama wajibi ku koya musu yadda za su yi
tsarki da yadda za su yi sallah da abin da za su faxa a sallar tasu,
waxanda za su aikata da kuma waxanda za su nisanta, ku kuma dasa
musu son Allah da girmama shi a zukatansu, ku kuma bayyana musu
ni’imomin Allah na fili da na boye kevantattu da gama-gari, don yin
hakan shi zai cusa musu son Allah da tuna ni’imominsa a zukatansu.
Haka nan ku dasa musu son annabi tsira da amincin Allah su tababata
a gare shi a cikin zukatansu, ku kuma bayyana musu abubuwan da ya
aikata na alheri babba ga al’ummarsa, sannan kuma lalle shine tsira da
amincin Allah su tabbaa a gare shi wanda ya wajaba a yiwa biyayya, a
kuma gabatar da sonsa da umarninsa akan kowanne abin halitta. Haka
nan kuma ku bayyana musu halayen annabi tsaira da amincin Allah su
tabbbata a gare shi da alayensa, da sahabbansa masu karamci, da irin
abubuwa da suka yi na ibada mai matuqar girma, da gagarumin aikin
da suka yi don tabbatar da Allah ya bawa addini musulunci nasara,
wanda hakan ne ya sa suka wuce kowa, duniya da na lahira, su ka
kuma jagoranci mutane ga aikata alheri har sai da mutanen suka shiga
addinin Allah qungiya qungiya saboda abin da suka gani na halayen
manzon Allah tsaira da amincin Allah su tabbata a gareshi da
sahabbansa ba tare da an tilasta musu ba.
84
Haka nan ya zama wajibi ku koyar da ‘ya’yanku faxar gaskiya
da aikata ta, idan kun tashi yi musu magana kada ku yi musu qarya,
idan kuma ku ka yi musu alqawari kada ku sava alqawuranku. An
ruwaito daga manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a
gare shi yace: “Duk wanda yace da yaro zo gashi kuma bai bashi ba to ya yi qarya’’1 Domin matuqar kuma matuqar ‘ya’yanku suka ganku
kuna yin qarya to za su xauki qarya ba a bakin komai ba, kamar yadda
idan suka ga kuna sava alqawari hakan zai sa su xauki sava alqawari
ba a bakin komai ba.
Haka nan ku yiwa ‘ya’yanku horo akan kyautatawa bayin
Allah, da aiyuka na matunci ku yi musu gargaxi daga ta’addanci da
zalumci ku kuma dasa musu son muminai a zukatansu, ku nuna musu
cewa lalle mumini ga mumini kamar gini ne wanda sashensa yake
qarfafar sashensa, ku kuma nuna musu cewa abin daya zama wajibi ga
musulmi shine su zama al’umma xaya, don su taso akan sabo da juna,
da qaunar juna, da haxin kai. Ku ji tsoron Allah ya ku bayin Allah! ku
nemi ilimin fahimtar hukunce-hukuncen addininku, da tarbiyar
‘ya’yanku, ku tsayar da sallah. Ku yi salati ga ma’abocin muqami,
abin yabo ma’abocin tafkin da za a sha ruwansa, kamar yadda Allah
Madaukakin Sarki ya yi muku umarni da salati da sallama a gare shi
inda yake cewa: “Lalle Allah da mala’ikunsa suna salati ga annabi, ya ku waxanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi” (Ahzab: 56)
Ya Allah, ka yi daxin salati ga bawanka kuma manzonka,
annabinmu Muhammad da alayensa da sahabbansa. Ya Allah ka qara
yarda da shugabanmu Abubakar, da Umar, da Usman, da Ali da
sauran sahabbai baki xaya.
1 Musnad Ahmad da Sharhu assunnah na Baghawi
85
Hububa Ta Biyu
Godiya ta tabbata ga Allah shi kaxai, ina shedawa bubu abin bautawa
da gaskiya sai Allah shi kaxai yake bashi da abokin tarayya, kuma
annabi Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne, Allah ya yi daxin
tsira da aminci da albarka a gare shi da alayensa da sahabbansa baki
xaya .
Bayan haka, lalle ya wajaba a gareku ku kwaxaitar da
‘ya’yanku da suka iya karatu akan karatun littafai masu amfani, da
suka hada da litattafai masu daraja kuma kuvutattu daga sauya
ma’anonin Alqur’ani da littatafan hadisi ingantattu na annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi, irinsu littafin sheikh Abdur
Rahman As-sa’adi – Allah ya gafarta musu baki xaya, hakan nan
kuma litattafan tarihi ingantattu waxanda babu son zuciya a cikinsu,
musamman ma tarihin farkon musulunci kasancewar karanta tarihin
wancan lokaci zai qarawa mai karatu sanin halayen annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi da sahabbansa, ya qarawa mai
karatu son su, tare da fahimtar addini da take qunshe a cikinsu, haka
nan ku gargaxe su daga karatun littatafai masu cutarwa, waxanda ka
iya yin illa ga aqidar musulmi, ko ibadarsu, ko halayensu, sannan
kuma da karanta jaridu, da mujallu masu vatarwa waxanda suke
kunshe da jefa shakku da motsa fitina, ko waxanda suka yi nazari na
wani al’amari na addini ta fuskar da bata dace ba.
Ba shakka karanta irin waxannan littatafai masu cutarwa na iya
yin tasiri ga aqidar mai karatu, da sauya yadda yake kallon abubuwa,
ba shakka waxanda za su kuvuta daga wannan sai waxanda Allah ya
yiwa baiwa da ilimi da hikimar ban-bance tsakanin gaskiya da vata,
abubuwa masu amfani da masu cutarwa.
Ya ku muminai! Lalle nauyin da Allah ya xora mana dangane
da al’amuran ‘ya’yanmu yana da yawa, mu iyaye, mazanmu da
matanmu, muna roqon Allah wanda shine ya xora mana wannan
nauyi da ya taimakawa mana, ya kuma yi mana dace wajen gyaruwa
da samun damar kawo gyara. Don ba shakka da za ace kowanne
mutum zai gyaru ya gyara iyalinsa da al’umma ta gyaru, domin
86
al’umma ba komai bace face xaixaikun mutane. Ina neman tsari da
Allah daga shexan la’ananne.
“Lalle Allah yana yin umarni da adalci da kyautatawa ma’abocin zumunta, kuma yana hani ga alfasha da abin qi da rarrabe jama’ah, yana yi muka gargaxi tsammanin ku kuna tunawa (Nahl: 90).
Ku godewa Allah bisa ni’imominsa sai ya qara muku, kuma lalle
ambaton Allah shine mafi girma, kuma Allah yana sane da abin da ku
ke aikatawa. Ina fadin wannan magana tawa ina neman gafarar Allah
gareni da ku.
87
11
Saki Shine Ke Rushe Gidajen Aure
Godiya ta tabbata ga Allah, muna neman taimakonsa, muna neman
gafararsa, muna kuma neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu,
da miyagun aiyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar haqiqa shine
shiryayye, wanda kuma ya vatar ba mai shiryar da shi, kuma ina
shedawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shedawa
Shugabanmu annabi Muhammadu bawan Allah ne kuma manzonsa
ne, ya isar da saqo ya sauke, nauyin amfana, ya yiwa al’umma nasiha
ya yi jihadi wajen xaukaka addinin Allah matuqar jihadi ya barmu
akan hanya mai haske wacce hasken darenta dai-dai yake da na
ranarta, ba wanda zai kauce daga tafarkinta sai halakakke. Allah ya yi
daxin tsira da albarka bisa alayensa da sahabbansa da mabiyansa da
wanda suka biyo su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
Bayan haka, ya ku waxanda suka yi imani ku ji tsoron Allah
haqiqa nin jin tsoron sa kuma kuyi riko da addinin musulimci wanda
shine igiyar da bata tsinkewa, kuma ku nisanci duk wani nau‘ina sabo
ku sani cewa kafafuwan ku ba za su iya jurewa azabar wuta ba, kuma
ku sani cewa, mala’ikan mutuwa sai da ya qetare ku ya tafi ga
wasunku, kuma ba shakka wata rana zai tsallake waxansu ya iso gare
ku don haka ku zauna cikin shiri. Mai wayo shine wanda ya yiwa
kansa hisabi, yayi aiki domin abin da zai biyo bayan mutuwa,
kasashshe kuwa shine wanda ya biyewa son zuciyarsa ya rinqa yiwa
Allah buri,
Ya ku bayin Allah! a kullum aka wayi gari sai an bada labarai
da ke bayyana haqiqanin rayuwar da mutane suka tsinci kansu a
cikin, ta halin ko-in-kula da ladubban magana da taka-tsan-tsan da
abin da magana za ta haifar ta yadda za ka ga kalmomi suna ta faman
fitowa daga bakunan mutane amma su ba abin da ya dame su, irin
kalmomin da sau da yawa su kan iya jefa su cikin hanyoyin vata da
88
zubewar mutunci, kamar yadda za ka ga ba a xauki kalmomin a bakin
komai ba, don haka ba a waiwayawa a dubi abin da suka qunsa, irin
waxannan mutane ba su san cewa ba “Lalle wuta da tsinken ashana akan kunna ta, kamar yadda komai girman yaqi farkonsa magana ce’’ Ya ku mutane! Yanzu za ku yi mamaki idan aka ce muku kalma
xaya rak za ta iya zamowa gatarin da zai iya wargaza gidaje? ya lalata
zamantakewar aure? Shin za ku yi mamaki idan aka ce muku kalma
xaya na iya sauya rayuwar mai ita, daga rayuwa mai daxi da
kwanciyar hankali ta jefa shi cikin tashin hankali da bala’i? Shin
xayan ku zai yi mamaki idan aka ce masa akwai wata kalma guda
xaya da za ta iya motsa xaixaiku da jama’a ta haifar da buqatar a yi ta
ban baki da neman alfarma kafin a warkar da raunin da ta haifar?
Ba shakka wannan kalma itace ta kansa idanuwa kuka, ta sanya
zukata su yi baqin ciki, ta tsoratar da su, ba shakka wannan kalma ‘yar
qarama ce sai dai abin da ta qunsa yana da girma, ba shakka wannan
kalma ta kan jefa kunnuwa cikin tsoro saboda tsananinta, ta mayar da
farin ciki ya koma baqin ciki, ta mayar da murmushi ya koma yaqe,
ba shakka wannan kalma itace kalmar saki, itace saki, ko ka san
menene saki? Ita kalmar saki itace kalmar bankwana, ta rabuwa ta
rikici ta vatawa da juna. Don Allah ku bani labarin gidaje nawa
wannan kalma ta rusa, danqon zumunta nawa ta raba, da ke tsakanin
‘yan uwa da masoya. Wayyo Allah saki wane irin lokaci ne na tashin
hankali haka nan lokacine na baqin ciki, ranar da mace za ta ji da
kunnuwanta cewa an sake ta, ta share hawayenta ta yi bankwana da
mijinta, kai wannan lokaci ne damuwa wanda a lokacin ne kumatun
mace zai bushe, a lokacin da za ta tsaya a kofar gida don ta yi masa
kallo na qarshe, ta yi masa duba na bankwana, da ba za a manta da su
ba, kai wannan lokaci ne na baqin ciki a lokacin da kwanciyar hankali
za ta naxe tabarma daga farfajiyar wancan gida na musulmi mai
albarka.
Ya ku bayin Allah ; ba shakka zamantakewar aure wani nau’ine
na musamman na soyayya da ke zuciya, wanda a duk nau’oin soyayya
ba shi da abokin haxi, kasancewar shine abin da ke sa kowanne daga
cikin ma’aurata ya sami natsuwa, wanda kuma a sanadiyyarsa ‘yan
89
adam biyu su ke haxuwa ta yadda da kowanne xaya daga cikisu zai
cike gurbin da xan uwansa ya gaza, kamar yadda haxuwa da za ta kai
ga samar da wani mutum irinsu “kuma Allah ya sanya muku matan aure daga kawunanku, kuma ya sanya muku daga matan auren ku xiya da jikoki kuma ya azurta ku da abubuwa masu daxi, shin fa da qarya suke yin imani, kuma da ni’imar Allah suke kafirta? (Nahl: 72)
Ba shakka lalacewar zamantakewar tsakanin ma’aurata ta kan
kunna wutar rabuwa, yawan faxace-faxace kuma ya qara rura ta, don
da ce ma’aurata za su so junanasu so na gaskiya, kuma ko wane daga
cikinsu ya shaqu da xan uwansa da an sami qauna a tsakaninsu wanda
a sanadiyyar hakan zai qaunaci iyalin xan uwansa, domin kuwa qauna
tsakanin ma’aurata na daga cikin zamantakewa wanda hakan zai jawo
danqon zumunta tsakanin dangin kowannensu a sami danqon qauna
tsakanin ma’aurata da dangin junansu. Haka nan irin wannan danqon
zumunci shine abin da zai mamaye tunanin al’umma. Don haka duk
wani abu da za a samu na daidaito a tushen ginin al’umma zai kawo
natsuwa da kwanciyar hankali a tsakaninsu baki xaya, kamar yadda
duk wani abu da ka iya kawo barazana ga zamantakewar aure zai
zamo barazana ce gare su baki xaya, ya cutar da su ya kai su ga
halaka, haka nan kuma duk wanda bashi da alheri ga iyalinsa, ba zai
zamo alheri ga al’umma ba. Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gareshi yace:
Mafi alherinku shine mafi alheri, ga iyalinsa kuma ni nafi
ku alheri ga iyalina, Tirmidhi ya fitar da shi da isnadi
ingantacce.
Ya ku bayin Allah! Haqiqa Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gareshi ya faxa a shahararren hadisinsa: “ka zavi ma’abociyyar addini sai ka ga albarka” Bukhari da Muslim.
Ba shakka wannan mace ita ce wanda shari’ah ta kwaxaitar da a
nemi aurenta, ta kuma yi addu’a mara kyau ga wanda ya nemi auren
wacce ba irintaba, ya nuna ba ya sonta ya qyale ta.
90
Kuma abu ne sannanne ga kowa cewa ba ta yadda za a yi
zuciyar musulmi ta nemi mai addini har sai shi kansa ya kasance
zuciyarsa tana danfare da addini ya kasance kuma zuciya ce mai
tsarki, wanda kuwa yake da irin wannan hali ba makawa za a azurta
shi da qauna da soyayya tsakaninsa da matarsa, domin kuwa hakan na
daga nau’in kasancewar sai hali ya zo xaya ake abota, ta hanyar yin
kama da juna a xabi’u da siffofi masu kyau. Wanda kuma savanin
haka shine na kama da juna a munanan siffofi da halaye na kaskanci
waxanda ba za su samar da soyayya ko qauna ba.
Manzon Allah tsira da amanincin Allah su tabbata agareshi
yace:
Mafi alherin daxin duniya itace mace ta qwarai” Muslim
ya ruwaito shi. Hakan nan matuqa akwai addini a wajen
miji da matarsa to duk irin savawar da suka samu, da
yadda suka juyawa junannsu baya, da irin yadda
zukatansu suka yi qunci, to ba shakka sai sun sami
hanyar warware kowanne irin rikici, don babu wanda zai
tsaurara addini face ya yi galaba akansa, shi kuwa
addinin sauqine da tausasawa da rahama da yafiya,
kamar yadda yake kulawa da riqon alqawari da xaukakar
mutunci da nisanta shi da duk abin da zai iya kaiwa ga
rage daraja ko qaskanta. Haka nan duk wanda waxannan
suka zamo halayensa to ba shakka, ba zai tava qasa a
gwiwa wajen aikata abin da ake yi masa umarni da shi a
cikin fadar manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shiba ‘’Da ace zan umarci wani ya yiwa wani sujjada da na umarci mace tayiwa mijinta sujjada’’ Tirmidhi ya fitar da shi kamar yadda ya zo a
ingantattacen hadisi, da inda yake cewa “Ina yi muku wasiyya da ku riqe mata da alheri” Bukhari da Musulim
sun haxu akansa. Haka nan sakamakon addinin mace
yana bayyana ne a irin abin da ya zo a cikin hadisi
sayyidatina A’isha Allah ya yarda da ita wanda a cikinsa
91
take cewa: “Ya ku jama’a mata da ace kun san haqqoqin da mazanku suke da shi akanku da xaya daga cikinku ta rinqa share qafar mijinta da sararin fuskarta
Ba shakka, babu wautar da ta kai miji ya rinqa munanawa matarsa,
kamar yadda ba shashancin da ya kai mace ta munanawa mijinta.
Don haka, ku ji tsoron Allah ya ku bayin Allah! Kuma ku nemi sanin
hukunce-hukuncen addinininku da zamantakewarku ta aure.
Ku yi salati da sallama -Allah ya yi muku rahama – ga
fiyayyen wanda ya tsayar da sallah, ma’abocin muqami abin yabo, da
kwari wanda za a sha ruwansa, kamar yadda Allah ya yi muku
umarni da yi masa salati da sallama inda yake cewa: “Lalle Allah yana yin umarni da adalci da kyautatawa ma’abocin zumunta, kuma yana hani ga alfasha da abin qi da rarrabe jama’ah, yana yi muka gargaxi tsammanin ku kuna tunawa (Nahl:90) Ya Allah ka yi salati da aminci
ga bawanka kuma manzonka annabinmu Muhammad da alayensa da
sahabbansa. Ya Allah ka yarda da khalifofinsa shiryayyu,
shugabanmu Abubakar, da Umar, da Usman da Aliyu da sauran
sahabbai baki xaya.
92
Huxuba Ta Biyu
Godiya ta tabbata ga Allah shi kaxai, ina shedawa babu abin bautawa
da gaskiya sai Allah shi kaxai yake ba shi da abokin tarayya, ina kuma
shedawa lalle shugabanmu Annabi Muhammad bawansa ne manzonsa
ne, Allah ya qara tsira da albarka a gare shi da alayensa dasahabbansa
baki daya,
Ya ku mutane! Lalle saki kalma ce ba wanda zai yi musun
muhimmancinta da buqatar ta da ma’aurata ke da ita a lokacin da
rayuwa qarqashin inuwa xaya ta gagara, a lokacin da tsanar juna ta
kai mutuqa ta yadda zai yi wuya asami qaunar juna, to ya zama wajibi
su rabu bisa kyautatawa, cikin mutumci kamar yadda suke hulxa don
cimma waxancan manufofi ta gagara.
Kuma in sun rabu Allah zai wadatar da kowanne daga
yalwarsa, Kuma Allah ya kasance Mayalwaci Mai
hikima [Nisa’i: 30]
Kuma haqiqa Allah bai halicci ma’aurata da xabi’a iri xaya ba don
haka duk ma’auratan da suke zaton cewa su halittu ne dai-dai da juna
to ba shakka suna yin rayuwace ta mafarki domin idan ba haka ba ta
yaya miji zai yi tunanin cewa mace ta yi tunani da irin hankalinsa. Ko
ita ta yi zaton cewa ya yi tunani da yadda take ji a zuciyarta. “Kuma su matan suna da kamar abin da yake kansu, yadda aka sani. Kuma maza suna da wata daraja akansu (su matan)” (Baqarah: 228)
Haka nan ba ta yadda za a yi ace koda yaushe ana cikin zaman jin
daxi cikakke, don ba shakka wata rana sai an sami savani, guguwa ta
turnuqe. don haka sa rai da cikakkiyar kwanciyar hankali nau’i ne na
ruxin kai, don haka alamar hankali itace shirin jurewa yanayi mara
daxi da akan iya shiga tare da kaucewa yawan qorafi akansa.
“sa’annan idan kun qi su, to akwai tsammanin ku qi wani abu alhali
93
kuwa Allah ya sanya wani alheri mai yawa a cikinsa” (Nisa’i: 19)
Kuma manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a
gareshi yace:
Kada munini ya tsangwami mumina domin kuwa idan
ya qi wani hali na ta to zai amince da wani, Muslim ya
ruwaito. Wani mawaqi yana cewa:
Duk wanda yake bibiyar laifuka da nufin lalubosu, to ba
zai tava yin aboki ba har abada.
Kamar yadda zaka ga gidaje da yawa waxanda suka rasa ruhin addini
sun auka cikin muguntar juna, da qunci, matsalolin suka lulluve su ta
fuskar tunani da halaye da zamantakewa, kamar yadda an wayi gari a
yau, ana iya sakin mace a kan ma’auni xaya na nama wanda mijin ya
xamfara sakinta da shi in ta saya, ta yadda za ka ga waxannan suna
tafiya cikin duhu, suna aiyuka irin na wawaye, su rinka faxawa cikin
savon Allah, da zalunci. Kuyi salati da sallah –Allah yayi muku
rahama ga fiyayyen wanda ya tsayar da sallah, ma’abocin muqami
abin yabo, da tafki abin sha kamar yadda Allah yayi muku umarni da
hakan inda yake cewa:
Lalle Allah da mala’ikunsa suna salati ga annabi, ya ku
waxanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku
yi sallama domin amintarwa a gare shi (Ahzab: 56).
Ya Allah ka yi salati da sallama ga annabi, da sauran sahabbai baki
xaya.
94
12
Yawaitar Saki Ce Take Lalata Rayuwar Aure
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu, wanda ya raya zukatan
muminai da Alqur’ani da sunnar shugaban manzanni, Godiya da yabo
sun tabbata ga ubangijiinmu, bisa wannan falala bayyananniya, Ina
kuma shedawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake
bashi da abokin tarayya, mai iko kuma mai cikakkan qarfi, Ina kuma
shedawa annabinmu da shugabanmu Annabi Muhammad bawansa ne
kuma manzonsa ne, mai gaskiya da cika alqawari, ya Allah ka yi
daxin tsira, da aminci, da albarka ga bawanka kuma manzonka
Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa baki xaya.
Bayan haka! Ku ji tsoron Allah haqiqanin jin tsoron Allah, ku
kuma yi riqo da shiryarwar manzon Allah wanda ya xaukaka, ya ku
musulmai.
Ku sani cewa tsiran musulmi, da yin kyakkyawan qarshensa, da
samun kwanciyar hakalinsa, a duniya da lahira suna samuwane ta
hanyar yiwa kai hisabi, da tilasta ta akan bin abin da Allah yake so, da
nisanta da fushinsa. Allah Madaukakin Sarki yace:
Ya ku waxanda suka yi imani, ku bi Allah da taqawa
kuma rai ya dubi abin da ya gabatar domin gobe, kuma
ku bi Allah da taqawa. Lalle Allah mai kididdigewane ga
abin da kuke aikatawa” (Hashr: 18). Hakanan manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace:
“halal xin da Allah ya fi qi shine saki”
95
Ya ku bayin Allah! haqiqa saki ya yi yawa a yau, a sanadiyyar rasa
tsayuwar namiji a cikin waxansu al’ummomi masu yawa, wannan
kuwa ya biyo bayan gafala da aka yi da ginshiqin hukunce-
hukuncensa, wato littafin Allah da sunnar manzonsa da waxansu
mutane suke yi suka koma dogaro da waxansu littatafai gurvatattu
waxanda suka sauya haqiqan salon zamantakewa, suka lalata
zamantakewar aurensu ba tare da sun sani ba. Kamar yadda kafafen
yaxa labarai suka xauki kaso mai yawa na wannan lefi ta fuskoki
daban-daban na kallace kallace da ake yi koda yaushe, su kuwa sai
suka yi amfani da damar wajen cusa tunani mara kyau, da ra’ayoyi
jirkitattu dangane da zamantakewar aure, wanda hakan ya jawo mata
suka manta da tarihinsu.
Sau da yawa za ka iske akwai wani abin kallo wanda mata dubu
za su kalle shi a lokaci xaya, wanda da zarar ya zauna cikin
qwaqwalarsu ya kuma mamaye tunaninsu, sai su wayi gari ba su da
ikon zavi, a cire musu duk wata natsuwa, su wayi gari suna
kwaikwayon abin da suka gani dubunnan lokuta ta hanyoyin daban-
daban, a dubunan yanayi, don haka kada kuyi mamaki bayan haka
idan mai doki ya koma kuturi, namiji ya wayi gari ya koma mace, kai
wani abin mamaki ma waxansu daga cikin kafafen yaxa labarai suna
shelanta cewa gudunmawa suke ba mace, kuma riga kafi suke bata,
irin wanda za a yiwa mutum allura da waxansu qwayoyin cuta don
gar kuwar jikinsa ta saba da su, ta yadda a lokacin da annoba ta zo
garkuwar jikin ta riga ta gane su don haka sai taba jikin kariya. Amma
a haqiqanin al’amari babu abin da suke qarawa da waxannan
abubuwa da suke da’awar magancewa sai tsanani, domin kuwa
wannan abin da waxannan kafafen yaxa labarai suke, ba komai ba ne
face haikewa annoba a lokacin da take kan ganiyarta.
Ba shakka wani mai magana yayi gaskiya da yake cewa:
Ashe magani na cutarwa yake yi, kamar yadda mashayin
giya kan yi maganin shan giya da shan giya.
96
Haqiqanin abin da yake faruwa a yau ya ku muslmi shine, cikin
gidajen musulmi suna tasirantuwa da waje, kamar yadda kowacce
guguwa ta taso da ta shafi sakaci da addini, da jahilci ta taso a waje sai
ta yi naso ta shiga cikin gidaje ta yadda ba wanda zai kuvuta daga
bala’inta sai wanda Allah ya kare.
Ya kuma kamata mu sani cewa, rayuwar aure rayuwace ta
zamantakewar al’umma, don haka ya zama tilas kowacce al’umma ta
kasance ta na da shugaba da za a koma wajensa a duk lokacin da aka
yi savanin ra’ayi ko bukata ta taso, kuma ba shakka namiji ya fi
cancanta da wannan shugabanci domin shine ya fi sanin maslaha, ya fi
iko wajen aikata abubuwa, saboda abin da Allah ya yi masa baiwa da
shi na ikon yin hakan.
Kuma ba shakka, irin waxannan abubuwan da mace take koya a
yau daga abubuwan da suke faruwa a maqotanta na hamayya da
namiji a haqqinsa na jagoranci na daga cikin sakin hanya
madaidaiciya da vata bayyananne.
Kamar yadda jagorancin namiji a gidansa ba ya nufin cewa an
bashi haqqin yin kama-karya, da nuna fin qarfi domin kuwa aure ba
alaqa ce ta bauta ba, kamar yadda ba alaqa bace ta cin moriyar jikin
mace, Ba shakka al’amrin ya wuce haka. Haka nan kuma kowanne
daga cikin ma’aurata mutum ne cikakke, yana da hankalin da zai yi
tunanin da shi da zuciya da yake so ko qi da ita, don haka ya zama
wajibi a ba mace haqqinta duk da cewa miji shine shugaba akanta.
“Kuma su matan suna da kamar abin da yake kansu, yadda aka sani“ (Bakara: 228)
Kamar yadda shugabancin namiji baya nufin ya wadatar da shi
daga matarsa, Allah Madaukakin Sarki yana cewa: “Su tufane a gareku kuma ku tufane a garesu” (Baqara: 187).
Kuma ba shakka sakin mata da ake yi ya yi yawa a yau, kamar
yadda yawancin masu saki xayan biyu ne, ko dai mutumin da ya yi
aiki da ikon da yake da shi ya yi watsi da tausayi, ya wayi gari a
gidansa shugabane mai mulkin kama-karya kawai wanda ba zai
xanxani soyayya da kwanciyar hankali ba, ballantana zaman gaskiya
da jin daxi.
97
Ko kuma mutumin da ya biyewa son zuciyarsa ya yi watsi da
nauyin shugabancin da yake kansa, ya wayi gari a gidansa ya zamo
bawa. Kamar yadda saki ya yi yawa saboda hassada da munafunci da
suka yi yawa, waxanda suka jinkirta xabi’u suka sauya yanayi, suka
mayar da qauna da haxin kai suka zamo daliline na qiyayya da
rabuwar kai. Sau da yawa za ka iske ‘yan uwan ma’aurata suna da
waxansu dalilai na bayyane da ke iya zamowa sababi na kai tsaye na
faxawa cikin rikice-rikice a waxansu lokuta uba ko uwa ko xan uwa
ko ‘yar uwa kan iya shishshigi cikin al’amarin ma’aurata wanda hakan
zai sa miji ya shiga ruxanin wanda zai goyi baya, shin iyayensa
newaxanda suka haife shi jariri, suka yi renonsa tun yana yaro
qarami? Ko matarsa wacce ta qauracewa gidansu da ‘yan uwanta da
mahaifanta duk dominsa.
Ba shakka irin waxannan matsaloli suna da wahalar warwarewa
komai qanqantarsu,
Ba shakka wannan shishshigi a cikin gidajen aure shine ke
zama barazana, ga da yawa daga cikin gidajen aure, yanzu don Allah
waxannan mutane kome suke nema da za su yi ta faman kai hari ga
gidajen aure? su rinka shigowa gidaje ta bayan gida? su kekketa
suturarsa su da alfarmar hijabansa, su wargaza zamantakewarsa su
jefa ma’aurata cikin qiyayya da juna?.
A haqiqanin gaskiya, irin waxannan mutane suna da
mummunan tasiri ga gidajen aure, waxanda sune suke haxuwa su
samar da al’umma. Ba shakka duk wani mai hankali ba zai gaza
fahimtar cewa sharrinsu sharrine da yake iya shafar kowa ba, haka nan
abin da suke aikatawa fitina ce a ban qasa da varna babba.
Ya ku bayin Allah!
Ba shakka alaqar aure, alaqace mai qarfi, kuma mai nisan zango, don
haka Allah ya yi rahama ga dukknan mutumin da ya ke kyakkyawan
hali, mai tsarkin zuciya, mai sauqin hali da tausayi, da jinqai, mai
tausayin iyalinsa, wanda ba ya xorawa mace abin da ya fi qarfinta.
Haka nan Allah ya yi albarka ga matar da ba ta neman mijinta ya yi
98
abin da ya fi qarfinsa, ba ta yi masa magana ta gatsali, manzon Allah
tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yace: “lalle mafi sharrin mutane a wurin Allah ranar alqiyama shine mutumin da zai san sirrin matarsa, ita ma ta san sirrinsa sannan kuma ya rinqa yaxa shi’’ Abu Dawud ya rawaito. Manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi yana cewa: “Idan mace ta sallaci salloli biyar, ta kikaye farjinta, ta yi biyayya ga mijinta, za ta shiga aljanna ta duk qofar da ta ga dama “ Ibn Hibban ya ruwaito.
Daga waxannan abubuwa za a fahimci cewa miji ba shi da
wanda ya fi dacewa da ya kasance abokinsa a rayuwasa, ya nemi
taimakonsa wajen sauke nauyin da yake wuyansa, kamar mace mai
kyakkyawar zamantakewa mai nagartattun xabi’u, wacce idan ya
kalleta zai yi farin ciki, ta yi masa biyayya idan ya yi mata umarni,
kuma ba za ta bari ya ga wani abu da baya so a kanta da dukiyarsa ba,
lalle irin wannan matar itace ginshiqin gida mai daxin zama kamar
yadda itace tushen tsayuwarsa.
Salihan mata masu xa’ane, masu tsarewa ga gaibi saboda
abin da Allah ya tsare (Nisa’i: 34).
Ya ku mutane! sau da yawa kowanne xaya daga cikinmu ya kan
tsinci kansa a yanayin da shi kansa bai amince da halin da yake ciki
ba, sai dai kawai ya jure, ya kuma bawa kansa uzuri gwargwadon
yadda zai zo masa, don haka ya kamata itama zamantakewar tsakanin
ma’aurata ta zamo haka, ta yadda kowanne daga cikinsu zai nemawa
xan uwansa mafita. Don ba shakka mumini a kullum shine yake nemo
uzuri, shi kuwa munafuki sai dai ya nemo kura-kurai, don haka ya
zama tilas a kauda ido daga kura-kurai in har ana son zamantakewa ta
yi dai-dai. “Ko akwai wanda bai taba kuskureba? wanda ko yaushe yake yin dai-dai”.
Kamar yadda babu abin da zai sauqaqa matsalolin rayuwa da
wahalhalu ga ma’aurata kamar junansu, kamar yadda ba wanda zai
rage raxaxin masifar da ta same shi ga kansa, ko waninsa kamar
matarsa, ga mace kuma mijinta, domin da haka ne wanda masifar ta
99
aukawa zai ji cewa yana da wani mutum na daban da zai qara masa
qwarin gwiwa ya xauke masa rabin nauyin masifar da ta auka masa.
Mu duba yadda uwar muminai Khadija Allah ya qara yarda da ita,
matar manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, yadda
ta zame masa kamar zuciyarsu xaya take a duk lokacin da wata masifa
ta same shi, ta kasance gareshi kai kace ba ta tava cewa babu ba, in
banda a kalmar shahada. Kamar yadda ba ta gushe ba tana qarfafarsa,
da kwantar masa da hankali kai kace a kullum haifar masa da sabon
farin ciki take yi saboda tausasassar zuciya, ta yi amfani da dukiyarta
wajen tallafa masa ta yi amfani kalamanta wajen xauke masa kewa da
cewa: “Ko kaxan wallahi Allah ba zai tava tozarta ka ba, domin kana sada zumunta, kana faxar gaskiya, kana xaukar nauyin talaka, kana kuma taimako bisa mastalolin rayuwa’’. Bukhari ya ruwaito.
Allah ya yi min albarka, ya yi muku albarka, a cikin fahimtar
Alqur’ani mai girma. Ina faxin wannan maganar tawa ina neman
gafarar Allah a gareni da gare ku, da kuma sauran musulmai maza da
mata ku nemi gafararsa zai gafarta muku domin lalle shi mai gafara
ne.
100
Huduba ta biyu:
Godiya ta tabbata ga Allah godiya mai yawa mai kuma tsarki da
albarka kamar yadda yake so, kamar yadda nake shedawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah, ina kuma shedawa lalle annabi
Muhammad bawansane kuma manzonsa ne, zavavve daga cikin
halittunsa kuma badaxinsa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi da alayensa da sahabbansa, da waxanda suka biyo bayansa har
zuwa ranar sakamako.
Bayan haka,
Anas xan Malik ya ruwaito hadisi daga mahaifiyarsa Ummu
Sulaim’yar Malahan Al-ansari Allah ya yarda da su yace: “wani xan uwa nawa ya yi rashin lafiya xan gidan Abu Xalhatu wanda ake kira da suna Umair a lokacin da abu Xalhatu baya nan sai yaronsa ya rasu, don haka sai Ummu Sulaim ta haxa shi, ta kuma ce kada ku bawa Abu Xalhatu labarin xansa ya rasu, ana haka sai ga shi ya dawo daga masallaci a lokacin kuma ta yi kwalliya, ta yi ado sai yace: Ko yaya xana yake? sai tace ai tunda yake bai tava samun natsuwa kamar ta yau ba, ta kawo masa abincin dare suka ci shi da abokansa, sannan ya je suka kwanta da ita cikin yanayi mafi cika da shaquwa da juna na tsakanin ma’aurata. Can da dare ya kawo qarshe sai tace da shi, ko menene ra’ayinka dangane da waxansu mutane da suka karvo aron wani abu, bayan sun yi amfani da shi sai masu kayan suka nemi su dawo musu da shi, sai suka nuna rashin jin dadi sai yace ‘’Lalle ba su yi adalci ba.sai tace ‘’To lalle wannan xa naka arone daga Allah, to yanzu kuma ya karvi kayansa. Nan take sai ya yi inna lillahi wa inna ilaihi raju’un ya yi wa Allah godiya” Ya kuma ce ba zan bari ki rinjaye ni a wajen haquri ba. Da gari ya waye sai ya yi sammako wajen manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, a lokacin da ya ganshi sai yace:”Allah ya yi muku albarka a darenku “
Bukhari da Musulim sun haxu akansa.
101
Allahu Akbar! Da irin wannan ne ya kamata ma’aurata su rayu,
da irin wannan ne ya kamata a yi rayuwa ta kwanciyar hankali da jin
daxi a zuciya da ‘ya’ya da dukiya. Sannan ku sani -Allah ya yi muku
rahama-’cewa kowanne daga cikin ma’aurata yana da haqqi akan xan
uwansa. Haqqine akan miji ya kula da ita, kada ya xora mata wani
abu sai wanda za ta iya, ya kuma zaunar da ita a gida wanda ya dace
da irinta, ya ilmantar da ita, ya tarbiyantar da ita ya kuma yi kishinta
ya bata kariya kada kuma ya ha’inceta, kada kuma ya rinqa nemo
laifukanta, ya kuma yi mata mu’amala ta kirki, manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi yana cewa: “ina yi muku wasiyya da riqe mata da alheri” Bukhari da Musulim sun haxu akansa.
An kuma tambaye shi menene haqqin matar xayanku akansa;
sai yace ‘’ka ciyar da ita idan ka ci ka tufatar da ita idan ka tufata kada
ka doki fuska kada kace mata mummuna kada kuma ka kaurace mata
face a gida ‘’Abu Dawud ya rawaito shi.
Haka nan yana daga cikin haqqin miji akan matarsa, ta yi masa
biyayya a abin da bai savawa shari’a ba, ta kuma bi shi gidansa, kada
ta yi azumin nafila sai da izininsa, kuma kada ta yiwa wani izini da
shiga gidansa sai da izininsa, kuma kada ta fita ba tare da izininsa ba,
ta gode masa bisa ni’imominsa, kada ta musa su, ta tsare masa
addininta da mutuncinta, manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gareshi yace: “Duk matar da ta rasu alhali mijinta yana mai yarda da ita za ta shiga aljanna’1’. To wannan kenan, ku yi salati -Allah ya yi muku rahama- ga
fiyayyen halitta wanda yafi kowa a cikin mutane, kamar yadda Allah
ya yi mana umarni da haka. “Lalle Allah da mala’ikunsa suna salati ga annabi, Ya ku waxanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi” (Ahzab: 56)
1 Tirmidhi da Hakim
102
13
Waliccin Mahaifi Nau’i Biyu Ne Na Yin Dole Da Na Izini
Godiya ta tabbata ga Allah, muna neman taimakonsa, muna neman
gafararsa, muna kuma neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu,
da miyagun aiyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar haqiqa shine
shiryayye, wanda kuma ya vatar ba mai shiryar da shi. Ina shedawa
babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad
bawansa ne kuma manzonsa ne. Bayan haka ya ku bayin Allah ku ji
tsoron Allah, haqiqanin jin tsoronsa ku kuma kiyaye dokokinsa a
sarari da voye.
Ya ku musulmai! Lalle Allah ya karrama xan adam a cikin
waxanda ya halitta ya fifita shi, ya kuma zavi waxanda ya fifita daga
cikinsu da annabta, da manzanci, daga cikin waxanda kuma ya fifita
mafificinsu shine annabi Muhammad xan Abdullah ya saukar masa da
wahayi dangane da haqqin xan adam da cewa: “kuma akwai daga ayoyinSa Ya halitta muku matan aure daga kanku, domin ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku. Lalle a cikin wancan akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani” (Rum: 21)
Kuma Allah Maxaukakin Sarki yana cewa: “Ya ku mutane ku bi Ubangijinku da taqawa, wanda ya halicce ku daga rai guda, kuma ya halitta daga gare shi ma’auransa, kuma ya watsa daga garesu masu yawa maza da mata. Kuma kubi Allah da taqawa wanda kuke roqon juna da (sunan) Shi, da kuma zumunta lalle ne Allah ya kasance akanku Mai tsaro ne. (Nisa’i:1)
Ya ku bayin Allah! abin da ake nufi da wallicci a shari’a shine
zartar da wani abu da aka faxa akan wani ba tare da banbancin cewa
ya amince ko bai amince ba shi kuwa waliyyi shine wanda zai aiwatar
da hakan, ya kuma tilastawa wani akan haka, daga cikin wannan
akwai abin da yazo faxar Allah Maxaukakin Sarki: “To idan wanda
103
bashi yake kansa ya kasance wawa ko kuwa rarrauna, ko kuwa shi baya iya shinbta, to sai waliyyinshi ya yi shibtar da adalci “ (Baqara:
282).
Hukunci waliyyi a xaurin aure shine sharaxi na tilas na
ingancin xauruwar aure. Don haka baya halalta ga mace ta aurar da
kanta, ko ta yi waliccin xaurawa wata aure, ko ta wacce fuska
budurwa ce ita ko bazawara, mai daraja ko qasqantacciya, mai hankali
ko kwarkwar, ‘ya ce ko baiwa, waliyyinta ya yi mata izini, ko bai yi
mata ba. In kuwa aka ce ta xaura auren to sai an warware shi, ko an
sadu da ita ko kafin saduwa, koda kuwa an daxe har an haifi ‘ya’ya.
To amma sai dai ba za ayi haddi akansa ba, saboda shubuha in kuma
an sami ‘ya’ya na mahaifinsu ne, za a kuma bayar da sadaki da aka
ambata in kuwa ba a ambata ba sai a bayar da sadakin irinta. Kamar
yadda hukuncinsa, irin na aure ingantacce ne ta fuskar wajabcin idda
da haramtawa mijin ‘yan uwansa na surukuntaka, da haxuwar
dangantaka. Dangane kuwa da gado, kafin a warwareshi an yi savani.
Maganar da ta ke cewa babu gado magana ce ta malam Asbagh kuma
maganace mai rauni.
Ibn al-mundhir yace: “ya tabbata daga manzon Allah tsira da amincin Allah su Tabbata a gareshi cewa “ba aure matuqar ba wali”
an ruwaito wannan hadisin daga Umar xan Khaxxab da Ali xan Abi
Xalib da Abdullahi xan Mas’ud da Ibn Abbas, da Abu Huraira Allah
ya yarda da su. Shine abin da suka tafi akansa. kamar yadda kuma
shine abin da A’isha ta tafi akansa Allah ya yarda da ita, kuma shine
ra’ayin Sa’id xan Musayyib da Alhasan Albasri da Umar xan Abdul-
Aziz da Jabir xan Zaid, da Sufyan As-sauri da Ibn Abi Laila da Ibn
Shibrimata da Ibn Almubarak da Ashshafi’i da Ubaidullah xan Hasan
da Imam Ahmad da Ishaq da Abu Ubaida da sauran xaukacin
ma’abota ilimi. Kuma ibn Almundhir yana cewa: “ba a sami wani daga cikin sahabbai da ya savawa wannan ba”
Daga cikin dalilan da suka tabbatar da hakan akwai abin da
Aisha Allah ya yarda da ita ta ruwaito cewa, manzon Allah tsira da
amincn Allah su tabbata a gare shi cewa: “duk matar da ta yi aure ba tare da izinin waliyinta ba to aurenta vatacce ne, aurenta vataccene,
104
idan kuma ya sadu da ita tana da sadaki da abin da ya halalta na farjinta, idan akai faxa to shugaba shine waliyin wanda ba shi da waliyyi 1.
Da kuma abin da Ibn Majah ya ruwaito da Dar-quxni daga Abu
Hurairah Allah ya yarda da shi, daga manzon Allah tsira da amincin
Allah su tabbata a gareshi yace "mace ba ta aurar da mace, kuma mace ba ta aurar da kanta mazinaciya itace take aurar da kanta”2.
Da kuma abin da aka ruwaito daga Ikrima xan Khalid yace:
“wata rana hanya ta tava haxa waxansu matafiya sai wata mace bazawara ta damqa al’amarinta a hannun wani mutum wanda ba waliyyinta ba ya aurar da ita, sai labari ya iske Umar sai ya sa aka yiwa wanda ya aurar da ita bulala ya kuma soke aurenta”. Shafi’i da
Dar-quxni suka ruwaito. An kuma karvo daga Shafi’i yace: “babu wanda yake da tsanani a sahabban manzon Allah dangane da auren mace ba tare da waliyyi ba, kamar Ali Allah ya yarda da shi domin ya kan yi bulala idan an yi shi" Darquxni ya ruwaito.
Haka nan an sanya sharuxa guda bakwai ga waliyyi kafin auren
da ya xaura ya inganta waxanda sune: Hankali, yanci, balaga,
kasancewarsa namiji, musulunci da rashin haramar hajji ko umra, da
rashin tilastawa. Haka nan akwai waxansu sharuxa biyu da aka yi
savani akansu, waxanda sune: adalci da shiriya, haka kuma makaruhi
ne waliccin fasiqi matuqar an samu waliyyi adali, to amma idan ya
xaura auren ya yi, kamar yadda shiriya ba sharaxi ce ta walicci ba,
kasancewar wauta ba ta hana walicci, don haka idan aka samu wawa
mai faxa aji yana iya xaura aure ba tare da izinin waliyyinsa ba
kuma ba tare da izinin wacce ke qarqashin ba, to amma mustahabbine
ya nemi izinin ta da izinin waliyyinsa a matsayin mustahabbi kawai
ba sharaxi ba.
Wauta nau’i biyu ce:
1 Abu Dawud da Tirmidhi suka ruwaito
2
105
a. wauta amma akwai addini, da hankali, da basira, duk wanda aka
siffanta da haka to ana xaukarsa a matsayin wawa mai faxa
aji, domin babu warwarar juna tsakanin faxa aji da wauta, don
ba tilasne idan akwai ra’ayi ya zamo an samu hangen nesa ba.
b. wauta haxe da raunin ra’ayi da basira da tauyaya wajen gane
abubuwa. Dangane da wawa mai faxa aji, mun bayyana
ingancin waliccinsa, da ingancin auren da ya xaura duk da cewa
mustahabbi ne waliyinsa ya duba abin da aka aiwatar, kamar
yadda yake da ikon soke shi to amma idan an riga an xaura
auren to ya inganta. Shi kuwa mai raunin ra’ayi ba shi da ikon
waliccin aurar da ‘yarsa ko watanta, kamar yadda ba shi da ta
cewa wajen zavarwa wacce yake yiwa walicci miji, kamar
yadda aka yi savani dangane da wanda zai yi waliccin xaura
mata auren shin mahaifinta ne, ko wanda aka yiwa wasiyya.
Ya ku bayin Allah! Shi kansa mahaifi bai inganta ya kasance waliyyi
ba har sai waxancan sharuxa bakwai da suka gabata sun cika akansa,
idan ko ya kasance haka to waliccin nasa ya kasu gida biyu: walicci
mai dole , da na izini dangane da walicci na dole mahaifi yana da shi
ga nau’i uku na 'ya’yansa mata waxanda sune: mahaukaciyar
budurwa da bazawara yarinya wacce ba ta balaga ba, kamar yadda
yake da shi ga ‘ya’yansa nau’i uku ne na maza waxanda sune:
mahaukaci da karamin yaro da wawa.
Dangane da wakilcinsa akan waxanda muka gabatar daga
‘ya’yan mahaifi yana da ikon ya aurar da su ga wanda ya so, ba tare
da izininsa ko shawararsa ba, ko da kuwa ta hanyar yi musu dole ne,
sai dai idan da wanda yake da nakasa da za ta tilasta soke auren, idan
hakane to ba shi da ikon yi musu dole akan auren su. Kamar yadda
yana da ikon aurar da su ga wanda bai dace da su ba, da wanda yake
qasa da matsayinsu ta fuskar dukiya, da sadaki qasa da na irinsu, haka
nan ba su da magana a irin wannan auren ko su ko wasunsu to amma
a cikin wannan akwai qarin bayani.
Idan mahaukaciya ta kasance budurwa to yana da ikon yi mata
tilas, yarinya ce ita ko bazawarace baliga, ba tare da banbancin cewa
106
haukan nata na koda yaushe ne ko kuwa yakan yanke ta hanyar
kasancewa ta kan warke a waxansu lokuta, kamar yadda ba wajibi
bane a jira lokacin warkewar ta, haka nan kuma bazawara, baliga
kuma haukanta xorarre ne to ita ma yana da ikon yi mata dole, ko da
kuwa ta haifi ‘ya’ya kuma xanta ba shi da magana matuqar akwai
waliyyi, kuma matuqar tana da shiryayye kasancewar ana gabatar da
waliccin mahaifi akan nasa idan kuwa harta kasance takan warke a
waxansu lokuta, to ba shi da ikon yi mata dole, sai ya jira lokacin
warkewarta. Haka nan mahaukaciya idan ba ta haihu ba, kuma ba
wanda aka yiwa wasiyya da ita, to al’amarinta yana hannun alqali
haka nan idan mahaifin nata ya kasance shima mahaukaci ne.
2. Dangane da budurwa kuwa, mahaifinta na da ikon yi mata dole,
yarinya ce ko babba ko baliga, ba tare da banbancin cewa tana farkon
balagarta ne irin wacce ana qirga ta a matsayin 'yan mata ko wacce ta
xau tsawon lokaci tana zaune a gidan mahaifinta ba tayi aureba harta
kai ko da shekara sittin ne, ta zamo wacce ta xauke tsammanin aure.
Kasancewar mahaifi yana da ikon yiwa 'yarsa wacce ta xauke
tsammanin aure shine abin da ya fi shahara a mazahaba. Ku ji tsoron
Allah ya ku bayin Allah, ku nemi sanin hukunce hukuncen addinin ku
ko kuwa ku rabauta da abin da Allah ya siffanta a faxarsa: "gidajen Aljannar zama, suna shigarsu su da waxanda suke kyautata daga iyayensu da matansu da zuriyarsu kuma mala’iku suna shiga zuwa gun su ta kowacce kofa "(Ra’ad: 23).
Ina faxar wannan magana tawa ina roqon Allah ya gafarta
mana, ni da ku da kuma sauran musulmi maza da mata ku nemi
gafararsa zai gafarta muku don shi mai yawan gafara ne mai rahama.
107
Huduba ta Biyu:
Godiya ta tabbata ga Allah wanda yake hukunci da gaskiya, da Adalci
kuma shine mafificin masu hikima, kuma mafi tausayin masu tausayi,
ina kuma shedawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai
yake bashi da abokin tarayya. Wanda shine abin bauta na farko da na
qarashe, kuma ina sheda cewa shugabanmu Annabi Muhammad
manzonsa ne kuma ya aiko shi da addinin gaskiya, don ya xaukaka shi
akan kowanne addini. Wanda kuma shine fiyayyen halittarsa baki
xaya, Allah ya yi daxin tsira a gareshi da alayensa da sahabbansa
masu tsarki da ikhlasi da waxanda suka biyo su da kyautatawa zuwa
ranar sakamako.
Bayan haka, ya ku bayin Allah! Lalle walicci dole yana faxuwa
akan budurwa a lokuta guda biyu:
Na xaya: lokacin da mahaifinta ya hukunta shiryuwarta, wato ya sakar
mata akala saboda abin da ya gani ya kuma sani na kyawun tunaninta,
don haka sai ya hukunta cewa, ta shiryu sai dai waliccinsa zai ci gaba
da kasancewa akanta, koda bayan hukunta shiriyarta, to amma
waliccin nasa ya sauya daga waliccin yin dole izuwa na neman izini
da zavi, ta yanda zai zamo ra’ayinta shine abin la’akari a kowanne
al’amari nata, ta yadda waliyyanta wanda shine mahaifi zai zamo
baya da haqqin komai sai xaura mata aure, haka ma xaukar nauyinta
ba zai faxi akansa ba har sai ta yi aure mijinta ya sadu da ita.
3. Bazawara yarinya kuwa wacce ba ta balaga ba, hukuncinta hukunci
ne na budurwa yarinya dai-dai da dai-dai wato waliyyinta na da ikon
yi mata dole, saboda qarancin shekarunta wanda shine dalilin yin
dolen. Kuma babu banbancin zamowarta bazawara ne ta hanyar aure
ingantacce, ko waninsa matuqar dai an gusar da budurcinta ko ta
wacce hanya ne. Mahaifi nada haqqin waliccin dole akanta matuqar
dai bata balaga ba. Idan kuwa ta zama bazawara ta hanyar aure ya
mutu kafin ta balaga, sai kuma ta balaga kafin aure na biyu to ba za a
108
yi mata dole ba, to malam Suhnun yana ganin cewa za a yi mata tilas,
a kowanne irin hali. Dangane kuwa da yarinya qarama wacce ta zamo
bazawara ta hanyar wani abu da ya bijiro, kamar sanda ko ta hanyar
tsalle, ko duka ko zazzavi ko tunkuxowar jinin haila, hukuncinta irin
na qaramar yarinya ne, idan kuwa ta zama bazawara ta hanyar
haramci kamar zina ta haihu a sanadiyyar haka waliccin yin dole zai
cigaba da kasancewa akanta.
Kamar yadda za a gabatar da mahaifinta a wajen walicci akan xanta
na zina, ko wanda ta samu ta hanyar faxe, to amma idan budurwa
baliga ta zamo bazawara ta hanyar aure, ko dai ingantacce ne ko
vatacce ba tare da banbancin kasancewarsa vatacce ko wanda da aka
yi savani akansa, ko wanda aka haxu akansa, to amma za a xage masa
haddi saboda shubuha, ta walicci. Waliccin mahaifi zai sauya zuwa ga
waliccin izini, duk wacce aka aurar da ita nau’in auren da an haxu
akan vacinsa, to amma zai kawar mata da haddi saboda shubuha.
kuma mijin ya sadu da ita, ya gusar da budurcinta sai kuma ta rabu da
shi ta hanyar warwarewar aure, ko saki, ko mutuwa mahaifinta ba zai
yi mata dole ba, don kuwa za a xauki auren ne a matsayin aure
ingantacce, saboda za a sadar da yaro ga mahaifinsa a kuma kawar
masa da haddi. Kamar yadda iddarta za ta yi ne a gidan mijinta wanda
take zaune a cikinsa, kuma babu banbancin kasancewarta wawiya ko
natsatstsiya, to amma idan auren ya kasance wanda aka haxu akan
vacinsa, ba a kuma kawar masa da haddi ba, to mahaifi na iya yi mata
dole, kasancewar za a sadar da shi da zina ne, domin kuwa an mayar
da ita bazawara ne ta hanyar haram.
Ku yi salati da sallama ga fiyayyen halitta shugabanmu Annabi
Muhammad, kamar yadda Ubangijinmu ya yi mana umurni da yin
hakan, “Lalle Allah da mala’ikunsa suna salati ga annabi, Ya ku waxanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi” (Ahzab: 56). Tsira da aminci su tabbata
a gareshi da alayensa da sahabbansa baki xaya ya ku bayin Allah!
“Haqiqa Allah yana yin Umurni da adalci da kyautatawa ma’abocin zumunta, kuma yana hani ga alfasha da abin da aka qi da rarrabe
109
jama’a, yana yi muku gargaxi tsammanin ku kuna tunawa (Nahl: 90)
ina mai faxar wannan magana tawa ina neman gafarar Allah a gare ni
da ku da duk wanda ya yi imani ya musulunta, daga kowanne zunubi
sai ku nemi gafararsa lalle shi mai yawan gafara ne mai rahama.
110
14
Savani Tsakanin Ma’aurata Da Hukuncin Adalai
Godiya ta tabbata ga Allah, muna neman taimakonsa, muna neman
gafararsa, muna kuma neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu,
da miyagun aiyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar haqiqa shine
shiryayye, wanda kuma ya vatar ba za ka tava samar masa majivincin
lamari mai shiryar da shi ba, ina shedawa babu abin bautawa da
gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad bawansa ne kuma
manzonsa ne.
Bayan haka, ya ku bayin Allah! Ku ji tsoron Allah haqiqanin
jin tsoronsa, kuma ku sani cewa duk lokacin da aka sami savani
tsakanin ma’aurata, lamarin zamantakewa ya yi tsamari a tsakaninsu,
to ko dai cutarwar daga matar take, ko daga mijin ko kuma dukkansu
biyun, in kuwa har al’amarin ya rikice aka rasa gane wanda ya shiga
haqqin wani to ga yadda za a lalubo bakin zaren, idan an gano cewa
cutarwar daga mace take ta zamo fanxararriya kenan, abin da ake nufi
da fanxararriya itace wacce take savawa mijinta, ta dena yi masa
biyayya, irin biyayyar da ta zamo wajibi akanta ta yiwa mijin, ko
kuma ta yi watsi da haqqin Allah Maxaukakin Sarki ya xorawa mace
ta bijirewa mijinta ko dai ta hanyar hana shi saduwa da ita, ko ta hana
shi jin daxi da ita koda kuwa ba ta hanyar saduwa bane, ko ta fita
zuwa wani wuri ba da izininsa ba, ta je inda ba ya so ko ta rufe masa
kofa ko ta hana shi shiga ko ta ha’ince shi a dukiyarsa ko ta aikata
alfasha, haka nan za ta kasance fanxararriya idan ta yi watsi da
haqqoqin Allah Maxaukakin Sarki ta hanyar dena tsarki ko wankan
janaba, ko ta sava wani abu da Allah Maxaukakin Sarki ya wajabta
mata. Allah Maxaukakin Sarki yace: “kuma waxanda kuke tsoron bijirewarsu to ku yi musu gargaxi kuma ku qaurace musu a cikin
111
wuraren kwanciya, kuma ku doke su. sannan kuma idan sun yi muku xa’a, to kada ku nemi wata hanya a kansu.” (Nisa’i:35)
In ana son magance matsalar fanxarewar mace to sai za abi
waxannan matakai kamar yadda ya zo a cikin nassin ayar na farko
shine wa’azi, wa’azi: shine ambaton abubuwan da za su tausasa
zukata ta hanyar kwaxaitarwa dangane da ladan biyayya ga miji, da
tsoratarwa game da azabar da take tattare da sava masa, da farko
mijine zai yi mata wa’azi da fatan ko za ta gyaru da wa’azinsa, idan
kuwa hakan ta ci tura sai liman ya yi mata, wa’azin ko wani da ke iya
wakiltarsa a irin waxannan al’amura a lokacin da ya kai masa qararta,
to idan kuwa har wa’azin mijin ko na liman bai yi amfani ba, sai ya
yi niyyar qaurace mata.
Abu na biyu: qauracewa: qauracewa itace dena saduwa da ita,
da qauracewa kwanciya da ita a shimfixa xaya, amma abin da ya fi
shine ya qaurace mata wata xaya, kamar yadda zai iya yin qari akan
hakan, to amma kada ya kai wata huxu. Idan kuma qauracewar ba ta
yi amfani ba sai ya doketa, duka wanda ba matsananci ba.Ya halalta
ga mijin ya yi duka ba mai tsanani ba matuqar qauracewar da wa’azi
ba su yi amfani ba. duka mai tsanani shine wanda zai sa mace ta sha
wahala wanda ka iya karya qashi ko ya raunata jiki. Miji ba shi da
haqqin yin dukan da ya wuce iyaka, koda kuwa yana sane da cewa ba
za ta dena abin da takeyi ba sai ya yi hakan, kamar yadda idan ya yi
mata duka mai tsanani to ya zamo xan ta’adda, ita kuma tana da
haqqin ta nemi saki ta kuma nemi a rama mata, saboda haka, dukan da
aka yi izini da shi shine duka mara tsanani, tare da kaucewa fuska,
kamar yadda abin da zai sa ayi dukan shine kasancewa dukan zai yi
amfani idan kuma ya san cewa ba zai yi amfani ba to ya kamata kada
ya daketa domin dukan ba zai sa ta dena abin da takeyi ba wannan
kuwa ya samo asali ne kasancewar duk wata hanya da za abi matuqar
ba za ta kai ga inda akeso ba shari’a ba za ta amince abi ta ba. To
amma fa wannan ya taqaita ne kawai ga duka, banda wa’azi da
qauracewa, waxanda miji zai aikata su koda kuwa ba ya zaton cewa
za su yi amfani.Wani abin lura shine kada ya tsallake xaya daga cikin
112
matakai zuwa wani da zaton cewa matakin da ya zo kafinsa ba zai yi
amfani ba.
Abu na huxu shine horo ta hanyar dukiya, matuqar miji yana da
ikon ladabtar da matarsa ko kuma ta hanyar yanke hukuncin alkali ne
to amma sai bai aikata hakan ba, to tana da haqqin kulawa ko kuwa ta
rinjaye shi ne, saboda da qabilancin danginta ne kasancewarsu mutane
ne irin waxanda ba za a iya zartar da hukunci akansu ba, idan haka ne
to ba ta da haqqin kulawa. Idan kuwa cutarwar ta hanyar miji ce, ya
kasance yana dukanta ko cutar da ita ko qaurace mata, ko tsine mata,
ko zagi ko cin zarafi, ita kuma tana son zama da shi haka ba ta son a
raba aurensu, ta kuma kai qara wajen shugaba ta tabbatar da cewa
yana cutar da ita, ko dai ta hanyar kawo hujja ko shi ya amsa da
kansa, ko al’amarin ya bazu, to shugaba zai bi waxannan matakai don
jan kunnen sa:
1. Shugaba zai yi masa wa’azi, ya ja kunnensa ya yi iyaka
qoqarinsa wajen hana shi gwargwadon ikonsa.
2. Idan wa’azi kuma da jan kunne ba su yi amfani ba, to sai ya yi
mata Umurni da ta qaurace masa a wurin kwana.
3. Idan qauracewar ba ta yi amfani ba sai ya yi masa barazana da
xauri ko duka. Malam Almuwaq yace: “haqiqa malamai sun ce ana iya xaure miji to amma ba zan iya tuna wani wuri da suka ce xaure mace ba”.
4. Idan barazanar ba ta yi amfani ba sai ya yi Umurni da dukansa
gwargwadon ijtihadinsa, to amma an shimfixa sharuxa guda
biyu kafin akai ga shugaba ya doke shi kamar haka; na farko sai
an tabbatar da cewa yana cutar da ita. Na biyu sai yana da
tabbas ko yana da cikakken zaton dukan zai yi amfani wajen jan
kunnensa idan kuwa har ba a tabbatar da cewar ya qetare iyaka
ba, kuma ba zaton cewa dukan zai yi amfani to ba abun da
shugaba zai yi masa inba wa azi da jankunne ba tare da duka ba,
hakan nan baya cikin nau’in cutarwa ya hanata fita yawon miqe
kafa ko na shaqatawa, ko kuma ya doketa duka mara tsanani a
sanadiyyar qin yin Sallah da abubuwan da suke kama da haka
ko a dalilin zai yi mata kishiya.
113
Kamar yadda ba shi da ‘yancin rufe kofa ya hanata shiga gida, haka
nan ba zai hanata kasuwanci na saye da sayarwa ba, matuqar ba fita
take yi ba, ko kevewa da wanda ba muharraminta ba, ko yana ji mata
tsoron lalacewa dalilin yin hakan. bai wajaba miji ya saki matarsa
fajira ba, kamar yadda ba za a tilasta masa ya saketa ba, kamar ta
kasance ba ta salla ko azumi ko ba ta wankan janaba, amma yana da
ikon ladabtar da ita to ya cigaba da zama da ita, in kuma ya ga dama
yana iya rabuwa da ita kamar yadda ya halalta ya karvi abin fansa
daga gare ta a matsayin khul’i. Wannan kenan, duk wanda ya san matarsa tana zina bai halalta
ya cutar da ita da niyyar ta fanshi kanta ba, idan kuma itace da kanta
tayi h akan ba tare da cutar da ita ba, to ya halalta ya karva.
A lokacin da dukkan waxannan matakai guda hudu ba su yi
amfani wajen jan kunnensa ya dena zaluntarta da cutar da ita ba, ta
kuma nemi saki sai shugaba ya sakar masa ita, ko ita kanta ta fanshi
kanta bisa sharuxan da muka ambata a baya dangane da cutarwa. Ina
faxar wannan magana tawa ina mai roqon gafarar Allah gare ni da
ku, da sauran musulmai maza da mata, ku nemi gafararsa lalle shi
Mai yawan gafarane Mai rahama.
114
Huxuba Ta Biyu
Godiya ta tabbata ga Allah, godiya mai yawa, mai albarka a cikinta,
kamar yadda Ubangjinmu yake so kuma ya yarda, ina shedawa babu
abin bautawa da gaskiya sai shi, shi kaxai yake ba shi da abokin
taraiya, ina kuma shedawa Annabi Muhammad bawansa ne kuma
mazonsa ne wanda ya fifita, kuma badaxinsa tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi da waxanda suka biyo su da kyautatawa har zuwa
ranar sakamako
Ya ku bayin Allah! Idan lefi ya kasance na ma’auratane su
biyu kuma kowanne daga cikinsu yana da’awar cewa na xaya ne, a
misali kowanne yana iqrarin xayan yana dukansa sai a aika masu
hunkuci guda biyu.
Ko yaushe ya kamata a aika masu hukunci biyu?
Ana aikawa da su ne a duk lokacin da aka sami keta haqqoqi
daga ma’aurata biyu, aka tabbatar da cewa kowanne daga cikinsu
yana shiga cikin haqqin xan uwansa to sai shugaba ya yi musu wa’azi
ya kuma ja musu kunne, sannan ya doke su gwargwadon ijtihadinsa.
haka idan mace ta yi kukan miji yana cutarta sai ta kai qararsa
wajen shugaba, sannan qorafin yayi yawa ba tare da wata hujjaba ba,
ko kuma kowannensu yana qorafi ba hujja a irin wannan yanayi
shugaba zai Umurci miji ya zaunar da ita tsakanin mutane biyu adalai
nagari, waxanda da za a iya karvar shedarsu, ya xora musu nauyin sa
ido akan al’amuaransu, da gano cutarwar da ake yi mata, kuma
matuqar ta natsu da su to bai halalta a mayar da al'amarin hannun
wasunsu ba.
Haka nan shugaba zai nemo labarinta daga maqotanta da kuma
waxancan mutane biyu da ta natsu da su, ya kuma halalta a karvi
shedarsu, to idan suka bada sheda akan cutarwar da yake yi mata, ya
tabbata cewa mijine yake shiga haqqinta, to sai ya bi matakan ladabtar
da shi da suka gabata, in har tana son ta cigaba da zama da shi ta
kuma aminta cewa ba zai cutar da ita ba. In kuma tana son rabuwa da
shi to sai ya sakar masa ita ta fuskar da muka bayyana.
115
Idan kuwa suka bayar da shedar cewa bijirewar daga ita ne to
sai yabi matakai da suka gabata wajen jan kunnenta. To idan kuwa
daga sune gaba dayansu sai yayi musu wa'azi yayi musu gargadi ya
dokesu gwagwadon ijtihadinsa
idan kuma qorafi ya yi yawa aka cigaba da rikici da samun
matsaloli, kuma aka kasa gane mai cutarwa don a gusar da cutarwar to
sai shugaba ya aika masu hukunci biyu daga vangaren kowanne daga
cikinsu. Ibn Asim a cikin Tuhfa yace "idan aka tabbatar da cutarwa ta yi tsanani, ga mace daga mijinta ta yi ta faman qara, a aika da masu hukunci biyu, da za su yi hukunci kamar yadda alqur'ani ya hukunta"
Allah Maxaukakin sarki yana cewa: “Ya ku waxanda suka yi imani, ku bi Allah da taqawa kuma rai ya dubi abin da ya gabatar domin gobe, kuma ku bi Allah da taqawa”.
Ina roqon Allah ya yi min albarka, ni da ku, a cikin fahimtar
Alqur’ani mai girma. Ina faxin wannan maganar tawa ina neman
gafarar Allah a gareni da gare ku, da kuma sauran musulmai maza da
mata ku nemi gafararsa zai gafarta muku domin lalle shi mai gafara
ne. “Haqiqa Allah yana yin Umurni da adalci da kyautatawa ma’abocin zumunta, kuma yana hani ga alfasha da abin da aka qi da rarrabe jama’a, yana yi muku gargaxi tsammanin ku kuna tunawa (Nahl: 90)
116
15
Shar'anta Aika Masu Hukunci Biyu
Huxuba ta Xaya
Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa muna kuma neman
gafararsa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da
munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da
shi, wanda kuma ya shiryar babu mai vatar da shi. Kuma ina shedawa
babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shedawa
Shugabanmu Annabi Muhammadu bawan Allah ne kuma manzonsa
ne. Allah ya yi daxin tsira bisa alayensa da sahabbansa da waxanda
suka biyo su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.
Ya ku mutane! Ku ji tsoron Allah ku kuma yi masa godiya da
ya halitta dominku mata daga kawunanku don ku sami nutsuwa da su,
ya kuma sanya qauna da tausayi a tsakaninku, lalle a cikin wancan
akwai ayoyi ga mutane masu tunana.Yaku bayin Allah! Asalin masu
hukunci biyu faxin Allah Maxaukakin Sarki: “Kuma idan kun ji tsoron savawar tsakaninsu, to ku aika da wani mai sulhu daga mutanensa da wani mai sulhu daga mutanenta. Idan sun yi nufin gyarawa, Allah zai daidaita tsakaninsu (ma’auratan). Lalle ne Allah ya kasance Masani Mai jarabawa” (Nisa’i: 85). Kuma kamar yadda aka
gani a abin da ayar ta bayyana cewa, masu hukuncine guda biyu kuma
daga cikin ‘yan gidansu, haka nan kuma aikin da aka xora musu shine
su yi sulhu, Umurnin da aka yi kuma na aikawa da su ana maganane a
cikinsa da shugabanni, da sarakuna, da jagorori, haka nan kuma ana
aike sune in an ji tsoron savani a tsakanin ma'aurata biyu. Haka nan
Usman xan Affan ya aika Abdullahi xan Abbas Allah ya yarda da su
shi da Mu'awiyya xan Abi Sufyan, Allah ya yarda da su labarin abin
da ya faru da Aqilu xan Abu Xalib da matarsa Fatima ‘yar Utbatu xan
117
Rabi'atu, xan Abbas yace: “An aikeni ni da Mu'awuya a matsayin masu hukunci aka ce mana in kuna ganin za ku hada ku haxa in kuma rabawa za ku yi ku raba," Ma'amar yace: “labari ya isheni cewa wanda ya aika su shine Usman xan Affan Allah ya yarda da shi” Da kuma
abin da Abdur-Razzaq ya fitar daga Ubaidatu Assalmani yace: “Na halarci majalisin Ali xan Abi Xalib a lokacin da wata mata ta zo masa da mijinta, kowanne daga cikinsu tare da wata tawaga ta mutane, sai kowanne suka fitar da mai hukunci, sai yace da masu hukunci biyu: "ko kun san abin da yake kanku ? Idan kun ga za ku haxa ku haxa in kuma kun ga za ku raba ku raba." Haka nan ba’a sharxanta amincewar
ma'auratan biyu ba, Qurxubi yana cewa: wannan isnadi ne ingantacce
kuma tabbatacce da aka ruwaito daga Ali ta hanyoyi tabbatattu daga
Ibn Sirin daga Ubaidatu. Haka Abu Amru ya faxa: Wannan maganar
ta sayyidina Ali Malik ya fitar da ita a Al-muwatta a bayanin saki
babin abin da ya zo dangane da masu hukunci biyu. Da kuma abin da
ya fitar da shi daga Abu Salama yace: In masu hukunci biyun sun ga
dama su raba in kuma sunga dama su hada."Haka nan Sha'abi ya fitar
da hadisi irinsa.
Sharuxan masu hukunci biyu:
An sharxanta wa ingancin masu hukunci biyu kowannensu ya kasance
musulmi, 'yantacce, baligi, namiji, adali, shiryayye, da fahimta
dangane da abin da ya shafi hakan, su kuma kasance daga 'yan
uwansu. Don haka kafiri ko bawa ko qaramin yaro bai inganta su yi
hukunci ba. Haka nan kasancewa namiji sharaxi ne don haka
hukuncin mace bai inganta ba, haka kuma jagorancinsu, kasancewar
shi mai hukunci shugabane da ya zama wajibi a yi koyi da shi. Haka
nan adalci shima sharaxi ne don haka wanda ba adali ba kamar yaro
ko mahaukaci ko fasiqi, duk waxannan hukuncinsu baya inganta.
Haka nan natsuwa, don haka hukuncin wawa baya inganta
domin shi wawa kasancewar shima yana buqatar kasancewa
qarqashin wanda zai yi masa walicci don haka ba zai zamo adali ba,
ko da kuwa ya fi duk waxanda suke raye a zamaninsa nagarta,
kasancewar xaya daga cikin sharaxin adalci shine ya kasance babu
118
wanda yake walicci akansa. Haka nan kuma idan wawa ya kasance ba
ya zaman kowa wato ba shida waliyyi ya kuma kasance ba adali bane
to ba za a karvi hukuncinsa ba. To amma wanda ya siffantu da abin da
ake xauka a matsayin adalci to adaline.
Dangane kuwa da fahimta akan haka: Abin da ake nema daga
wanda zai yi hukunci ya kasance ya fahimci hukunce hukuncen da
suke da dangantaka da cutarwa tsakanin ma'aurata. Don haka ba ya
inganta a sa jahili da bai san abin da aka xora masa nauyinsa ba ya yi
hukunci, domin sharaxi ne ga duk wanda za a xorawa nauyin wani
al'amari ya san hukunce-hukuncensa na shari'a, don haka wanda ba
masani ba hukuncinsa baya inganta, sai dai idan zai shawarci malamai
a abin da zai yi hukunci da shi. Idan ya yi hukunci da abin da suka ba
shi shawara to za a zartar da hukuncin nasa.
Kamar yadda kuma an sharxanta cewa, tilas ne daga 'yan uwan
miji a samu mai hukunci da mai hukunci daga 'yan uwan mata,
wannan sharaxi wajibi ne domin masu hukunci biyu ba za su kasance
ba sai daga ‘yan uwan miji da na matar saboda abin da nassi ya zo da
shi, kuma kasancewar sune suka fi sanin abin da ke faruwa tsakanin
ma’auratan, suka fi sanin xabi’unsu, don haka za su fi kowa iya sanin
hanyoyin da za su gyara tsakaninsu, don haka sun fi cancanta fiye da
wani bare. Sannan kasancewar suna daga cikin ‘yan uwansu, hakan
zai fi ba su dama su yi qoqari matuqa wajen yin gaskiya da kaiwa
qololuwa wajen tausasawa.
Idan kuwa a ‘yan uwansu ba a sami wanda zai dace da hakan
ba, sai a aika waxanda ba su ba daga waxanda ba na kusa da suba,
kuma mustahabbi ne su kasance waxanda suka sansu, in ba haka ba to
a samo a maqotansu don maqoci ya fi kowa sanin halin da maqocinsa
yake ciki.
Ina faxin wannan magana tawa ina mai neman gafarar Allah
gare ni da ku da sauran musulmi maza da mata daga kowanne zunubi,
ku nemi gafararsa zai gafarta muku lalle ne shi mai yawan gafara ne
mai yawan rahama.
119
Huxuba ta biyu
Godiya ta tabbata ga Allah shi kaxai, ina kuma shedawa babu abin
bautawa da gasikya sai Allah, kuma annabi Muhammad bawansa ne
kuma manzonsa ne, tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi Allah
ya yi albarka a gare shi da alayensa da sahabbansa.
Ya ku mutane! Ya zama wajibi ga masu hukunci biyu su yi
sulhu tsakanin ma’aurata biyu ta kowacce fuska mai yiwuwa, Allah
Maxaukakin Sarki yace: “idan sun yi nufin gyarawa Allah zai daiadaita tsakaninsu” (Nisa’i: 35). Ma’ana idan masu hukunci biyun
suka yi nufin gyarawa to Allah zai haxa kan ma’auratan biyu.
Wannan ita ce maganar Abdullahi xan Abbas da Mujahid da waxansu
su ka tafi akansa. Abin da da ake nufi da gyara a nan shine aikata abin
da ya fi zamowa gyara tsakanin ma’aurata biyu, ba wai lalle ana nufin
sulhu wanda yake savanin rabuwa ba, don sau da yawa yana
kasancewa abin da ya fi zamowa gyara shine a rabu, kamar yadda
yake iya kasancewa kuma cigaba da zama aure.
Wajibi na farko da ke kan masu hukunci shine, su haxa kansu
bisa zaman lafiya, da kyautata mu’amala matuqar sun sami damar yin
hakan. Idan kuwa suka gano wanda yake yin zalunci sai su karvi
haqqi daga gareshi su damqawa abokin zamansa, su tilasta shi akan
janye cutarwar, za su yi hakan ne da farko ta hanyar wa’azi da jan
kunne da hana shi, idan sun dawo sun koma yadda suke to sai su
qyalesu, idan kuwa sun ga kansu ya rabu, an kasa shirya tsakaninsu,
kuma al’amarin yaqi ci yaqi cinyewa bayan sun yi iyakar bakin
qoqarinsu wajen hada kansu iyakar iyawarsu, bayan sun tunatar da su
Allah da zaman tare, amma abinda ya fi zama dole shine su nemo
wanene ya fanxare a cikinsu, idan har suka gano wanda ya fanxare a
cikinsu don matuqar sun gano wanda ya fanxare al’amarin zai zo
musu da sauqi. Daga nan kuma in sun ga cewar rabuwar itace tafi to
shike nan.
Hanyar da za su bi wajen gano haka kuwa itace, kowanne ya
keve da xan uwansa, kevewa wacce ba za ta savawa shari’a ba, ya yi
120
masa magana da cewa, kai kuwa menene yake vata maka rai dangane
da abokin zamanka? In har kana da buqata ko ki na da buqata zamu
nuna masa laifinsa. Bayan sun saurari kowanne, sun tattara bayanai,
sai a duba idan ya tabbata cewa miji shine yake da laifi yake cutar da
ita ba ya son cigaba da zama da ita sai su sakar masa ita, ba tare da
fansa ba, in har taqi amincewa da cigaba da zama dashi, in kuwa ta
yarda da za ta ci gaba da zama da shi to ba za hukunta saki ba, kuma
igiyar auren tana nan a hannunsa, in kuwa ya so ya ci gaba da zama da
ita taqi amincewa to sai su yi hukunci da saki ba tare da biyansa
komai ba, kamar yadda muka ambata, kasancewar cutarwar daga
gareshi take.
Idan kuwa ya tabbata cewar laifin na matar ne kuma itace take
kawo savani, shi kuma yace yana son ta fanshi kanta, da abin da suka
ga ya dace da bangarorin biyu, ko kuwa za ta kai ga ta yi fansar kanta
da abin da ya qaru akan sadakinta ne. Idan kuwa ba ya son ta fanshi
kanta ya ga kuma cewa zai ci gaba da zama da ita a matsayin matarsa,
to sai su damqa masa amanar ta, su yi masa wasiyya da ya riqe ta da
alheri ya kuma yi hakuri da cutarwarta gareshi. A nan masu hukunchi
ba su da wata magana da ta wuce yin wasiyyar. Don haka da za su
raba tsakaninsu a dai-dai lokacin aka gano cewar cutarwar daga gareta
ne, shi kuma miji bai amince da ta fanshi kanta ba, ba za ayi la’akari
da rabawar masu hukunci ba, za ta kuma cigaba da kasancewa matar
aure. Kamar yadda hakan daliline mai qarfi cewa, su ko dai ba masu
ilimi bane ko kuma ba adalai ne ba. Wasu kuma suka ce za a zartar
da shi a kuma tilasta wa miji ya karvi fansa ta fuskar sauya
mummunan abu, domin kasancewarta tana savon Allah ne.
Idan kuwa suka kasa haqiqance komai, a ka cigaba da samun
matsala fa? An yi bayani mai tsawo akan hakan a manyan littatafai.
Idan kuwa suka gano cewa rashin kirkinsu ne su duka biyun ta yadda
kowannensu yana da laifi wajen cutar da xan uwansa, to saki ya zama
wajibi ba tare da fansa ba, wajen da yawa daga cikin malamai in har
bata yarda da cigaba da zama dashi ba kamar yadda waxansu manyan
malamai suka nuna da suka haxa da Addirdir da Assawi.
121
Ba shakka ginshiqin da aka xora al’amarin masu hukunci biyu
shine nassin Alqur’ani Allah Maxaukakin Sarki yana cewa: “Kuma idan kun ji tsoron savawar tsakaninsu, to ku aika da wani mai sulhu daga mutanensa da wani mai sulhu daga mutanenta. Idan sun yi nufin gyarawa, Allah zai daidaita tsakaninsu (ma’auratan). Lalle ne Allah ya kasance Masani Mai jarabawa” (Nisa’i: 85).
An samo cewa Qurtubi yana cewa: “wannan nassi ne daga Allah maxaukain Sarki cewa, su alqalai ne ba wakilai ba, ba kuma shedu ba. Bisa wannan in sun ga cewar za su raba tsakanin ma’aurata biyu to ya halalta su raba, za a kuma zartar da ita, haka nan ba banbanci ko hakan ya zo dai dai da hukuncin alkalin garin ko ya sava masa koda kuwa shine ya naxa su, kamar yadda ba banbanci ko ma’auratan biyu sun wakilta su su yi hakan ko ba su wakilta su ba, ko ma’auratan biyu sun amince a raba ko basu amince ba, koda kuwa sune suka naxa su, kasancewar su masu hukunci ne da nassin da ya gabata, da kuma abin da muka ruwaito a baya daga Ali da xan Abbas da Abu Salama da Sha’abi Allah ya yarda da su.
- Masu hukunci biyu na iya yin hukunci da sakin matar da aka
sadu da wacce ba a sadu da it aba.
- Idan masu hukunci biyu suka yi hukunci da raba aure za a zartar
da sakinsu ko da fansa ko ba fansa. Allah Maxaukakin Sarki
yace: “kuma idan kun ji tsoron savawar tsakaninsu, to ku aika da wani mai sulhu daga mutanensa da wani mai sulhu daga mutanenta. Idan sun yi nufin gyarawa, Allah zai daidaita tsakaninsu. Lalle ne Allah ya kasance Masani, Mai jarrabawa.” (Nisa’i: 35). Ina roqon Allah ya yi mana albarka ni daku cikin fahimtar
Alqur’ani mai girma, ya kuma amfane ni ya amfane ku da abin
dake cikinsa na ayoyi da anbato mai hikima. Tsira da amincin
Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad da
alayensa da sahabbansa. ina wannan magana tawa ina neman
gafarar Allah mai girma a gare ni da ku.
122
16
Hukuncin Cutar Da Mace Da yin Saki A sanadiyyar
Cutarwa
Huxuba ta Xaya
Godiya ta tabbata ga Allah kuma ina shedawa babu abin bautawa da
gaskiya sai Allah, kuma ina shedawa Shugabanm annabi Muhammadu
bawan Allah ne kuma manzonsa ne, ya isar da saqo, ya sauke nauyin
amana, ya yiwa al’umma nasiha ya yi jihadi wajen xaukaka addinin
Allah matuqar jihadi ya barmu akan hanya mai haske wacce hasken
darenta dai-dai yake da na ranarta, ba wanda zai kauce daga tafarkinta
sai hallakakke. Allah ya yi daxin tsira da albarka bisa alayensa da
sahabbansa da mabiyansa da wanda suka biyo su da kyautatawa har
zuwa ranar sakamako.
Bayan haka, kuji tsoron Allah ya ku bayin Allah! Ku kuma yi
masa biyayya, ku ji tsoron ranar da ba za a zalunci wata rai ba ko da
gwargwadon nauyin qwayar zarra ne. “kuma wani rai mai xaukar nauyi bai xaukar nauyin wani rai. Kuma idan ran da aka nauyayawa kaya yayi kira (ga wani mataimaki) zuwa ga kayansa, ba za a xauki komai ba daga gare shi, kuma ko da (wanda ake kiran) ya kasance makusancin zumunta ne” (Fatir: 18). “Ya ku mutane ku bi Ubangijinku da taqawa, wanda ya halicce ku daga rai guda, kuma ya halitta daga gare shi ma’auransa, kuma ya watsa daga garesu masu yawa maza da mata. Kuma kubi Allah da taqawa wanda kuke roqon juna da (sunan) Shi, da kuma zumunta lalle ne Allah ya kasance akanku Mai tsaro ne. (Nisa’i:1).
Ya ku bayin Allah! Haqiqa, cutar da mace na daga cikin
abubuwan da Allah ya haramta ga mazaje, manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi yace: “wanda ya fi kowa cikar imani shine wanda ya fi kowa kyawun halaye, kuma zavavvu daga
123
cikin ku sune zavavvu ga matayensu” Tirmizhi ya ruwaito. Kuma mai
tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace: “mafi alkhairin maza acikin al’ummata sune waxanda ba sa yin ta’addanci ga matansu, suke tausaya musu, kuma basa zaluntar su duk wanda yake da mata yaqi tufatar da ita da abin da zai suturce al’aurarta, kuma yaqi ciyar da ita da abin da za ta qoshi da shi, shugaba yana da haqqin ya raba su” daga Badruz zaujaini.
Ya ku mutane! haqiqa cutar da mace ya kan kasance kodai ta
hanyar cutar da jiki ko dukiya, idan ya kasance da jiki ko dai ya
kasance mai sauqi ko bayyananniyar cutarwa mai tsanani, hakan
kuma tana iya kasancewa mai maituwace ko ya kasance sau xaya,
haka nan mace tana iya sharxanta cewar ba zai cutar da ita ba, tun a
lokacin xaurin aure, kuma tana iya qin sharxanta hakan, kamar yadda
tana iya haxa sharaxin nata da rantsuwa ko ba ta barshi tare da
rantsuwa ba.
To ko yaushe ne ake yin saki a cikin waxannanal’amura?
Amsar wannan tambaya ita ce za ta bayyana mana sharuxan da suka
zama wajibi kafin a saki mace saboda cutarwa. Mafi girman ginshiqi a
cikin su shine mace ta nemi ayi sakin, domin tana da zavin cigaba da
zama da shi in ta ga dama, duk da cewa yana cutar da ita, in kuwa ta
kasance qaramace to za a yi aiki ne da maganar waliyyinta wajen
rabuwa ko cigaba da zama.
Abu na farko: idan miji ya cutar da dukiyar matarsa ba tare da
ta kasance tana da wani sharaxi akan hakan ba, to sai shugaba ya hana
shi yin hakan, ya kuma nemi ya biya kuxin da ya xauka, idan ya sake
maimaitawa bayan hana shi sai shugaba ya yi masa horo ba tare da
sakar masa ita ba. Idan kuwa cutar da dukiyar tata taci gaba da
faruwa, to nan ba za ayi aiki da maganar mace wawiya wacce aka
wakilta wani akanta ba, a maimakon haka za ayi aikine da maganar
waliyyinta. Savanin cutarwa ta jiki wacce ba za ayi aiki da maganar
waliyyinta ba sai dai idan ita ce ta wakilta shi.
Abu na biyu: cutarwa da shari’a ta xauka a matsayin cutarwa a
shari’ance itace cutarwar da mace take da haqqi in an yi mata ta nemi
saki, itace wacce ake yi ta hanyar aikata duk wani abu da miji zai yi
124
wanda bai halalta ya aikata shi a shari’ance ba, kamar ya qaurace mata
ba tare da wani dalili na shari’aba, ko da kuwa ta hanyar qin yi mata
magana ne, ko juya mata fuska a wurin kwanciya, ko zaginta, ko tsine
mata, ko zagin iyayenta, a misali yace da ita “yar karnuka” ko ‘yar tsinannu” ko ‘yar kafiri” a irin wannan yanayi ana iya sakar masa ita
gwargwadon ijtihadin alkali, kamar yadda za a ladabtar da shi a kuma
sakar masa ita, idan ya sadu da ita ta dubura. Kuma kafin a yi saki sai
an tabbatar da gaskiyar cutarwar.
Abu na uku: Hanyar tabbatar da cutarwa da aka yiwa xaya daga
cikin ma’aurata takan tabbata ne ta daya daga cikin abubuwa guda
biyu, ko dai ta hanyar samun hujja ko ta hanyar samun labari mai
yawa, wanda kuma ya fi kowanne daga cikin waxannan hanyoyi shine
ya tabbatar da bakinsa da cutarwa.
i- Hujja: ya zama wajibi kafin a karvi hujja sai ta cika
waxannan sharuxxan:
Shedar adalai guda biyu ko su wuce haka, haka nan tilas
ne su kasance maza biyu, shedar namiji xaya da mata
biyu ba zata wadatar ba, kamar yadda shedar mutum
xaya da rantsuwa ita ma ba za ta wadatar wajen adalci
ba.
Tilas ne su ganewa idanuwansu cutarwar, saboda
maqotakarsu da ma’aurata ko kusancinsu ko abin da ya
yi kama da haka.
Tilas ne shedun su yi sheda akan ya doketa ko ya cutar da
ita ba tare da wani lefin da zai tilasta hakan ba.
Tilas ne shedun su tabbatar da cewa ba su san cewa
wanda yake cutar da itan ya dena ya tuba ba, in kuwa ba
haka ba alkali ba zai yi aiki da shedarsu ba. Haka nan
idan mijin ya yi da’awar cewar ta amince ya sadu da ita
ta bayan ta nemi araba su, ita kuma ta gaskata shi to
haqqin ta ya faxi ba tare da banbancin kasancewarta
jahila ko mai ilimi ba, ko da kuwa ta yi da’awar jahilci ba
za a yi mata uzuri ba. Haka nan kevancewa tsakaninsu da
125
amincewarta bayan ta nemi saki yana da hukunci iri xaya
dana saduwa, kasancewar idan aka sami savani dangane
da saduwa ko rashin ta za a yi aiki ne da maganar wanda
yace an sadu.
ii- samun labari ta hanyoyi da yawa daga bakin maqota mata da
masu
hidima da sauransu cewa, lalle wane yana dukan matarsa
wance ko yana zaginta ba tare da haqqi ba ko yana barinta
da yunwa, ko juya mata baya a makwanci ko ba yayi mata
magana, ko ma ko wane irin abu daza a iya lissafawa a
matsayin cutar da ita. Hakanan shedar mutum biyu adalai
tana iya wadatarwa daga yaxuwar labari tsakanin mutane da
yawa da maqota da cutar da ake yi. To amma an fi son a
sami shedu masu yawa. wannan shine abin da ya fi shahara a
mazhaba kuma shine abin da ake aiki da shi kamar yadda ba
ya halalta ayi aiki da labarin mata wajen shedar cutarwa su
kaxai kasancewar saki yana daga cikin dangogin haddi, don
haka bai halalta a yi aiki da shedar mata su kaxai ba, ya
zama tilas labarin ya watsu a same shi a tsakaninsu da
waxansu da suka haxa da ‘yan aiki da makota.
Abu na huxu:
Cutarwa mai sauqi da wacce ta yi tsanani, Imam Malik Allah ya
yi masa rahama yace: “bamu sami wani abu sananne ba dangane da kasancewar cutarwa mai sauki ko mai tsanani ba” Wato kamar dai ya bar shi ga al’adar ma’aurata masu rikici da
juna duq abin da shugaba zai yi ijtihadinsa gwargwadon
al’adunsu, kuma a wannan ba a aiki al’adun garin alqali.
Abu na Biyar: shin tilasne cutarwa ta maimaitu?
Malamai sun banbance tsakanain cutarwa mai sauqi da cutarwa
mummuna ta sarari, sai suka haxu akan cewa mace na da ikon
neman saki idan miji ya cutar da ita mummunar cutarwa ko da
126
kuwa sau xaya ne, in har ta tabbatar da hakan da xaya daga
cikin hanyoyin tabbatarwa.
Idan kuwa cutarwar ta kasance mai sauqi ce, ba mummuna ba an
sharxanta cewa sai ta maimaitu. Haka nan sai an yawaita samun
qorafi wajen alkali tare da tabbatar da hakan a gabansa don ya yi masa
wa’azi ya ja masa kunnensa ya yi masa gargadi, to idan ya qi ji, ta
nemi saki sai a amsa mata.
Abu na shida: Yadda ake tabbatar da cutarwa a gaban shugaba:
duk macen da take qarqasih mijinta za ta kasance ne ko dai ta
sharxanta cewa ba zai cutar da ita ba, tun lokacin xaurin aure, misali
ta ce in har ya cutar da ita to al’amarin ta zai kasance a hannunta. ko
kuma ta kasance ba ta sharxanta hakan ba. To koma dai menene daga
cikin waxannan halaye guda biyu mace za ta nemi saki ne ta hanyar
xaukaka al’amrinta zuwa wajen shugaba. Ta kuma tabbatar masa da
cewar ana cutar da ita ta xaya daga cikin hanyoyin cutarwa da muka
ambata, kuma bata da ikon sakin kanta kafin ta kai al’amarinta zuwa
ga shugaba da ta tabbatar masa. Haka nan kuma sai ya nemi jin ta
bakin miji har dai ya tabbatar cewa ba shi da ragowar wani uzuri da za
a iya masa. Ana yin saki ne a lokacin da miji ya cutar da matarsa saki
xaya marar kome ba tare da banabancin cewar ba ita bace ta saki
kanta ko shugaba ne ya sake ta ba. Kamar yadda ba ta da iko sai na
saki xaya, ko da kuwa an yi saki ya wuce sau xaya. Malamai suka ce
mace tana da ‘yanci na tilasta mijinta ya sake ta saki xaya mara kome
a dalilin cutarwa da mijinta ya keyi mata.
Ya ku ‘yan uwa! Ku yi salati da sallama ga shugabanmu,
msoyinmu kuma mai ceton mu, annabi Muhammad kamar yadda
Allah ya yi muku Umurni da yi masa salati in da yace: “Lalle Allah da mala’ikunsa suna salati ga annabi, ya ku waxanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi” (Ahzab: 56). Ya Allah ka yi daxin tsira da aminci a gareshi da
alayensa da sahabbansa aminci mai yawa. Ina fadin wannan magana
ina neman gafarar Allah a gare ni da ku, da sauran musulmi maza da
mata daga kowanne zunubi, ku nemi gafararsa zai gafarta muku don
shi Mai yawan gafara ne Mai yawan rahama.
127
Huxuba Biyu
Godiya ta tabbata ga Allah wanda shine masanin abin da ke cikin
zukata da abubuwanda aka voye a cikin rai, ina gode masa, tsarki ya
tabbata gareshi, ina kuma gode masa a bisa abin da ya yi mana na
ni’imomi da falala mai tarin yawa, ina kuma shedawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah kuma ina shedawa annabi Muhammad
bawansane kuma manzonsa ne, wanda shine mai tsarki wanda aka
tsarkake, mai babban asali da tsarki tsira da amincin Allah da albarka
su tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa ma’abota falala da
abubuwan al’ajabi da mabiyansu da kyautatawa har zuwa ranar
sakamako.
Bayan haka, ya ku bayin Allah! Ku sani cewa tausayi ba yana
nufin tausayi ba tare da aiki da hankali ba, ko kuma jin qai ne da zai
savawa adalci da tsari ba, ko kaxan ba haka ba ne, tausayi wata
dabi’ace kawai dake kare haqqoqin baki xayansu. Don haka a duk
lokacin da aka samu savani tsakanain ma’aurata biyu ko xaya daga
cikinsu ya cutar da xaya, to ya zama tilas a xaukaka al’amarin zuwa
ga shugaba, saboda abin da Allah ya wajabta musu, Allah
Maxaukakin Sarki yana cewa: “Kuma in sun rabu Allah zai wadatar da kowanne daga yalwarsa, Kuma Allah ya kasance Mayalwaci Mai hikima [Nisa’i: 30]
Ina roqon Allah ya yi mana albarka, ni da ku baki xaya wajen
fahimtar Alqur’ani mai girma ya kuma amfane mu ni da ku da abin da
yake cikinsa na ayoyi da Ambato mai hikima, ya kuma karva mana ni
da ku domin shi mai ji ne kuma masani. Ku miqe zuwa sallah Allah
ya yi muku rahama.
128
17
Rabon Kwana Da Adalci Tsakanini Ma’aurata
Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa muna kuma neman
gafararsa, muna neman tsarin Allah daga sharrin kawunanmu, da
munanan ayyukanmu, duk wanda Allah ya shiryar babu mai vatar
dashi, wanda kuma ya vatar babu mai shiryar da shi. Kuma ina
shedawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shedawa
Shugabanmu Annabi Muhammadu bawan Allah ne kuma manzonsa
ne. Bayaban haka kuji tsoron Allah yaku bayin Allah, haqiqanin jin
tsoron Allah kukiyaye dokokin sa a sarari da boye Allah Maxaukakin
Sarki yana cewa: “Ya ku mutane ku bi Ubangijinku da taqawa, wanda ya halicce ku daga rai guda, kuma ya halitta daga gare shi ma’auransa, kuma ya watsa daga garesu masu yawa maza da mata. Kuma kubi Allah da taqawa wanda kuke roqon juna da (sunan) Shi, da kuma zumunta lalle ne Allah ya kasance akanku Mai tsaro ne. (Nisa’i:1)
Yana kuma cewa: “ku auri abin da ya yi muku daxi daga mata; biyu-biyu, da uku-uku da huxu-huxu, sannan idan kunji tsoron ba za ku yi adalci ba, to (ku auri) guda ko abin da hannayenku na dama suka mallaka….” (Nisa’i: 3) yana kuma cewa: “Kuma ba za ku iya yin adalci ba a tsakanin mata ko da kun yi kwaxayin yi. Saboda haka kada ku karkata, dukan karkata har ku barta kamar wadda aka rataye. Kuma idan kun yi sulhu, kuma kuka yi taqawa, to lalle ne Allah ya kasance Mai gafara, Mai jinqai.” (Nisa’i:129).
Haka kuma manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a
gareshi yace: “duk wanda yake da mata biyu a qarqashinsa sai ya karkata zuwa guda xaya daga cikinsu zai zo ranar tashin alqiyama, yana jan xaya daga cikin varin jikinsa a qasa ko a karkace” 1 ya ku
mutane! Haqiqa dukkan wanda ya auri mace biyu ya zamo tilas ya yi
1 Musnad Ahmad da sunan Ibn Majah
129
adalci tsakanin su, wannan abu ne da ya tabbata da nassin Alqur’ani
da sunna da haxuwar malamai. Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:
sannan idan kun ji tsoron ba za ku yi adalci ba, to (ku auri) guda ko abin da hannayenku na dama suka mallaka….” (Nisa’i: 3) yana kuma
cewa: “kuma ku yi zamantakewa da su da alheri…” (Nisa’i: 19)
Kamar yadda kuma manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace:
Duk wanda ya kasance a qarqashinsa akwai mace fiye da
xaya sai ya karkata ga xaya daga cikinsu zai zo ranar
tashin Alqiyama yana jan varin jikiinsa a kasa ko kuma a
karkace1
An kuma karvo daga Anas daga annabi tsira da amincin
Allah su tabbata a gareshi ya kasance yana da mata tara
ya kasance idan ya raba kwana tsakanainsu, baya
dawowa wajen ta farko har sai bayan kwana tara. Imam
Muslim ya ruwaito shi. Haka nan al’ummata ta haxu
gaba xayanta akan wajabcin adalci, don haka duk wanda
bai yi adalci tsakanin matansa ba ya savawa Allah
Maxaukakin Sarki, ya savawa manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi don haka limancinsa
ba ya inganta, haka ma shugabancinsa ko karvar
shedarsa. kuma duk wanda ya yi jayayya da wajabcinsa
za a nemi ya tuba tsawon kwanaki uku idan bai tuba ba,
to za a kashe shi don zama kafiri a lokacin da ake neman
tubansa. (Duba: kifayatu attalib arrabani juz’i na uku shafi na 135).
Ya ku bayin Allah! lalle vangaren da ya zama wajibi na raba dai-dai
shine rabon kwana banda sauran abubuwan da suka haxa da saduwa
da soyayya “kuma ba za ku iya yin adalci ba a tsakanin mata ko da
1Malaman hadisai biyar suka ruwaito shi.
130
kun yi kwaxayin yi. Saboda haka kada ku karkata, dukkan karkata har ku barta kamar wadda aka rataye. Kuma idan kun yi sulhu, kuma kuka yi taqawa, to lalle ne Allah ya kasance Mai gafara, Mai jinqai.”
(Nisa’i:129) malamai sun ce duk wanda ba zai shiga qarqashin iko ba,
to ba zai shiga qarqashin wajabci ba, kamar yadda adalci wajen
soyayya da qauna da saduwa wannan shine abin da manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yake roqon Allah kada ya
kama shi da laifi akansa inda yake cewa: “ya ubangiji wannan rabo na ne cikin abin da na mallaka, kada ka kama ni da laifin abin da kai kaxai ka mallakeshi ni ban mallake shi ba”1
adalci da aka yi Umurni
da shi wanda bawa zai yi wanda yake da iko akansa shine wanda ya
shafi rabon kwana, in har kuwa ba zai iya yin adalci a cikinsa ba ya
haramta gare shi ya auri mace fiye da xaya Allah Maxaukakin Sarki
yana cewa:
idan kun ji tsoron ba za ku yi adalci ba, to (ku auri) guda
ko abin da hannayenku na dama suka mallaka.. (Nisa’i:
3)
Don haka da ake kore musu adalci wani wuri aka kuma tabbatar da shi
a wani wuri, hakan ya nuna akwai adalci kala biyu, adalcin da aka
kore wanda ya shafi abubuwa waxanda mulkine na Allah Maxaukakin
Sarki. Shi kuwa adalci da aka yi Umurni da shi shine duk abin da xan
adam yake da iko akansa, kamar yadda karkata wacce ta halalta ta kan
kasance tsakanin mata wacce aka hana ita ce wacce miji zai karkata
gaba xaya.
Abin da ya zama wajibi shine daidaito tsakanin mata a wajen
kwana ya bar al’amarin saduwa ga xabi’a da bukatarsa, to amma duk
da haka bai kamata ya yi zalunci a cikinsa ta yadda zai taqaita shi ga
xaya daga cikinsu don ya yi tanadin wata saboda ya fi sha’awar wata
ba, ba shakka yin hakan cutarwa ne ga wacce take da wannan daren,
kuma yin hakan abune da aka yi hani akansa. kamar yadda mijin da
1 Al mustadrak ala sahih al hakim
131
ya zama wajibi akansa ya yi adalci wajen rabon kwana shine miji
wanda yake baligi, mai hankali, mazaunin gida ba matafiyi ba, kuma
babu banbanci tsakanin kasancewar sa ‘yantacce ko bawa, mai lafiya
ko mara lafiya, rashin lafiya da zai iya kewaye gidajen matansa. Matar
da za a yi mata rabon kwana kuma tana da sharuxa guda biyu:
Na farko: ya kasance ya sadu da ita, idan bai sadu da ita ba to ba ta da
haqqin kwana.
Na biyu: ta zama wacce za a iya saduwa da ita in har ta kasance
qaramace ba a iya saduwa da ita, ko da kuwa an sadu da ita, to amma
idan ya sadu da ita matar za a iya saduwa ita to ya zama tilas a raba
kwana da ita. haka ma kuma idan ba za a iya saduwa da ita ba, saboda
wani dalili na shari’a ko na al’ada ko na xabi’a to ya zama wajibi
araba kwana da ita, waxannan sun haxa da mai haila, da mai jinin
biqi ko wacce take aikin hajji ko Umra a lokacin, haka nan wacce
mijin ta ya yi rantsuwa ba zai sadu da ita ba, da wacce ya yi mata
zihari da mai larura a farji ta qari da mahaukaciya da kuturwa da mai
tsukakken farji, da mai qari da mai warin farji dukkan waxannan za a
raba kwana da su. Kamar yadda ba banbanci tsakanin mace musulma
da ma’abociyar littafi da ‘yantacciya, da baiwa, da mai lafiya da mara
lafiya, koda kuwa rashin lafiya na iya hana saduwa, rabon kwana
tsakanin dukkan waxannan da kuma mace musulma ‘yan tacciya mai
lafiya mai tsarki baliga wacce aka sadu da ita duk dai-dai suke da juna
wajen kwana, dangane kuwa da tsawon lokacin rabon shine dare da
yinin da ke biye da shi, saboda manzon Allah tsira da amincin Allah
su tabbata a gareshi ya kasance yanayin hakan. Kamar yadda yake
kuma abu ne da aka samo ta hanyar ruwayoyi mutawatirai daga
wurinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, haka nan rabon
kwana na wajibi shine na dare banda rana. Haka nan ana so a fara da
dare kasancewar shine lokacin kwanciya, matukar dai ba dawowa ya
yi daga tafiya ba, in kuwa hakane to an bashi zavi ya sauka wajen duk
wacce ya ga dama a lokacin da ya dawo. kamar yadda mijin bashi da
ikon ragewa akan dare xaya da yini, ko yayi qari sai da amincewarsu
kasancewar su sune suke da haqqi akan hakan, kuma duk abin da
suka amince da shi ya zama tilas miji ya yi aiki da shi. To amma fa
132
wannan idan matan nasa sauna gari xaya ne ko abin da za a iya yi
masa hukunci da gari xaya idan kuma suka kasance a garuruwa biyu
to ya halalta ayi rabon kowacce juma’a ko wata xai-xai, ko wata
biyu-biyu gwqargwadon abin da zai yiwu, ba tare da cutarwa ba,
kuma haramun ne miji ya shiga wajen kishiyarta a ranar kwanan ta sai
in da wata buqata; buqatar da ba ta jin daxi ba, ya halalta ya gaisa da
kishiyar ta da tambayar halin da take ciki a bakin kofa ba tare da ya
shiga ba, idan kwana ya wuce ta hanyar wucewar lokacinsa ba za’a
ramawa wacce darenta ya wuce ba, ba kuma za a sauya mata da wani
ba, duk a waxannan ba banbanci tsakanin wucewa ta hanyar uzuri ko
ba da uzuri ba, ko kuma ya zalunceta ta hanyar kwana a xakin
kishiyarta kwana biyu, ko kuma ya kwana ne a masallaci a ranar duk
ba za a ramaba. Akwai wasu abubuwa da bai halalta miji ya yi ba sai
da yardar matansa, miji ba shi da ikon qari a kwana xaya da yini ko ya
rage sai da yardarsu, kamar yadda ya gabata, haka nan ba zai zaunar
da su gida xaya ba wanda za su yi tarayya wajen kayan amfani da
suka haxa da wurin wanka da xakin girki da banxaki ba, sai sai da
amincewarsu. Duk wacce ta amince da zama da kishiyar ta a haka,
sannan daga baya ta nemi cin gashin kanta ba za a amsa mata ba, sai
dai idan wani abu ne ya faru da ya jawo hakan. idan kuwa ya zaunar
da matansa a gida xaya kowacce mace tana da xakin ta da xakin
girkinta da xakin wankanta, da ban xakinta na kanta yana da ikon
yin hakan, su kuma ba su da zavi akan hakan kasancewar ya cika
musu haqqinsu na cin gashin kai, kamar yadda miji yana da haqqin
kiransu wani gida nasa na musamman, kowacce a ranar kwananta in
sun yarda da hakan, in kuwa ba haka ba to ba shi da haqqin tilasta su,
amma abin da ya fi dacewa shine ya je gidan kowacce daga cikisu
ranar kwananta, saboda manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi haka yake aikatawa. Haka nan ana iya fifita wata
cikin mata matuqar xayar ta yarda da hakan, abin da ake nufi da
fififtawa shine ya fifita kishiyarta akan ta ta hanyar kwana a wurinta
koda yaushe, ko kuma ya yiwa wannaan kwana biyu ita kuma xaya ya
yi mata biyu, in ta yarda kamar yadda ya halalta ya sadu da kishiyarta
a ranar ta, in mai kwanan ta yarda, to amma bai halalta ya sadu da
133
xayarsu a gaban xayar ba, da ittifaqin malamai, ko da kuwa sun yarda
da haka, kamar yadda bai halalta ya kwanta shimfixa xaya tare da su
ba, ko da kuwa ba saduwa zai yi da suba koda kuwa sun yarda, kamar
yadda ba zai shiga da su xakin wanka tare ba koda kuwa sun yarda,
don dukkan waxannan wurare ne da ake zaton buxewar al’aura da
motsa kishi, kamar yadda ya savawa mutunci. Idan mace mai kwana
ta rufewa mijinta qofa, ta hana shi shiga kwanciya a wurinta ta hanyar
yin wani abu da ya hana hakan to za a xauke ta a matsayin mace
wacce ta fanxare don haka ya halalta ga mijin ya kwana a xakin
kishiyarta a wanna daren.
Haqqin kwana wajen mace amarya,
Yaku bayin Allah! Ku sani cewa duk wanda ya auri budurwa alhali
yana da waxansu matan ya zauna wurinta kwana bakwai, in kuwa
bazawarace ya aura zai zauna kwana uku daga nan kuma sai ya faro
lissafi tsakanain ta da kishiyoyinta, ko da sauran matansa ba kuma
dolene sai ya rama musu ba. Saboda faxin manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi yace: “budurwa tana da kwanaki bakwai bazawara kuwa kwana uku”1
a wata riwayar kuma yace: “in kina so in yi miki kwana bakwai in kuma kina so in yi miki kwana uku sannan in kewaya”2, sai manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata agareshi ya bayyana cewa kwana uku ba za a ramasu ga
bazawara ba.Wannan kuma ya samo asaline kasancewa mace Amarya
tana bukatar qarin xauke kewa da walwala don kunyarta ta ragu
duhun kanta ya yi sauqi wanda hakan na buqatar lokaci mai xan
tsawo kafin hakan ta faru, kamar yadda budurwa ta fi bazawara
buqatar hakan, sai aka qara mata kwanakin. Wannan kuma haqqin na
ita matar da ta shigo gida ta yadda ba shi da haqqin qyaleshi sai da
izininta, in kuwa bai yi ba zai rama mata saboda nassin da ya gabata
saboda abin da muka ambata na bukatarta da xauke kewa da cire mata
damuwa.
1 Muwaxxa Malik Takhrijin AbdulBaqi
2 Muwaxxa Malik Takhrijin AbdulBaqi
134
Ya ku bayin Allah! haqiqa aure xabi’ace da Allah Maxaukakin
Sarki ya sanyawa bayinsa hanyar abin da ya sanya musu na sha’awa,
don a samu zuri’a a tsakaninsu da wanzuwar jinsin xan adam, sannan
kuma sunnar Allah ce ta cika raya qasa da kare zuciya da tsare zuri’a
da gina rayuwar iyali da kuma sauke haqqoqin aure da sada zumunta
da taimakon juna da yiwa juna alkhairi da sauransu. Allah
Maxaukakin Sarki yan cewa:
ku auri abin da ya yi muku daxi daga mata; biyu-biyu, da
uk-uku da huxu-huxu,” (Nisa’i: 3) kuma manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace: “duk
wanda yake da wadatar yin aure bai yi aure ba, ba ya tare
dani” ku yi salati da sallama ga fiyayyen halittun Allah,
annabin rahama kamar yadda mahallicci ya yi mana
Umurni da haka a inda yake cewa: “Lalle Allah da
mala’ikunsa suna salati ga annabi, ya ku waxanda suka yi
imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin
amintarwa a gare shi (Ahzab: 56)
Ya Allah, ka yi daxin salati ga bawanka kuma manzonka, annabinmu
Muhammad da alayensa da sahabbansa.
135
Huxuba ta Biyu:
Godiya ta tabbata ga Allah shi kaxai, ina shedawa babu abin bautawa
da gaskiya sai Allah shi kaxai yake ba shi da abokin tarayya, ina
kuma shedawa shugabanmu Annabi Muhammad bawansane kuma
manzonsa ne, tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya yi
masa albarka da alayensa da sahabbansa.
Bayan haka:
Ya ku musulmai ku sani cewa, idan miji ya so yin tafiya to idan
a cikin matansa akwai wacce ba za ya iya yin tafiya da ita ba, aka
kuma samu cewa a cikinsu akwai wacce ta fi tausaya masa da bin
Umurninsa, to wannan zai ba shi uzurin ya yi tafiya da ita, ya kuma
zamo uzuri ga xayar na rashin tafiya da ita, idan kuma su ka yi dai-dai
da juna, sai a duba tafiyar idan ta aikin hajji ce ko yaqi to sai ya yi
quri’a a tsakanin su, ya tafi da wacce quri’arta ta fito, daga nan kuma
ba dole ba ne ya ramawa wacce bai yi tafiyar da ita ba kwanakinta ba
bayan dawowarsa, zai sake lissafin raba kwanaki ne kawai a
tsakaninsu.
Idan kuwa tafiyar ta kasuwanci ce an yo ruwayoyi guda biyu,
xaya ta ce za ayi quri’a, xayar kuma ta ce ba za a yi quri’a ba. Don
haka zavi ya rage gare shi. dalilin da ya sa muka ce zai yi quri’a a
tsakaninsu shine kasancewar annabi tsira da Amincin Allah su
tabbbata a gareshi yana yin quri’a ne.
Ya zo a hadisin da aka haxu akansa (Bukhari da Muslim) daga
Aisha Allah ya yarda da ita ta ce: “lalle annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kasance idan ya yi nufin zai yi tafiya sai ya yi quri’a tsakanin matansa, duk wacce quri’arta ta fito sai ya fita tare da ita” wannan kuwa ya samo asali ne kasancewar ba wacce a cikinsu ta
fi wata cancanta. Dalilin kuwa da ya sa aka kevance tafiya aikin hajji
da yaqi saboda kasancewarsu sun fi qarfi ta fuskar kasancewarsu duk
jinsin farilla ne, kuma manzon Allah tsira da amincin Allah su
tabbata gare shi bai yi quri’a a savaninsu ba, don haka ana yin ta ne
don koyi.
136
Lalle Allah yana yin umurni da adalci da kyautatawa
ma’abocin zumunta, kuma yana hani ga alfasha da abin
qi da rarrabe jama’ah, yana yi muka gargaxi tsammanin
ku kuna tunawa (Nahl: 90)
137
18
Kyautar Kwana Da Sayar Da Shi
Godiya ta tabbata ga Allah kuma ina shedawa babu abin bautawa da
gaskiya sai Allah, kuma ina shedawa Shugabanm annabi Muhammadu
bawan Allah ne kuma manzonsa ne, ya isar da saqo ya sauke, nauyin
amana, ya yiwa al’umma nasiha ya yi jihadi wajen xaukaka addinin
Allah matuqar jihadi ya barmu akan hanya mai haske wacce hasken
darenta dadai yake da na ranarta, ba wanda zai kauce daga tafarkinta
sai hallakakke. Allah ya yi daxin tsira da albarka bisa alayensa da
sahabbansa da mabiyansa da wanda suka biyo su da kyautatawa har
zuwa ranar sakamako.
Bayan haka, Ya ku mutane! ina yi muku wasiyya da ni kaina da
jin tsoron Allah ku ji tsoronsa. Allah ya yi muku rahama, ku kuma
kasance masu kyautatawa domin Allah Maxaukakin Sarki yana tare
da waxanda suke jin tsoronSa da waxanda su ke masu kyautatawa.
Ya ku mutane! Lalle tsaida adalci al’ada ce da duk wata
al’umma mai daraja ta gaje shi, ta ke kuma samar masa da kariya,
suke kuma gina tsare tsare don tabbatar da cewa ya tabbata ya kuma
kankama a jikinsu. Haka nan adalci abu ne da ya wajaba a yiwa
kowanne mutum na kusa da na nesa, mai qarfi da mai rauni,
mawadaci da matalauci, mazaunin gida da matafiyi, mata da ‘ya’ya
masu hidima da sauransu.
Kyan adalci da qaunarsa abubuwa ne da tun asali aka cusawa
zukata, don haka zukata suke jin daxi idan sun ga alamun adalci
matuqar dai son zuciya bai yi rinjaye ba. Saboda wani al’amari da ya
shafeta musamman ba.
Ya ku bayin Allah! Yana daga cikin adalcin miji ya sanya
kwanan matarsa daga gareta kamar yadda ya halalta ta bayar da
kyautarsa ga kishiyarta idan ta ga damar yin hakan.
138
Asalin inda aka samo wannan mas’ala shine hadisin A’isha
Allah ya yarda da ita. “Haqiqa Saudatu ‘yar Zam’atu ta bayar da kyautar kwananta ga A’isha Allah ya yarda da ita, don haka annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ke raba mata kwananta da na A’isha” Bukhari da Muslim suka ruwaito. Da kuma wani
hadisin na ta dangane da faxar Allah.
“ Babu laifi akansu su yi sulhu a tsakaninsu, kuma yin sulhune mafi alheri” (Nisa’i: 128) sai tace itace mace da take qarqashin
namiji, amma ba ta burgeshi sosai, sai ya yi nufin sakinta ya auri wata,
sai tace da shi ka cigaba da riqe ni kada ka sakeni, sannan ka auri wata
a maimakon haka na halalta maka ciyarwa da rabon kwana a gare ni,
shine faxin Allah maxaukakin sarki: “ ba bu laifi akansu su yi sulhu a tsakaninsu, kuma yin sulhune mafi alheri” (Nisa’i:128). A wata
ruwayar kuma ta ce: “shine namiji ya ga wani abu da ya hana matarsa ta burge shi da ya shafi tsufa ko waninsa, sai ya yi nufin rabuwa da ita, sai tace masa ka cigaba da riqeni ka raba ka bani duk abin da kaga dama, sai ta ce to ba laifi idan suka yi yarjejeniya akan hakan”. To ta
wannan fuskar za mu ga cewa mace da za ta yiwa mijinta kyautar
kwananta, ko ta yi wa kishiyarta, idan har kishiyar ta yi kyautar tilas
ne sai mijin ya karva. Haka nan yana iya mayar da kyautar ga wacce
ta yi kasancewar ta na iya yiwuwa yana da wata buqata gurin wacce ta
yi kyautar. kamar yadda wacce ta yi kyauta ba ta da ikon karve
kyautar tata matuqar mijin ya karva, in kuwa ta yi kyautar nan ga
mijin ba za ta kasance ta shi bace ta yadda zai ba wacce ya ga dama a
maimakon haka za a xauki kwanan nata ne kamar babu shi, don haka
sai kwanan ya koma ga wacce ta ke biye da ita, to idan sun kasance su
huxu ne to rabon kwanan zai zamo na uku ne, idan wacce ta yi
kyautar ita ce mai biyewa wacce yake xakinta sai ya kwana a xakin
wacce ke biye da ita haka nan za a ci gaba.
Haka nan mace wadda ta yi kyauta da kwananta na da ikon
janye kyautarta duk loqacin da ta so, ko dai a dalilin tsananin kishi ta
yadda ba za ta iya cika alqawarin ba. kamar yadda ba banbanci
tsakanin kyautar da aka iyakance da loqaci da wacce ba a iyakance ba.
Haka nan wacce ta bayar da kwananta tana iya janye sauran da suka
139
rage amma banda waxanda suka wuce. kamar yadda miji na iya sayen
kwanan mace daga wurinta ya musanya shi da wani abu da aka
ambata ya zamo rana xaya ko fiye da haka ko na dundundun, ya na
iya kevance wata daga cikin matansa da abin da ya saya, kamar yadda
kuma ya halalta kishiya ta sayi kwanan kishiyarta da ga wurinta ta
yadda za ta kevanta da abin da ta saya.
Kamar yadda ya halalta mace ta ba mijinta wani abu don ya ci
gaba da riqeta kada ya saketa ko da tana da kishiya ko ita kaxai ce.
kamar yadda wata ta daban wacce ba matarsa ba ta na iya bawa miji
wani abu don ya ci gaba da riqe matarsa kada ya rabu da ita. kuma
karvar da miji zai yi baya cikin cin dukiya ta hanyar varna, koda kuwa
ya so ne ya fifita wata a kanta sai ta qi amincewa sai ya bata zavi
kodai saki ko ta amince da fifitawar sai ta yi masa izini saboda haka
dangane da da wannan akwai maganganu guda biyu, to amma an
rinjiyar da halalci saboda qissar Saudatu ‘yar Zam’at Allah ya yarda
da ita.
Kamar yadda miji yana iya bawa mace wani abu don ta cigaba
da zama da shi kada ta nemi rabuwa da shi, ko saboda ta kyautata
zama da shi, kamar yadda ita ma za ta iya ba shi wani abu don ya
kyautata zama da ita.
Ya Allah ka yi daxin tsira da aminci da albarka ga bawanka
kuma manzonka annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa. Ya
Allah ka yarda da halifofi shiryayyu shugabanmu Abubakar da Umar
da Usman da Ali da sauran sahabbai ba ki xaya.
140
Huxuba ta Biyu
Godiya ta tabbata ga Allah shi kaxai, ina kuma shedawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah, ina kuma shedawa shugabanmu Annabi
Muhammad bawansane kumsa manzon ne. Allah ya yi xaxin tsira da
aminci da albarka a gareshi da alayensa da sahabbansa.
Ya ku bayin Allah! lalle akwai waxansu fitintinu a al’amarin
kishiyoyi, kishiyar mace ita ce matar mijinta. haqiqa an fitini mata ta
wanna fuskar da bala’i nau’i biyu, bala’in kishi “haqiqa Allah ya rubuta kishi ga mata” da kuma bala’in yi musu kishiya: “biyu-biyu da uku-uku da huxu-huxu. (Nisa’i: 3) don haka wacce aka jarabce ta da
kishi da kishiya sai ta yi haquri tana da ladan wanda ya yi shahada.
kasancewar idan ba ta yi haquri ba hakan na iya kai ta ga kafirci ko
ridda, sau da yawa akwai matan da suka kafirce a sarari ko dai sun
sani ko ba su sani ba, a loqacin da suka yiwa Allah katsalandan
saboda ya halalta yin kishiya, ko kuma ga manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi saboda ya auri mace fiye da xaya,
wannan shine halin da yawa daga cikin waxanda suka samu miji ya yi
musu kishiya. Dangane kuwa da wacce ba ta samu miji ba sai kaji
tana cewa da babu gara ba daxi, kuma da hanau qara mannau”
Kamar yadda waxanda su kai fito na fito da nassosin da suka
shar’anta auren mace fiye da xaya sun manta cewa wanda ya
shar’anta hakan shine wanda ya halicci maza da mata. Kamar yadda
suka halalta baxala da yin qawaye, don haka sai aka jarabcesu da
cututtuka wanda hakan zai qarfafi shari’ar auren mace fiye da xaya
wacce ta haramta baxala da fasiqanci.
Ya ku bayin Allah! Ku ji tsoron Allah a kawunanku, kuma ku
yi aiki da shari’ar Allah, hakanan ku yi qoqarin taimakon juna, da
fahimtar juna da soyayya su yi muku jagoranci don hakan shine halin
musulunci, kamar yadda ya zama wajibi musulmi su aikata shi. Ya
Allah ka xaukaki musulunci da musulmai ka kuma qasqantar da
kafirci da kafirai, ka rusa maqiya addininka kuma ka taimaki bayinka
masu kaxaita Allah.
141
Ya Allah ka amintar da mu a cikin qasashenmu, kuma ka gyara
mu mazanmu da matanmu da jagoranmu, ka gyara jagororin musulmi
baki xaya lalle kai mai iko ne bisa kome, ya Allah ka gafarta mana da
‘yan uwanmu da suka riga mu imani kuma kada ka sanya qunci a
zukatanmu ga waxanda suka yi imani, ya Allah lalle kai mai Tausayi
ne mai rahama. “Ya Allah ka bamu mai kyau a cikin duniya, ka bamu mai kyau a lahira, kuma ka tsare mana azabar wuta” (Baqara: 201)
“Lalle Allah Yana yin umurni da adalci da kyautatawa ma’abocin zumunta, kuma Yana hani ga alfasha da abin qi da rarrabe jama’ah, Yana yi muku gargaxi tsammanin ku kuna tunawa (Nahl:
90).
Ina roqon Allah ya yi mana albarka, ni da ku baki xaya wajen
fahimtar Alqur’ani mai girma ya kuma amfane mu ni da ku da abin da
yake cikinsa na ayoyi da Ambato mai hikima, ya kuma karva mana ni
da ku domin shi mai ji ne kuma masani. Ina roqon Allah ya gafarta
min, ya gafarta muku. lalle shi mai yawan gafara ne mai rahama.
142
19 Bin Iyaye
Huxuba ta Xaya
Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa muna yaba masa muna
neman gafararsa, muna neman taimakonsa, muna tuba a gareshi, muna
dogara da shi, muna kuma neman tsarin Allah daga sharrin
kawunanmu, da miyagun aiyukanmu, muna kuma shedawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah kuma Muhammad bawansa kuma
manzonsa, Allah ya yi daxin tsira a gare shi da alayensa da
sahabbansa har zuwa ranar sakamako.
Bayan haka:
Ya ku mutane! Ku ji tsoron Allah ga abin da ya wajabta muku na
haqqinsa da kuma haqqin bayinsa da yake kanku, kuma lalle mafi
girman haqqi da yake kanku shine haqqin iyaye da haqqin ‘yan uwa
makusanta domin kuwa Allah ya sanya kowanne haqqi a matakin da
ke biye da haqqinsa wanda yake haxe da na manzonsa. Allah
maxaukakin sarki yace:
Kuma ku bautawa Allah, kada ku haxa wani da shi, kuma
ga mahaifa ku yi kyautatawa, kuma ga ma’abocin
zumunta (Nisa’i: 36).
Allah maxaukakin sarki yace:
kuma mun yiwa mutum wasiyyar kyautatawa ga
uwayensa.”(Ankabut: 8). Kamar yadda ya bayyana
dalilin hakan don jan hankalin ‘ya’ya da kwaxaitar da su
su kula da wannan wasiyya da cewa : “uwarsa ta xauke
143
shi a cikin rauni akan wani rauni” (wato rauni akan wani
raunin da wahala wacce akan wata ta ciki da kuma
loqacin haihuwa), sannan renonsa da da xaukarsa da
shayar da shi kafin a yaye shi Allah maxaukakin sarki
yana cewa: “kuma yayensa a cikin shekaru biyu (muka ce
masa) “ka gode min da kuma mahaifanka biyu, makoma
zuwa gareni kawai take (Luqman: 14).
Kuma ba shakka manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a
gareshi ya gabatar da bin iyaye akan jihadi a cikin hanyar Allah.
Hadisi ya zo cikin Bukhari da Muslim daga Abdullah xan
Mas’ud Allah ya yarda da shi yace: “Na tambayi manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi cewa wanne aiki ne Allah ya fi so? Sai yace: “bin iyaye”sai nace sannan wanne? Sai yace: “jihadi a cikin hanyar Allah”
Ya zo kuma a cikin sahihu Muslim cewa, wani mutum ya zo
wajen manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace:
Ina yi maka mubaya‘a bisa hijira da jihadi ina neman
lada daga Allah sai yace: “shin iyayenka biyu akwai
wanda yake da rai? Sai yace: sai yace qwarai kuwa su
duka biyu suna da rai, sai yace: “kuma kana neman lada
gurin Allah? Sai yace: qwarai kuwa, sai yace: “koma
wajen iyayenka ka kyautata zama da su” haka nan a cikin
wani hadisi da isnadinsa mai kyau ne cewa yayi; wani
mutum yace: “ya ma’aikin Allah ni ina sha’awar jihadi
ne kuma na kasa yinsa, sai yace: “shin daga cikin
iyayenka akwai wanda ya yi saura? sai yace: mahaifiyata,
sai yace: “ka kiyaye haqqoqin Allah wajen kyautata mata
in kayi hakan to ka yi hajji, ka yi Umra, ka yi jihadi,”
Haka nan Allah ya yi wasiyya ga kyautatawa iyaye a duniya ko da
kuwa sun kasance kafirai ne, ko da kuwa suna Umurtar xansu wajen
tarayya da Allah wajen bauta sai dai ba zai yi musu biyayya ba wajen
144
yin kafirci ba. Allah yace: “kuma idan mahaifanka suka tsananta maka ka yi shirka game da addini, ga abin da baka da ilimi gareshi, to kada ka yi musu xa’a. Kuma ka mu’amalance su a cikin duniya gwargwadon shari’a, kuma ka bi hanyar wanda ya mayar da al’amari gareni” (Lukman: 51).
Haka nan ya zo a cikin sahihai biyu (Bukhari da Muslim), daga
Asma’u ‘yar Abubakar Allah ya yarda da su tace: “mahaifiyata ta zo wurina alhalin tana mushrika, wacce Abubakar ya sake tun a Jahiliyya sai ta zo wajen ‘yarta Asma’u a Madina bayan sulhun hudaibiyya. Sai Asma’u tace: sai na nemi fatawar manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi nace: mahaifiyata ta zo tana son in kyautata mata, shin ina iya kyautatawa mahaifiyata ya ma’aikin Allah? Sai yace: “qwarai kuwa ki kyautatawa mahaifiyarki”. Ya ku musulmai! kyautatawa iyaye yana kasancewa ta hanyar
yi musu abin kirki, da kyautata musu ta fuskar yi musu magana da aiki
da dukiya. Kyautata musu a magana shine ka yi musu magana da
tattausan harshe, da magana mai daxi, ta hanyar amfani da kalamai da
ke nuna girmamawa. kyautata musu ta hanyar aiki kuwa shine yi
musu hidima, da hannunka gwargwadon iko wajen biyan buqatunsu
da taimakonsu a cikin al’amuransu, da sauqaqa musu a cikin
al’amuransu, da yi musu biyayya a cikin duk wani abu da ba zai cutar
da kai a addininka ko duniyar ka ba, kada ka manta Allah yana sane
da duk wani abu da zai cutar da kai, in ka yi wani abu don kawai ka
sava musu bayan a haqiqanin gaskiya ba zai cutar da kai ba. kyautata
musu da dukiya kuma ya qunshi wadata su da dukiyar ka a duk
loqacin da suka buqaci hakan cikin daxin rai ba tare da kayi musu
gori ba ko ka cutar da su ba. A maimakon haka ka basu kana jin cewa
su ne suka yi maka alheri ta hanyar karvarsa da yin amfani da shi.
Kuma kamar yadda kyautatawa iyaye yake kasancewa a loqacin
da suke raye, haka nan yana kasancewa bayan rayuwarsu. Haqiqa
wani mutum daga Banu Salama ya zo wajen annabi tsira da amincin
Allah su tabbata a gareshi yace: ya manzon Allah shin akwai wani abu
na kyautatawa iyaye ne da yayi saura bayan rasuwarsu? Sai manzon
Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace: “qwarai kuwa,
145
yi musu addu’a, da nema musu gafara da zartar da wasiyyarsu, da sadar da zumuntar da ba za ta sadu ba sai da su, da girmama abokansu1
.
Allahu Akbar! Lalle kyautatawa iyaye abu ne mai girma, wanda
ya game komai, ciki har da girmama abokansu da sada zumunta da su
duk yana cikin kyautata musu.
Haka nan ya zo cikin Sahih Muslim daga Abdullah xan Umar
xan Khaxxab Allah ya yarda da su, cewa ya kasance ya bi wata
hanyar Makkah yana haye da jaki yana hutawa akansa idan ya gaji da
hawa taguwa, sai wani balaraben qauye yazo wucewa, sai yace: kai ne
wane xan wane? sai yace: qwarai kuwa, sai kawai ya ba shi jakin,
yace da shi “hau wannan” ya kuma ba shi wani rawani da ke kansa
yace da shi, “xaura akanka” sai suka ce da Abdullahi xan Umar xan
Khaxxab Allah ya yarda da su sai yace: “lalle wannan ya kasance abokin Umar kuma na ji manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yana cewa: “yana daga cikin kyautatawa iyaye mutum ya sadar da zumunta da masoyin babansa”2
Ya ku musulmai! Wannan shine bayanin matsayin kyautatawa
iyaye da girman martabarsu, sakamakonsa kuwa shine lada mai yawa
a lahira da sakamako kwatankwacinsa a nan duniya don ba shakka
duk wanda ya kyautatawa iyayensa, ‘yayansa’ za su kyautata masa.
haka nan yana daga cikin kyautatawa iyaye yaye musu baqin ciki
kamar yadda ya zo a cikin sahihai biyu (Bukhari da Muslim) daga
hadisin da Umar Allah ya yarda da shi a qissar mutum uku waxanda
kwana ya kama su a wani kogo sai suka shige, sai wani dutse ya toshe
qofar kogon da su suna ciki sai xayan su yace: “ya Allah haqiqa ya kasance ina da iyaye biyu tsofaffi sun manyanta kuma na kasance bana ciyar da wani kafinsu ko iyali ko dukiya, sai wata rana neman abin kiwo ya sa nayi nisa ban dawo wajensu ba har suka yi barci, a loqacin dana tatso musu abincinsu sai na same su sun yi barci, sai naci gaba da tsayuwa da qwarya a hannuna ina jiran farkawarsu har sai da
1 Sunan Ibn Majah
2 Musnad ashshihab al kada’I da Sunan Ibn Majah
146
alfijir ya keto sannan suka ta shi suka ci abincinsu, ya Allah idan nayi wannan ne don neman yardarka ka yaye mana abin da muke ciki na wannan dutse, sai dutsen ya buxa xan kaxan, sai suma abokansa su kayi tawassuli da kyawawan aiyukan su sai dutsen ya buxe gaba xaya, suka fito suna tafiya da qafafunsu” kuma haqiqa kyautatawa iyaye na
jawo yalwar arziki, da nisan kwana, da kyakkyawan qarshe. An karvo
daga Ali xan Abu Xalib Allah ya yarda da shi, lalle annnabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi yace: “duk wanda zai yi farin cikin Allah ya yi masa nisan kwana, ya yalwata masa arziqinsa, ya kuma kare shi daga mummunan qarshe to ya ji tsoron Allah, ya kuma sadar da zumunta”.1 haka nan kyautatawa iyaye shine qololuwar nau’in
sadar da zumunta domin sune waxanda suka fi kowa kusanci da kai ta
fuskar dangantaka.
1 Mussnad Ahmad da Sahih Albukhari
147
Huxuba ta biyu:
Godiya ta tabbata ga Allah shi kaxai, ina kuma shedawa babu abin
bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake ba shi da abokin tarayya,
ina kuma shedawa Annabi Muhammad bawansa ne kuma manzonsa
ne, tsira da amincin Allah da albarkarsa su tabbata a gareshi da
alayensa da sahabbansa.
Ya ku mutane!
Haqiqa ba ya dacewa da duk wani mai hankali da ya san falalar
kyautatawa iyaye da kyakkyawan sakamakonsa a duniya da lahira,
sannnan kuma ya yi watsi da shi ya qi tsayawa da shi, ko kuma ya
sava musu ya yanke zumuntarsa, haqiqa Allah maxaukakin sarki ya yi
hani da savawa iyaye a loqacin da kyautata musu ya fi kowanne
tsanani. Allah maxaukakin sarki yana cewa: “kuma Ubangijinka ya hukunta kada ku bautawa kowa face shi, kuma game da mahaifa biyu ku kyautata musu ko da xayansu ya kai ga tsufa a wurinka ko dukansu biyun, to kada kace musu tir, kuma kada ka tsawace su kuma ka faxa musu magana mai karamci. Kuma ka sassauta musu fukafukan tausayawa na rahama kuma kace Ubangiji ka yi musu rahama kamar yadda suka yi reno na ina qarami” (Isra’: 23-24)
A irin wannan yanayi na kaiwar iyaye matakin girma ake
samun rauni na jiki da na hankali, kamar yadda a waxansu lokuta ma
sukan kai mafi qasqancin shekaru wanada shine dalilin damuwa ko
kuma qosawa da su, to a irin wannan loqaci ne Allah ya yi hani da ya
nuna qosawarsa da iyayensa biyu, ya yi masa Umurnin ya yi musu
magana ta giramamawa, ya kuma qasqantar da kansa daga gare su ya
kuma shimfixa musu tausayi, ya yi musu magana irin ta wanda bai
xauki kansa a bakin komai ba a gabansu, ya yi musu mu’amala irin ta
mai hidima wanda ke qasqantar da kansa a gaban maigidansa, don
tausaya musu da kyautata musu, ya kuma roqa musu jin qai a wurin
148
Allah, kamar yadda su ka ji qansa a loqacin yana qarami a loqacin
yana cikin tsananin buqata suke rene shi.
Lalle ya zama wajibi akan mumini ya tsayu akan kyautatawa
iyayensa, kada kuma ya manta da kyautatawar da suka yi masa yana
qarami, baya iya amfanar kansa ko ya kare kansa daga cutarwa, ita
kuwa mahaifiyarsa ta hana idanunta barci don shi yayi barci, saboda
shi ta hana jikinta hutu saboda shi ya huta, shi kuwa mahaifinsa ya
karaxe ko ina ya rasa kwanciyar hankali, saboda tunanin yadda zai
samo musu abin da za su rayu da shi, ya kuma kula da shi don haka
kowannensu ya wajaba a gareshi ya kyautata musu sakamakon
aikinsu.
Ya zo a cikin Sahihai biyu (Bukhari da Muslim) daga Abu
Huraira cewa, wani mutum yace: “ya manzon Allah a cikin mutane waye ya fi cancanta in kyautatawa mu’amalata? Sai yace: mahaifiyarka, yace: sannan wa? Yace: “mahifiyarka”sai yace: sannan wa? Yace: “mahaifiyarka” yace: sannan wa? Yace: “mahaifinka”
Muna roqon Allah ya bamu dacewa da kyautatawa iyayenmu
mata da maza, ya kuma ba mu damar yin hakan don Allah da
kyakkyawan nufi da tsayuwa akan dai-dai, lalle shi mai yawan kyauta
ne kuma mai karamci.
Ina faxin wannan magana tawa ina neman gafarar Allah gare ni
da gare ku, ku nemi gafararsa don shi mai yawan gafara ne mai yawan
jinqai.
149
20
Aikin Mace Da Matsayinta A Musulunci
Huxuba ta Xaya
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu, kyakkyawan sakamako
na ga masu taqawa, kuma babu qiyayya sai ga azzalumai, kuma ina
shedawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah wanda shine
majivincin lamarin salihai, ina kuma shedawa shugabanmu Annabi
Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne, wanda shine cikamakin
annabawa shugaban mursalai, jagoran masu hasken goshi da qafafuwa
da alayensa da sahabbansa da waxanda suka biyo su da kyautatawa
har zuwa ranar sakamako.
“Ya ku waxanda suka yi imani! Kubi Allah da taqawa akan
haqqin binsa da taqawa kuma kada ku mutu face kuna masu
sallamawa’’ (A’li-imran: 102). “Ya ku mutane ku bi Ubangijinku da taqawa, wanda ya halicce ku daga rai guda, kuma ya halitta daga gare shi ma’auransa, kuma ya watsa daga garesu masu yawa maza da mata. Kuma kubi Allah da taqawa wanda kuke roqon juna da (sunan) Shi, da kuma zumunta lalle ne Allah ya kasance akanku Mai tsaro ne”.
(Nisa’i: 1) Allah maxaukakin sarki yana cewa: “Allah yana yi muku wasiyya a cikin ‘yayanku’, namiji yana da rabon mata biyu. Idan sun kasance mata ne fiye da biyu kuwa, to suna da biyu daga kashi uku xin abin da ya bari, kuma idan ta zamo guda ce (kawai), to tana da rabi. kuma iyayensa biyu ko wanne xaya daga cikinsu yana da kashi xaya daga cikin kashi shida xin abin da ya bari idan yana da xa (na miji), idan ko ba shi da xa kuma, iyayensa ne kawai zasu gajeshi to uwa tana da xaya daga cikin uku, sannan idan ‘yan’uwa sun kasance gare shi, to uwarsu tana da xaya daga cikin kashi shida bayan wasiyya wacce ya yi ko kuwa bashi. Ubanninku da ‘ya’yayenku ba ku
150
sani ba, waxannen su ne mafi kusantar amfani a gareku. hukunci ne daga Allah. lalle ne, Allah ya kasance masani ma haikima”
(Nisa’i:11)
Haqiqa Allah Maxaukakin Sarki ya saukar da sura guda a cikin
littafinsa wacce ya kira da surar mata,wacce ita ce sura ta uku a
manyan surori bayan fatiha, don haka za mu ga cewa an gabatar da
mace a farkon Alqur’ani mai girma, kamar yadda a duk Alqur’ani
babu surar da aka kira ta da sunan maza, ko sura da sunan annnabi
Adam amincin Allah ya tabbata a gareshi, sai dai a cikinsa akwai
suratul Maryam, da suratul Al’imran, da suratul Mujadalat, da suratul
Mumtahana, dukkan waxannan surori ne da manyan darussan da suke
koyarwa, shine mace da girman darajarta da xaukakar matsayinta da
kuma muhimmancin ta da musulunci ya ba ta. Ba shakka Allah
Maxaukakin Sarki ya ambaci mata a cikin suratul nisa’i, ya kuma rufe
ta da ambaton mata. aya ta farko tana cewa: “Ya ku mutane ku bi Ubangijinku da taqawa, wanda ya halicce ku daga rai guda, kuma ya halitta daga gare shi ma’auransa, kuma ya watsa daga garesu masu yawa maza da mata. Kuma kubi Allah da taqawa wanda kuke roqon juna da (sunan) Shi, da kuma zumunta lalle ne Allah ya kasance akanku Mai tsaro ne. (Nisa’i:1) ya kuma cika ayoyinta da ambatonsu
inda yake cewa: “kuma idan sun kasance ‘yan’uwa maza da mata, to namiji yana da misalin rabon mata biyu… (Nisa’i:176).
Sai aya ta farko ya tabbatar da asalin xan Adam guda xaya ne
maza da mata da: “ya ku mutane lalle babanku xaya ne dukka daga Adam kuke, adam kuwa an halicceshi daga qasa” Bazzar ya ruwaito
kamar yadda ya zo a cikin aljami Assagir. Aya ta qarshe kuma, sai
ya ambaci haqqinta na mallaka da kasonta na gado da ta riqe kuxi ta
ci gashin kanta. A suratul Mujadala kuma ya tabbatar da haqqinta ne
na kai qara idan tana da qorafi da kuma wajabcin sauraron qarar tata
idan ta kai qara, Allah maxaukakin sarki yace: “lalle Allah ya ji maganar wadda ke yi maka jayayya game da mijinta, tana kai qara ga Allah” (Mujadalah: 1). Wannan mata kuwa itace Khaulatu ‘yar
Sa’alabatu, wata rana Umar xan Khaxxab Allah ya yarda da shi ya
zo wucewa yana haye da jaki, mutane suna tare da shi, sai ta tsayar da
151
shi loqaci mai tsawo ta yi masa wa’azi tace: “ya Umar a da ka kasance ana kiranka Umair, sannan aka kira ka da Umar ,sannan aka kira ka da Amirul Muminin, ka ji tsoron Allah ya kai Umar, duk wanda ya tabbata zai mutu ba shakka zai ji tsoron gafala, duk wanda ya sakankance da hisabi zai ji tsoron azaba”, shi kuwa sai ya yi tsaye
kawai yana sauraran maganarta.
Sai aka ce masa: ya Shugaban Muminai me ya sa ka tsayawa
wannan tsohuwa na tsawon loqaci haka? Sai yace: “wallahi da za ta tsare ni tun daga farkon safiya har zuwa qarshen yammaci ba zan gushe ba in ban da lokutan sallolin farilla, ko kun san wannan wacce tsohuwa ce? Ita ce Khaulatu ‘yar Sa’alabatu wacce Allah ya ji maganar ta daga saman bakwai, shin kuna ganin cewa ubangijin halittu zai ji maganarta, Umar kuma yaqi ji, (Tafsirin Tabari 17: 269)
A nan sai musulunci ya tabbatar mata da haqqin kai qara da
neman haqqinta, a duk loqacin da ta ga dama, ga duk wanda ta ga
dama. Kamar yadda aka tabbatar a littafin (al-qada’a) da (adda’awa).
Allah kuma ya rusa al’adar nan ta zihari ta jahiliyya da li’aninta a
dalilin kawo qararta da kai komo wurin manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi. wanda ada su zihari da li’ani duk
su a wrinsu saki ne, don haka sai aka sanyawa zihari kaffara kamar
yadda aka yi bayani a fasalin zihari, wanda da zarar ya yi kaffara to ta
koma matarsa kamar yadda take a baya.
A cikin suratul Muntahana kuma an daidaita tsakanin maza da
mata ta fuskar amincewa da mubaya’arsu bisa musulunci, aka kuma
tabbatarwa da mace haqqin hijira daga qasar abokan gaba a loqacin
da ta musulunta da rabuwa da mijinta kafiri wanda bai musulunta ba.
Ya ku bayin Allah! An saukar da sura ta musamman aka kira ta da
suna suratut Xalaq wanda a cikin ta aka yi bayanin saki filla-filla da
hukunce-hukuncen idda don kare martabarta da kyakkyawan sunanta,
da martabar tsatsonta, da zuriyarta. Don Allah ku dubi yadda
musulunci ya kula da mace ya kuma ba ta muhimmanci. ku duba
yawan abubuwan da ya shar’anta mata, da yawan ayoyin da aka
saukar, da yadda ake ta anbatonta a Alqur’ani aka kuma kira surori da
sunanta a Alqur’ani, da kuma yawan wasiyyoyin da aka yi don a
152
kyautata mata don a kare matsayinta, aka wajabta girmama ta da kare
haqqoqinta, a matsayinta na uwa da ‘ya da matar aure, da ‘yar uwa
muharrama da wacce ba muharrama ba. To amma duk da haka sai ka
ga waxansu mata na jayayya da wannan addini mai girma. Haka nan
bai dai-daita tsakaninta da maza ababen tausayi ba. Allah Maxaukakin
Sarki yana cewa annabi Adam amincin Allah ya tabbata a gare shi
yana yi masa gargaxi da Iblis, la’anar Allah ta tabbata a gareshi.
“Sai muka ce, ya Adamu! Lalle ne wannan maqiya ne
gareka da kuma ga matarka, saboda haka ya fitar da ku
daga aljannah ka wahala” (Taha: 117).
Sai ya kevance shi da wahala, ban da ita bai ce ku wahala ba, to amma
wai duk da haka sai kaji mata wai tana burin kasancewa kamar namiji.
Ya ku bayin Allah! Ba shakka mace bata son saki bata qaunar saki,
tana kuma tsanar saki musamman ma idan kansu ya haxu da mijinta.
Haka nan Allah Maxaukakin Sarki ba ya son saki, annabi tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi yana yin fushi da saki, haka nan
mala’iku suna yin fushi da saki domin ko duk abin da Allah yake
fushi da shi, mala’iku ma suna fushi da shi. Domin Allah yana cewa
ga wanda yake so: “lalle ne ni ina son wane kuma ku soshi” haka nan
zai ce dangane da wanda yake qi “lalle ne ni ina fushi da wane kuma ku yi fushi da shi” Ahmad ya ruwaito shi.
Iblis kuwa la’anar Allah ta tabbata a gare shi, yana son saki,
yana qaunar ayi saki, haka nan yana bayar da sakamako idan an yi
saki, haka nan duk shaixan na mutane da na aljanu suna son saki,
musamman ma idan ya kasance tsakanin ma’aurata ne masu kirki
masu qaunar juna da son addini.
Ya ku ‘yan’uwa na a imani! Don Allah ku dubi abin mamaki
wai duk da waxannan abubuwa da ake faxawa mumini amma sai kaga
yayi saki, musamman ma a loqacin da za’a iya dai-daitawa, akwai
sauran qauna da soyayya komai qanqantarta, haqiqa manzon Allah
tsira da amincin Allah su tabbata gare shi yana cewa:
153
Lalle kada mumini ya musgunawa mumina, in yaqi wani
hali nata zai amince da wani. Ahmad ya ruwaito.
Don haka idan zamantakewa ta qi daxi so da qauna suka yanke aka
rasa yadda za a yi a dai-daita tsakanin miji da matarsa, kuma mace
taga cewa tana son ta wayi gari ita ce zata rinqa saka maimakon a
saketa, ta rabu da miji maimakon ya rabu da ita don tana ganin cewa
sakinta qasqanci da wulaqanci ne, kuma saki abu ne mai arha qaddara
ce da bata da qima, tana son ta wayi gari ta ce masa na sakeka, da abin
da zai biyo bayan hakan shine nadama,ba shakka da wuya ka samu an
yi saki kuma kowa yana farin ciki sai dai a manyan laifuka da
munanan halaye da mugwayen xabi’u, a loqacin da ba ta yadda
za ayi a sami haxin kan juna, wanda saboda irin wannan yanayi ne aka
shar’anta saki.
Ya ku bayin Allah! A duk loqacin da saki ya auku sai nadama
ta biyo bayansa, miji ya wayi gari yana faxa a cikin ransa ina ma da
ace mahaifiyarsa ba ta haife shi ba, ita kuwa mace ta rinqa cewa: “in
da na mutu kafin wannan loqaci da tuni an mance da ni”. Wannan
yana faruwa ne kasancewar matuqar saki ya auku to ba za a iya janye
shi ba, kamar yadda idan ya kai uku ko da wanda ba kome ne to ba
yadda za a yi. Don Allah ku yi nazari ku gani cewa rantsuwa ana iya
yi mata kaffara ta hanyar ciyar da miskinai goma, shi kuwa saki ba shi
da wata kaffara sai rabuwa. “Kuma lalle ne Allah bai zama mai zalunci ga bayinsa ba” (Al-imran: 182). Haka nan a loqacin da akai
saki suka yi nadama baki xayansu tana iya yiwuwa su haxu a voye ko
su qirqiri wata kalma ta qarya ya faxawa alqali, da zaton cewa zasu
iya voyewa masanin fili da voye; ko kaxan, “lalle shi yana da sanin asirin da abin da ya fi voyuwa” (Xaha: 7).
Lalle Allah da mala’ikunsa suna salati ga annabi. Ya ku
waxanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku
yi sallama domin amintarwa a gare shi. (Ahzab: 56)
154
Huxuba ta biyu
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya halicci namiji da mace, wanda
yake shine mai fararwa da dawowa, wanda yake da tsananin kamu,
wanda shi yake aikata abin da yayi nufi, ina yaba masa, ina gode
masa, don ta hanyar gode masa ne ni’ima take dawwama. kuma ina
shedawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kaxai yake, ba
shi da abokin tarayya, kuma ina shedawa shugabanmu Annabi
Muhammad bawansa ne kuma manzonsa ne, Allah ya yi daxin tsira da
aminci a gareshi da alayensa da sahabbansa.
Bayan haka, Ya ku ‘yan’uwa! Ku ji tsoron Allah zai gyara
muku aiyukanku ya kuma gafarta muku zunubanku, duk wanda ya yi
xa’a ga Allah da manzonsa haqiqa ya rabauta rabo mai girma. Allah
maxaukakin sarki yace:
Maza masu tsayuwa ne akan mata saboda abin da Allah
ya fifita sashensu da shi akan sashe, kuma saboda abin
da suka ciyar daga dukiyoyinsu. To salihan mata masu
xa’a ne, masu tsarewa ga gaibi saboda abin da Allah ya
tsare. (Nisa’i: 24).
Ya ku bayin Allah! Wai ko menene ya ke sa mace take son ta kasance
itace a sama? Bayan kuma Allah Maxaukakin Sarki ya halicci namiji
sama da mace? Ya sanya mace qarqashin namiji? domin kuwa har
larabawa su kan ce wance a qarqashin wane take wato matarsa ce,
Allah Maxaukakin Sarki yana cewa: “Allah ya buga wani misali domin waxanda suka kafirta matar Nuhu da matar Luxu, sun kasance a qarqashin wasu bayi biyu daga bayinmu salihai sai suka yaudaresu, saboda haka ba su wadatar musu da komai ba daga Allah ba” (Tahrim:
10). Ba shakka Allah ya sanya namiji sama da mace da dukkan
abubuwan da za su ba shi dama ya tsayu da aikinsa wanda Allah ya
halicce shi dominsa, kamar yadda ya sanya mace ta banbanta da shi da
kowanne abu da zai bata dama ta yi aikin da aka halicce ta dominsa.
155
Don haka sai ya sanya namiji sama da ita da darajoji “kuma maza suna da wata daraja a kansu” (Baqara: 228) haka nan da fifiko, “ maza masu tsayuwa ne a kan mata, saboda abin da Allah ya fifita sashensu akan sashe” da kuma ciyarwa “ saboda abin da suka ciyar daga dukiyoyinsu”(Nisa’i: 34), haka nan a wurin sheda: “to idan basu zamo maza biyu ba, to namiji guda da mata biyu daga waxanda kuka yarda da su daga shedu”(Baqara: 282). Haka nan ta fuskar addini, “suna yin tasbihi a gareshi a cikinsu, safe da maraice waxansu maza” (Nur: 36-
37).
Ku saurara! Ku yi salati da sallama ga rahama mai shiryarwa da
ni’ima mai yawa, annabinmu Muhammad manzon Allah tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi, lalle Allah yana yi muku Umurni
da haka yace:
“Lalle Allah da mala’ikunsa suna salati ga annabi, ya ku
waxanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku
yi sallama domin amintarwa a gare shi. (Ahzab: 56)
Allah ya yi daxin tsira da aminci a gareshi da alayensa da
sahabbansa.
Ya Allah ka yarda da halifofinsa shiryayyu, Abubakar, da Umar, da
Usman da Ali da sauran sahabbai da tabi’ai da waxanda suka biyo su
da kyautatawa har zuwa ranar sakamako. ka haxa mu da su da
afuwarka da kyautatawarka ya mafi karamcin masu karamci.
Lalle Allah yana yin umurni da adalci da kyautatawa
ma’abocin zumunta, kuma yana hani ga alfasha da abin
qi da rarrabe jama’ah, yana yi muku gargaxi tsammanin
ku kuna tunawa (Nahl: 90).
Ku miqe domin yin sallah, – Allah ya yi muku rahama.