hukumar dake kula da lambar shaidar zama ‘dan kasa · cad na’urar amfani da kati cidr cibiyar...

16

Upload: lyhanh

Post on 03-Mar-2019

214 views

Category:

Documents


0 download

TRANSCRIPT

2

HUKUMAR DAKE KULA DA LAMBAR SHAIDAR ZAMA ‘DAN KASA An kirkiri wannan hukumar ce a karkashin kundin tsarin doka na 23 ta shekara 2007

TSARIN SAMAR DA KATIN SHAIDAR ZAMA ‘DAN KASA Yadda za’a aiwatar da shirin, da kuma yadda shirin zai amfani jama’a da kuma

gwamnati

3

An wallafa wannan littafi ne:

A sashen nazari da tsare tsare da kuma hul’da da jama’a na Hukumar dake kula da kuma samar da lambar shaidar zama ‘dan kasa (NIMC)

dake lamba 11 Sokode Crescent, Daura da Titin Dalaba, Wuse Zone 5.

P.M.B 18, Garki, Abuja, Najeriya. Adireshin yanar gizo: www.nimc.gov.ng

Email: [email protected]

ABUBUWAN DAKE CIKI:

4

Takaitattun sunaye……………….....……………………………………………………....….2 Bayani akan hukumar kula da shaidar zama ‘dan kasa (NIMC)……………..........…3 Bayani akan tsarin shedar zama dankasa (NIMS)……………………..…………….…4 Anfanin tsarin NIMS…………………………………………….………………..……..…..5 Lambar shedar zama ‘dankasa (NIN)……………………………………..…………….6 Yaushe ne za’a fara rajista?....................................................................................6 Yadda zakuyi rijistar samun lambar NIN………………………………………………8 Tsarin yin rijista da kanka……………………………………………………………….8 Tsarin yin rajista ga me bukatar taimako………………………………………………9 Muhimman takardu…………………………………………………………………………9 Menene dalilan daukar hoton yatsu da sauransu?.................................................. 10 Ta yaya za’a ajiye wannan bayanai naku?................................................................10 Yin gyara ko kuma canji ga bayanai………………………………………………….11 Shin akwai tsari na kare surrun bayananku kuma waye zai kare?............................11 Yaushene zaku iya samun wannan lamba ta (NIN)?.................................................13 Shin za’a bada katin shedar zama ‘dankasa kuwa?..................................................14 Menene tsawon lokaci da za’a dauka kafin a samu katin?.......................................15 Yaya kamannin katin yake?......................................................................................15 Ta yaya za’ayi amfani da wannan kati ko kuma lambar NIN?...................................16 Menene zai faru idan kuka manta labarku………………………………………………17 Menene zai faru idan katin ya bata ko ya lalace?.....................................................18 Shin za’a biya kudi kafin a bayarda da wannan lamba ko kati?................................18 Bayanai da tsarin taimako wajen amfani da tsarin NIMS…………………………19

5

MA’ANAR TAKAITATTUN SUNAYE: CAD Na’urar amfani da kati CIDR Cibiyar rajistar bayanai DNCR Tsohuwar Hukumar rajistar jama’a ta kasa FEPs Abokanan aiki na gaba-gaba ID Katin shaida LEA Hukumomin tsaro NID Rumbun bayanai shaidar zama ‘dan kasa NIMC Hukumar kula da shaidar zama ‘dan kasa NIMS Tsarin shaidar zama ‘dan kasa NIM Lambar shaidar zama ‘dan kasa NIS Hukumar kula da shige da fice ta kasa PIA Matakan kariya ga sirrinta bayanai PIVS Aikin tantance shaidar jama’a

6

BAYANAI AKAN HUKUMAR KULA DA SAMAR DA SHEDAR ZAMA ‘DAN KASA (NIMC) Kundin tsarin dokar NIMC ta shekara ta dubu biyu da bakwai (2007) ce ta bada izinin kafa hukukar samar da shaidar zama ‘dan kasa, aiyukan hukumar da karfin ikonta, samar da rumbun bayanan shedar zama ‘dan kasa, bayarwa da kuma amfani da katin komai da ruwanka, lambar shaidar zama dankasa (NIN) harha’dawa da tattara bayanan zama ‘dan kasa da muke dasu a yanzu. Dokar ta kuma baiwa hukumar ikon kafa dokoki da suka shafi ayyukan ta. dokar ta 2007 ta kuma kunshi shafe dokar da ta kafa tsohuwar hukumar rajistar jama'a ta kasa wato (DNCR) ta kuma mallake dukkanin kaddarorin wancan tsohuwar hukumar. DAGA WA’DANNAN BAYANAI, ZAMU IYA FAHIMATAR CEWA AIYUKAN HUKUMAR YA RABU ZUWA MAHIMMAN BANGARORI GUDA UKU:

A. Aikinta na farko shine kafa hukumar kula da tsarin shedar zama ‘dan kasa a matsayin muhimmiyar hanya kuma halartacciya a hukumance dan aiwatar da qudurori na yin gyara a bangaran tantance ‘dan kasa wanda doka ta amince da ita a sashe na 1,2,5 da na 6 na dokar NIMC ta 2007.

B. Kammala aikin da ya yi saura, da kuma mallakar kadarorin tsohuwar hukumar

rajistar jama'a ta kasa wato (DNCR) da su ka hada da duk ofisoshin maaikatunta na jihohi da kananan hukumomin kasa baki daya.

C. Kafa tsarin samar da lambar shaidar zama ‘yan kasa wato (NIMS) da gudanar

da shi ta hanyar-

i. Yiwa ‘ýan Najeriya da baki masu izinin zama rajista kamar yadda dokar ta tanada

ii. Kirkira da kuma samar da rumbun bayanai kan shaidar zama ‘dan

kasa.

iii. Bayar da wata lamba ta musamman wato (NIN) ga 'yan kasa da kuma ba’kin da suka cancanta.

iv. Bayar da katin komai da ruwanka ga duk 'yan kasa da suka kai

shekaru 16 ko sama da haka kuma wadanda su ka yi rajista

v. Samar da wata ingantacciyar hanyar da hukumomi da cibiyoyin tsaro na gwamnati zasu shiga rumbun bayanan shaidar zama dan kasa domin fayyace sahihan ýan kasa

vi. Daidaita da kuma tantance rumbun adana bayanai na sauran

ma'aikatun gwamnati domin kyautata aiyukan da zasu amfani jamaá.

vii. Hadin gwiwa tsakanin ma'aikatu masu zaman kansu.

7

viii. Rajistar haihuwa da mutuwa.

GUDANAR DA TSARIN KULA DA SHAIDAR ZAMA ‘DAN KASA (NIMS) An fara aiki gadan gadan ne a kan tsarin kula da shaidar zama ‘dan kasa (NIMS) a karshen shekara ta dubu biyu da tara (2009) bayan kammala nazari kan cewa hukumar ba zata iya amfani da mafi akasarin bayanan da ta gada daga tshohuwar hukumar kula da rijistar jama'a ta kasa ba wato DNCR. Ana fatan nan ba da dadewa ba duk wani ‘dan kasa da ya cancanta zai samu damar yin rajista a karkashin wannan tsari. Wannan littafi na dauke da bayanai akan manufar tsarin (NIMS) tare da alfanun sa ga gwamnati da kuma jama’ar kasa. Tsarin na NIMS na kunshe da rumbun bayanan shaidar zama dan kasa ko kuma cibiyar rajista (CIDR), kati mai ‘dauke da bayanai da kuma rukunin fayyace bayani akan kowanne ‘dan najeriya. Har ila yau ya kushi tsarin daidaita bayanai da hukumomi ke dasu a halin yanzu. Wani abu dake da ban sha'awa ga wannan tsari na NIMS shine samar da kayayyakin tattara bayanai kan shaidar zama ‘dan kasa na bai daya. Ana sa ran wannan zai kawo alfanu na zahiri ga gwamnati da kuma dukkanin 'yan kasa baki daya. FA’IDOJIN TSARIN SAMAR DA LAMBAR SHAIDAR ZAMA ‘DAN KASA (NIMS) Idan tsarin ya fara aiki gadan-gadan, zai samar da wad’annan abubuwa kamar haka:

a. Samar da sassaukar hanyar yin rijistar shaidar zama ‘dan kasa domin karba da kuma yin amfani da katin zama ‘dan kasa na komai da ruwanka wato (SMART CARD) da lambar shaidar zama ‘dan kasa (NIN).

b. Samar da kariya daga zamba ko katin jabu, da samar da tabbatacciyar

hanyar fayyace bayanai na bai daya.

c. Saukaka rayuwa ta hanyar bayyana ko kai wanene a nan cikin gida Najeriya dama kasashen wajen.

d. Inganta harkokin siyaysa ta hanyar saukaka aiyukan hukumar zabe.

e. Zai zama mai matukar wahala ga masu aikata munanan laifuka yin sojan

gona kuma hakan zai taimakawa gwamnati wajen inganta aiyukan tsaro a kasa.

f. Zai taimaka wajen tabbatar da ma’aikatan gwamnati na ainahi da ake da su ba na bogi ba

g. Zai taimaka wajen inganta darajar kud’in kasarmu, ya kuma inganta tsarin bada rance ga masu sana'o'i domin habaka tattalin arzikin Najeriya.

h. Zai taimaka wajen daidaitawa da kuma tattara bayanan shaidar zama ‘dan kasa a tsakankanin ma'aikatun gwamnati harma da masu zaman kansu domin kyautata amfani da dukiyar kasa, domin habaka tattalin arziki.

8

i. Zai bunkasa da kuma inganta aiyukan karbar ku’din haraji da sauran

ku’da’den shiga ta hanyar fayyace bayanai nan take.

j. Zai kare mutuncin kasarmu Najeriya a idanun duniya ta hanyar fayyace inda muka fito da kuma kasancewar mu sahihan ‘yan Najeriya.

Wannan tsari ne da zai ‘dauki dogon lokaci anayi dan haka bayyana dukkanin gara’basar sa a yanzu na da kamar wuya sai lokacin da mutane masu yawa sukayi rajista a karkashin tsarin. Adadin yawan jama'ar da ke cikin tsarin shine zai nuna yawan alfanun tsarin. Wannan tsari na NIMS ya sha bamban da na baya domin tsari ne da ya maida hankali wajen samarda sahihiyar hanyar tabbatar da shaidar zama dan kasa sabanin irin tsarin day a fi maida hankali a kan bada katin zama ‘dan kasa. LAMBAR SHAIDAR ZAMA ‘DAN KASA (NIN). Lambar shaidar zama dan kasa (NIN) - Wasu rukunin lambobi ne da za'a baiwa mutanen da sukayi rajista. Rijistar ta ‘kunshi cikakken suna da adireshin mutum tare da hoton yatsu, hannaye guda goma, hoto da kuma sa hannu na na'ura. Wannan duk za'ayi amfani da su ne a rumbun tattara bayanai domin tabbatar da cewa babu irin wannan bayanai da aka shigar a ciki. Da zarar an kammala wannan aiki za'a shigar da bayanan ne wajen ajiya tare da lamba ta musamman da aka makala mata. Ba za'a iya canza wannan lambar ba da zarar an baiwa mutum ita koda kuwa wanda aka baiwa ya mutu. Lambar ta NIN ita ce makullin dukkannin bayanai na mutum a rumbun bayanai kuma ita ce ake amfani da ita wajen fayyyace mutum a koina. YAUSHE NE ZA'A FARA YIN WANNAN RAJISTA? Da zarar abokanan aikinmu wato (FEPS) sun kammala shirye-shirye da sukeyi za'a fara. amma za'a fara aikin ne na gwaji a wasu zababbun yankuna na sassan kasar a shekara ta 2011. Don haka, za'a bukaci ku bada wasu bayananku, hoton yatsunku goma, hotunanku da kuma sa hannu domin samun damar yin wannan rajista. Za kuyi haka ne idan kuka isa zuwa cibiyar yin wannan aiki na musamman da za'a kafa nan gaba. kuna iyayin rajista ta hanyar yanar gizo wato internet. za’a iya samun wannan lamba acikin mako guda da yin rijista idan ba wata matsala aka samu ba. Bayan haka za'a baka katinka na shaidar zama ‘dan kasa a cikin wata ‘daya. Sai dai idan aka gano matsaloli acikin bayanan da ka bayar za'a sanar da kai a cikin kwana biyu wato sa’o’i 24 wata kila ma za'a iya gaiyatarka zuwa cibiyar da ka yi rajistar domin tantance bayanai da ka bayar ko neman karin bayani daga gareka.

9

YADDA ZA'AYI RAJISTA DOMIN SAMUN LAMBAR NIN: Dukkannin ‘dan kasa da kuma bako mai izinin zama da ya kai shekara 16 zuwa sama zai iya neman wannan lambar. Hanyoyin rajistar ba su da bambanci. Ko dai mutun ya shigar da bayanansa da kansa ko kuma maaikatan hukumar su taimaka masa wajen shigar da bayansa.A halin yanzu ana yin wasu shirye-shirye ta yadda zaa iya yiwa mutum rajista a ranar da aka haife shi, a kuma kamala shigar da sauran bayanai lokacin day a kai shekaru biyar (5) YADDA MAI YIN RAJISTA ZAI SHIGAR DA BAYANANSA DA KANSA Wannan tsari ne da zai taimakeka ka shigar da bayananka da kanka ta hanyar yanar gizo inda zaka bude shafin yanar gizo na hukumar ta nimc wato www.nimc.gov.ng ko kuma a kowace cibiyar yin rajista. Zaka cike fam sannan ka bugo takardar da ke ‘dauke da bayanan da lambar shaidar yin rajista mai ‘dauke da alamar shaidar rajista wacce ake kira 2d barcode. Sannan sai ka gabatar da wannan takarda ga jami'in dake cibiyar rajista mafi kusa da kai,shi kuma zai tantance bayanan da ka bayar sannan ya dauki hotonka da na yatsun ka da kuma sa hannunka. Har ila yau, za'a bukaci ka samar da wasu takardu ga wannan jami'in domin ya tantance gaskiyar bayanan da ka bayar adan yin rajista a tsarin na NIMS. Wad’annan takardu sun hada da takardar shaidar haihuwa, adireshin gida. TSARI DAN BUKATAR TAIMAKO:

Dangane da yadda za a taimaka maka ka yi rajista, za ka karbi fam na yin rajista

a cibiyar yin rajista mafi kusa. Kana iya cikawa da kanka, ko ka nemi wani

jami’i ya cika maka. Sannan sai ka mik’a fam din ga jami’in da yake yin

rajistar, ya shigar da dukkan bayanan a cikin naura mai kwakwalwa. Za a

tantance a kuma tabbatar da dukkan bayanan da ka rubuta. Bayan haka sai a

d’auki hotonka da na yatsun ,fuska,hannunka da na sa hannunka.

Bayan ka gama yin rajistar za’a sanar da kai ta hanyar ba ka rasit da yake nuna

cewar ka kammala rajistar. Wannan ne zai ba ka damar samun takardar shaida

ta wucin-gadi. Daga nan sai ka ci gaba da sauraro har lokacin da ka sami

lambarka ta dan kasa, sannan daga baya kuma hukumar ta NIMC ta mallaka

maka katin na SMART CARD mai dauke da lambar ka ta NIN. DALILAN ‘DAUKAR HOTON YATSUN HANNAYEN GOMA:

Dole ne a shigar da dukkan bayanai a kan ka,

domin a tsarin samar da lambar yan kasa wato

NIN ; lambar da aka ba ka da ita ake amfani a

10

adana dukkan bayanai na musamman a naura mai kwakwalwa da suka had’a da

hoton fuskarka da na yatsun hannunka, idan aka yi hakan to mawuyacin abu ne

a yi na jabu ko a sace su ko kuma su bata. Haka kuma da zarar an shigar da

hoton fuskarka da na yatsun hannunka, ba za a nemi ka sake yi ba sai kamar

bayan shekara biyar (5) nan gaba, lokacin da tsarin samar da lambar d’an kasa

ya kankama, hoton launin kwayar idon mutum kawai za a bukata.

Bayanai na halitta wad’anda ke rarrabe mutum, su ne suka fi sahihanci a tsarin

tantancewa na musamman. YADDA ZA’A AJIYE BAYANANKU: Za’a ajiye bayananku ne a babban rumbun tara bayanai na kasa cikin ingantacciyar kulawa da tsaro hakan zai bada damar fayyace ko kai wanene a ko ina kake a fadin kasar baza a baiwa kowa bayannanku ba, ba tare da izininkuba da kuma cikakken izini daga hukumar NIMC. Sai dai kuma dokar da ta kafa wannan hukuma ta nimc ta bada damar bayar da bayanan ku ba tare da izini ba ga hukumomin tsaro da kuma wasu hukumomi dake kula da laifuka na musamman wanda suka shafi na cin hanci da rashawa. Hukumomin sun ha’da da hukumar tsaro na farin kaya (SSS) hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) da kuma hukumar ‘yansanda ta kasa.(NPF).

11

12

Duk da haka, dole wadannan hukumomi su je kotu domin samun izinin karbar bayanan duk wanda suke bukata sakamakon wani dalilin da dokar ta amince das hi. GYARA DA KUMA YIN CANJIN BAYANAI: Kuna iya canza bayanan da kuka riga kuka bada. misali idan mace tayi aure tanaso ta canza zuwa sunan minjinta zata cike wani fam ko kuma ta fito da fam din daga shafin yanar gizo na hukumar. Sai a cike wannan fam ku kai cibiyar rajista mafi kusa daku. da zaran jami’an hukumar ta NIMC sun tantance wadannan bayanai akan tsofaffin bayanai sai a yi gyaran da kuke bukata. Sannan kuma za’a ajiye wadancan tsofaffin bayanai ko zasuyi amfani a inda kake bukatarsu. AKWAI TABBACIN SIRRINTA BAYANAI A KAI NA?

Kafin Kammala Tsarin Samar da Lambar Yan Kasa, Hukumar Samar da

Lambar Yan Kasa ta gudanar da nazari a kan Sirrinta Bayanai saboda fahimtar

had’arin da zai iya haifarwa ga mutum da kuma yadda za a kare aukuwar hakan.

An shigar da darusan da aka samu daga nazarin wajen kafa tsarin na NIMS,

musamman shirin sirrinta bayanai.

Ayyukan Hukumar Samar da Lambar yan kasa za su had’a da ajiye bayanai a

rumbun adana bayanai na k’asa don tabbatar da cewar daidai suke, sannan ana

sabunta su don kada wani abu ya same su. Ban da bibiyar yadda ake gudanar da

rajistar, a koyaushe Hukumar za ta ci-gaba da duba yadda ake amfani da

Lambar yan kasa da Katin na komai da ruwanka wato (Smart Card).

Ko da yake za a samar da cibiyoyin tuntub’a da kamfanoni masu zaman kansu

za su gudanar, Hukumar samar da lambar yan kasa za ta sa ido sosai a kan

wannan al’amari. Za a tabbatar da ingantattun matakai wajen samun damar

shiga Rumbun Adana Bayanai na Lambar yan kasa da kuma samar da

ingantaccen tsaro a kan bayanan. Don haka lokaci-lokaci Hukumar za ta bukaci

su ba ta bayani a kan yadda su ke adana bayanai da yin amfani da Lambar da

katin don tantancewa.

An had’a tsarin samar da lambar yan k’asa da rumbun adana bayanai na kasa ta

hanyar naura mai kwakwalwa ta yadda ana da masaniya a kan duk wasu

muamuloli nasu. Kamar dai yadda wasu sassa na dokar da ta kafa Hukumar ta

tanada, za a tilasta wa dukkan hukumomi ko k’ungiyoyi da suke ma’amala da

Tsarin samar da lambar yan kasa su bayar da duk wani bayani idan bukatar

hakan ta taso.

Haka kuma ta NIMC ta fayyace tsarin sirrinta bayanai a matsayin makami na

tabbatar da an kare hakkin jama’a a wajen tattara bayanai da adana su a rumbun

adana bayanai, da yin amfani da lambar yan kasa da kuma katin Shaida.

13

Dangane da haka Hukumar ta dauki alhakin kare sirrinku. A nan gaba ma za ta

nemi a sake yin gyara a kan dokokin kare da sirrinta bayanai. YAUSHE NE ZAN SAMI LAMBAR TA NIN BAYAN NAYI RAJISTA??

An shirya tsarin samar da lambar yan kasa ne ta yadda da zarar mutum ya yi

rajista kuma an tantance bayanan da ya bayar, sai a ba shi lamba. Bayan shigar

da bayanan a cibiyar adana bayanai, za ka iya samun lambarka ta NIN a cikin

‘yan dakikoki ko mintina ko awoyi ko kuma kwanaki, ya danganta da hanyar da

ka bi. Wasu daga cikin wannan hanyoyi sun hada da takaitaccyar sako ta wayar

salula SMS, kamfanonin kai sakonni wato courier ko kuma hanyar sako na Email. SHIN ZA’A BADA KATIN SHAIDAR ZAMA ‘DAN KASA KUWA? Hakika za’a bada kati, sai dai wannan karon katin na ‘dauke da bayanai a ciki zai zama kamar katin komai da ruwan ka ne ta yadda zai taimaka wajen bayyana ko kai wanene a koina a ko wanne lokaci a kuma kowanne irin yanayi. Zai kuma bada damar kuyi kasuwanci dashi domin yana dauke da tsarin biyan kudade a tattare da katin. Hukumar ta NIMC ta kuma tanadi wani tsari na musamman ta yadda zaku iya tantance ko ku su wanene ba tare da kati ba sai dai ka karanto lambar taka ta NIN Kasancewar yanzu mutane na amfani da kati daban-daban kamar katin shaidar wajen aiki, fasfo, lasisin tukin mota da dai sauransu domin bayyana ko su, su wanene, sai dai irin wadannan katina na jawo dalilin bada wasu bayanai da basu kamataba. Sau dayawa bazaka iya gane inda katin ya fito ba. Akasarin hanyar tantacewa shine ta duba hotunan dake jikin kati kamar yadda bankuna sukeyi a fa’din Najeriya. Wannan hanya bata da inganci kuma tana jawo aikata zamba ta hanyar yin sojan gona. Wannan tsarin, ya danganta da irin bayanin da ake bukata wajen gudanar da cinikayya, za’a fayyace bayanan ku ta hanyar duba bayanan da hoton dake kan katin ko kuma shigar da lambar NIN zuwa yanar gizo ko kuma hotunan yatsu ta hanyar anfani da na’urar (CAD) ko kuma me gaba daya ta hanyar binciken rumbun bayanan shaidar zama ‘dan kasa wajen amfani da hoton yatsu akan yanar gizo ko kuma akasin haka. Bayanai da kuma tsarin matakan tsaro dake kan katin zasu zama karbabbu ne a bisa dokokin inganci na kasa da kasa wato (ISO 27001, ICAO 9303) TSAWON LOKACIN DA ZA’A JIRA KAFIN A SAMU KATIN: An tsara yadda mai kati zai iya samun katinsa a cikin wata ‘daya amma sati ‘daya ne kawai ake bukata wajen buga katin. Zai dauki kimanin sati biyu idan ku ka je da kanku kar’bar katin. A tsarin hukumar ta NIMC za’a kai katunanne ta hanyar kamfanonin aika sakonni na courier ga masu shi. Don haka ana bukatar dan lokaci domin isar da katunan ga masu ita cikin sauki. Za’ayi wasu bincike da suka hada da na tsaro kafin akai katin ga masu shi. Baza a amince wani ya kar’bawa wani katin ba. Wani abun sha’awa kuma shine, zaka iya bin sahun yadda ake tafiyar da yima katin, saboda akwai wani sashe na musamman dake aiki ba dare ba rana da za’a iya

14

tuntu’ba a koda yaushe domin taimakawa wajen yin hakan. Za’a sanar da kai ta hanyar sakon wayar hannu ko E-mail idan aka kammala aikin katin. YAYA KAMANNIN KATIN ZAMA ‘DAN KASAR YAKE? Za’a tabbatar da cewa dukkannin abubuwan dake kan wannan kati sun dace da dokar ingancin kaya ta kasa da kasa. Za’a iya ganin misalin katin anan kasa. Sai dai saboda dalilai na tsaro, ba a bayan ainahin yadda katin ya ke ba. Akwai wani magadiso dake dauke da bayanai akan mutum, lambar NIN, sa hannu da kuma hotunan yatsun hannaye da ka iya fayyace bayanan ko kai wanene ta dukkannin hanyoyi da aka tanada domin yin hakan. Akwai alamomi na tsaro masu yawa da aka tanada domin gujewa yin katin na jabu. Bayan haka za’a sarrafa katin ne anan cikin gida Najeriya domin samar da aikinyi da kuma tabbatar da an kammala aikin cikin lokaci. YADDA AKE ANFANI DA LAMBAR NIN KO KATIN SHAIDAR ZAMA DAN KASA Akwai yanayi da dama da za’a bukaci ka fayyace ko kai wanene. Lambar NIN ko katin shaidar zama ‘dan kasa zai baka damar yin haka ta hanyoyin da kowa na iya gamsuwa dasu. Anan akwai wani tsari da ya ke bukatar mutum yasaka katin a cikin wata na’ura ta musamman wato (CAD) sannan ya dora hannunsa akan wannan na’ura domin tantance hoton zanen yatsu na yanzu da kuma wanda aka dauka a lokacin da aka baka katin. Akwai kuma tsarin tantancewa ta hanyar yanar gizo wato internet wanda ke da alaka da rumbun ajiyar bayanan. Ta wannan hanya za’a iya gane ko wanene kai ta wajen samun amsar “e ko a’a” akan mutumin da ake kokarin tantancewa. Za’a iya tantance bayanai masu zurfi dangane da girma ko muhimmancin mu’amalar da ake shirin yi. Dokar da ta kafa hukumar ta NIMC ta 2007 sashe na 27, ta tanadi cewar Hukumar zata sanar da wata rana wadda amfani da wannan lamba ta NIN zata zama dole akan kowa domin yin wasu maamuloli kamar haka:

A. Nema da kuma bayarda katin fasfo domin tafiye tafiye. B. Bude asusun ajiya a bankuna.

15

C. Sayan hannun Jari da Inshora. D. Yayin canji ko cinikin fili idan dokar amfani ta kasa ta zayyana hakan. E. Mu’amalar da ta shafi kudin fansho kamar yadda dokar fansho ta 2004 ta

zayyana. F. Mu’amalar da ta shafi tsarin Inshorar lafiya ta kasa (NHIS) G. Mu’amalar data hada da duk wani tsarin tallafi na Gwamnati H. Biyan kudaden ciniki ko bashi a bankuna da masana’antu. I. Rajistar yin zabe J. Biyan kudaden haraji K. Wasu ayyuka masu muhimmanci na gwamnati L. Da kuma dukkannin mu’amalar da hukumar NIMC zata bayyana a jerin

matakan gwamnatin tarayya.

ME ZAI FARU IDAN MUTUM YA MANTA LAMBARSA TA NIN?

Idan ka manta da Lambarka ta d’an kasa, za ka iya samun ta a Cibiyar yin

Rajista,ko ka cike fam na neman bayanai ka kai kowacce daga cibiyoyin

tuntuba da kamfanoni masu zaman kansu suke gudanarwa.

ME ZAI FARU IDAN KATI YA ‘BATA KO YA LALACE?

Ya zama wajibi ga duk ‘dan kasa ya kula da adana katinsa cikin kyakkyawan yanayi. Amma idan hakan ta faru, zaka iya kai rahoto zuwa ofishin Hukumar

NIMC mafi kusa da kai. Hukumar za ta goge shi daga naurarsu mai

kwakwalwa, kuma babu wanda zai iya sake amfani da shi har abada. Da

ma Lambarka ta dan kasa aba ce wadda babu wanda zai iya amfani da

ita.

Duk da haka, idan kana so a sake maka katin shaidar, sai ka cike takardar

nema a Cibiyar yin Rajistar da abokan huldarmu suke gudanarwa. Za ka

tura bukatar sake katin Shaidar zuwa ga adireshinmu ta hanyar sadarwa ta

naura mai kwakwalwa,sai ka fito da takardar bayani, wadda za ka kai

cibiyoyinmu na yin rajista mafi kusa da kai. Ko kuma ka je da kanka ka

cike fam din nan take. Jami’in yin rajistar zai tantance bayanin da ka

bayar dangane da wadanda ake da su. Da zarar an tantance, sai a fara

shirin ba ka sabon katin shaida wanda bisa ka’ida ba ya dadewa (mako

daya). Amma za a bukaci ka biya kudin sabuntawa. SHIN ANA BIYAN KUDI NE KAFIN KARBAR WANNAN LAMBA KO KATI? Yin rajista da kar’bar lamba da kati duk za’ayi shine a KYAUTA. Sai dai idan katinku ya ‘bata ko ya lalace to zaka biya kafin a sake baka wani sabo. Za’a fayyace adadin ku’di da za’a biya, sannan adadin ku’din yana iya canzawa daga lokaci zuwa lokaci. BAYANAI DA KUMA TAIMAKO WAJEN AMFANI DA TSARIN NIMS: A halin yanzu ana kokarin kafa ma’aikatu masu zaman kansu da zasu zama cibiyoyin tuntu’ba, dan samar da bayanai da kuma bada tallafi akan yadda za’ayi amfani da wannan tsari na NIMS. Har ila yau za’a iya samun bayanai akan wannan

16

tsari na NIMS daga wata cibiya ta sadarwa da zata zama a bude dare da rana. Sannan za’a zabi wasu kamfanonin aikawa da sako na courier domin aikin kai katinan da kuma lambobi idan bukatar hakan ta taso. Zaku iya karbar naku a cibiyoyin rajista mafi kusa da ku. Hukumar na da kudirin tabbatar da kyakkyawan tsarin samar da bayanai ga ‘yan Najeriya da baki masu izinin zama a kasa, domin gamsuwa wajen isar da bukatun jama’a ta hanyar amfani da manyan yaruka fiye da guda hu’du (4) da ake amfani dasu a Najeriya. Za’a samar da ingantaccen tsarin sadarwa da ya dace da wannan tsari na NIMS. DOMIN NEMAN KARIN BAYANI: +234 702 5420 706-9 +234 704 0144 452-7 Shafin yanar gizo: http://www.nimc.gov.ng E-mail: [email protected] Hukumar dake kula da kuma samar da Lambar shaidar zama ‘dan kasa Dake lamba 11 Sokode Crescent, daura da titin Dalaba, Wuse Zone 5. P.M.B 18, Garki, Abuja, Najeriya.