a nijeriya - international committee of the red cross nan icrc tana taimakawa wajen horas da sojoji...

BUNKASA DOKOKIN KASA DA KASA NA KULA DA Y’AN GUDUN HIJIRA DA TABBATAR DA KAIDOJIN AIWATAR DA DOKOKIN KASA DA KASA KULAWA DA HALIN RAYUWAR DA MUTANEN DA AKE TSARE DA SU SUKE CIKI Dalilin dokar IHL shine ta kare jama’a daga shiga wahalhalu a lokacin rikice-rikicen da ake amfani da makamai. A matsayinta na mai kare wadannan dokokin yaki na kasa da kasa, ICRC tana taimaka samar da kwararru a fanin shari’a domin tallafawa mahukunta Nijeriya wajen sanya hannu da aiwatar da kudurin dokar IHL. Haka nan ICRC tana taimakawa wajen horas da sojoji da malaman jami’oi da ke sashin koyar da shari’a da dalibansu a fanin dokokin IHL. Tare da hadin gwuiwar kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma watau ECOWAS, kungiyar ICRC tana bunkasa dokokin IHL a yankin Afrika taYamma. Jami’an rundunar y’an sandan Nijeriya suna samun horo a fanin bada taimakon agaji da ka`idojin aiwatar da dokokin kasa da kasa. Tare da amincewar mahukuntan Nijeriya, wakilan kungiyar ICRC sukan kai ziyara zuwa ga mutanen da ake tsare da su domin bincika ko yanayin zamansu da kulawar da ake da su ya kai mizanin na kasa da kasa. Ana tattauna abubuwan da suka binciko a asirce tare da hukumomin da suka dace na Nijeriya, kuma ba’a bayyana wadanan bayanai ga wani mutum na daban ko a bayyana shi ga jama’a. Idan akwai bukata, bayan tattaunawa da hukumomin da suka dace, kungiyar ICRC takan inganta yanayin gidajen yarin, ko kuma ta inganta hanyar samar masu da ruwan sha mai tsafta. ATAKAICE Boris Heger/ICRC Maria Olu-Egbuniwe/ICRC ICRC Abuja 29, Kumasi Crescent, Off Aminu Kano Crescent P.M.B 7654, Wuse II T: +234 9 461 96 11/2/3/4 [email protected] ICRC Jos 1 Rest House Road Off D.B Zang Road, GRA Jos T: +234 813 353 6501 jos_ [email protected] ICRC Kano 4 Mayango Road GRA Kano T: +234 64 91 27 33 [email protected] ICRC Maiduguri 7 Bifam rd, Off Circular Road (Damboa junct.) GRA, Maiduguri, T: +234 8107139438 [email protected] ICRC Port Harcourt 46b Orogbum Crescent T: +234 84 46 02 70/1 [email protected] Visit our website at: www.icrc.org © ICRC, June 2013 2013 0105/600 06.2013 5000 a Nijeriya ICRC tana ayyukan agaji a Nigeria tun daga 1988, kuma ta aiwatar da ayyukan a lokacin yakin basasan Nigeria. Cover photo: Cécile Massie/ICRC ICRC/2013 ICRC IN NIGERIA

Upload: lyliem

Post on 11-Apr-2018

219 views

Category:

Documents


5 download

TRANSCRIPT

Page 1: a Nijeriya - International Committee of the Red Cross nan ICRC tana taimakawa wajen horas da sojoji da malaman jami’oi da ke sashin koyar da shari’a da dalibansu a fanin dokokin

BUNKASA DOKOKIN KASA DA KASA NA KULA DA Y’AN GUDUN HIJIRA DA TABBATAR DA KAIDOJIN AIWATAR DA DOKOKIN KASA DA KASA

KULAWA DA HALIN RAYUWAR DA MUTANEN DA AKE TSARE DA SU SUKE CIKI

Dalilin dokar IHL shine ta kare jama’a daga shiga wahalhalu a lokacin rikice-rikicen da ake amfani da makamai. A matsayinta na mai kare wadannan dokokin yaki na kasa da kasa, ICRC tana taimaka samar da kwararru a fanin shari’a domin tallafawa mahukunta Nijeriya wajen sanya hannu da aiwatar da kudurin dokar IHL. Haka nan ICRC tana taimakawa wajen horas da sojoji da malaman jami’oi da ke sashin koyar da shari’a da dalibansu a fanin dokokin IHL.

Tare da hadin gwuiwar kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma watau ECOWAS, kungiyar ICRC tana bunkasa dokokin IHL a yankin Afrika taYamma. Jami’an rundunar y’an sandan Nijeriya suna samun horo a fanin bada taimakon agaji da ka`idojin aiwatar da dokokin kasa da kasa.

Tare da amincewar mahukuntan Nijeriya, wakilan kungiyar ICRC sukan kai ziyara zuwa ga mutanen da ake tsare da su domin bincika ko yanayin zamansu da kulawar da ake da su ya kai mizanin na kasa da kasa. Ana tattauna abubuwan da suka binciko a asirce tare da hukumomin da suka dace na Nijeriya, kuma ba’a bayyana wadanan bayanai ga wani mutum na daban ko a bayyana shi ga jama’a.

Idan akwai bukata, bayan tattaunawa da hukumomin da suka dace, kungiyar ICRC takan inganta yanayin gidajen yarin, ko kuma ta inganta hanyar samar masu da ruwan sha mai tsafta.

A T A K A I C E

Boris

Heg

er/I

CRC

Mar

ia O

lu-E

gbun

iwe/

ICRC

ICRC Abuja29, Kumasi Crescent, Off Aminu Kano CrescentP.M.B 7654, Wuse IIT: +234 9 461 96 11/2/3/4 [email protected]

ICRC Jos 1 Rest House Road Off D.B Zang Road, GRA JosT: +234 813 353 6501jos_ [email protected]

ICRC Kano 4 Mayango Road GRA KanoT: +234 64 91 27 [email protected]

ICRC Maiduguri 7 Bifam rd, Off Circular Road (Damboa junct.)GRA, Maiduguri, T: +234 8107139438 [email protected]

ICRC Port Harcourt 46b Orogbum Crescent T: +234 84 46 02 70/1 [email protected]

Visit our website at: www.icrc.org

© ICRC, June 2013

201

3 01

05/6

00 0

6.20

13 5

000

a Nijeriya

ICRC tana ayyukan agaji a Nigeria tun daga 1988, kuma ta aiwatar da ayyukan a lokacin yakin basasan Nigeria.

Cover photo: Cécile Massie/ICRC

ICRC/2013

ICRC IN NIGERIA

Page 2: a Nijeriya - International Committee of the Red Cross nan ICRC tana taimakawa wajen horas da sojoji da malaman jami’oi da ke sashin koyar da shari’a da dalibansu a fanin dokokin

TALLAFAWA CIBIYOYIN KULA DA LAFIYA WADANDA KE KARBAR MUTANEN DA SUKA JI RAUNI SANADIYYAR RIGINGIMUN DA AKA YI

KAI DAUKI GA SAKAMAKON TASHE-TASHEN HANKULA

INGANTA HANYAR SAMUN TSAFTATACCEN RUWAN SHA

AIKI TARE DA KUNGIYAR AGAJI TA RED CROSS TA KASA WATAU (NRCS)

Tare da hadin gwuiwar ma’aikatar lafiya, kungiyar agaji ta ICRC tana inganta kwarewar ma’aikatan kula da lafiya wadanda ke aikin dawainiyar kulawa da mutanen da suka samu raunuka a lokacin tashe-tashen hankula ta hanyar shirya masu kwasa-kwasai na horas da su a wasu zababbun asibitoci.

Idan ya zama tilas, kungiyar agaji ta ICRC ta kan tura cikakkiyar tawagar ma’aikatanta masu tiyata tare da kayan bada agaji da na tiyata wadanda akan aika da su zuwa ga asibitocin da aka kai marasa lafiya a sanadiyyar tashin bama- bamai ko wasu rigingimu na kabilanci.

Kungiyar agaji ta ICRC tana taimakawa wadanda suka bar gidajensu a sanadiyyar fadace- fadace na kabilanci da sauran rigingimu, takan aika masu da kayan kwanciya, sutura da abinci. Domin taimaka masu jure halin da suka samu kansu da ya rabasu da gidajensu ba shiri.

Hakan nan takan taimaka masu da tukwanen dafa abinci, gidan sauro da kayan kwanciya, kayan girki da kuma fannin tsafta. Ana bada taimakon wadannan kayayyaki ne ta hanyar hadin guiwa da kungiyar agaji ta Red Cross ta Nijeriya (NRCS).

Domin inganta matsayin kula da lafiya a yankunan da ake yawan samun hargitsi, ICRC ta kan aiwatar da ayyukan gyarawa ko tona sabin rijiyoyi da samar da ingantattun ruwan sha, musamman a cibiyoyin kula da lafiya da ke irin wadannan wuraren. Tare da hadin guiwar kungiyar agaji ta Red Cross ta Nijeriya ana samar da ruwan sha cikin gaggawa ga mutanen da suka rasa muhallansu.

Domin tabbatar da cewa ruwan shan yana da ingancin da aka amince da shi, ana tsaftacewa tare da kare wuraren samun ruwan sha a makarantu da na cibiyoyin alum’ ma inda mutanen da suka rasa muhallansu suka samu mafaka.

Kungiyoyin agaji na ICRC da NRCS suna aiki tare wajen bada taimakon agaji ga wadanda tashe-tashen hankula ya rutsa da su, tare da kokari wajen sada iyalan da suka rabu da yan uwansu sakamakon tashin hankali ko fadace -fadace.

Ta hanyar tallafawar kungiyar ICRC, ma’aikatan sa kai na kungiyar Red Cross ta kasa watau NRCS sukan bada taimakon agaji na matakin farko a yanayi na gaggawa, ta hanyar gaggauta kai wadanda suka ji rauni asibitoci da kulawa da gawarwakin wadanda suka rasu, ta yadda za’a aika da bayanai na wadanda suka rasu zuwa ga ‘yan uwansu. Akan kuma bada horaswa kan bada taimakon agaji a kauyukan da basu da ma’aikatan kula da lafiya. ICRC kuma ta kan tallafawa NRCS a sha’anin watsa bayananta watau sadarwa.

Susa

nne

Serr

y/IC

RC

Céci

le M

assi

e/IC

RC

M

iche

le U

ngar

o/IC

RC

Céci

le M

assi

e/IC

RC