Ôhar abada zuciyar biladama ta kasance …victimssupportfundng.org/hausa.pdfbabu wata alÕumma da...

20
Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa ‘HAR ABADA ZUCIYAR BILADAMA TA KASANCE MAI TAUSAYI DA KUMA KARAMCI’ Maigirma Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan, GCFR

Upload: others

Post on 02-Apr-2020

1 views

Category:

Documents


0 download

TRANSCRIPT

Page 1: ÔHAR ABADA ZUCIYAR BILADAMA TA KASANCE …victimssupportfundng.org/hausa.pdfBabu wata alÕumma da bata daba dandana rikici ba. Amma a matsayinmu na mutane da Ubangiji Ya halitta,

Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa

‘HAR ABADA ZUCIYAR BILADAMA TA

KASANCE MAI TAUSAYI DA KUMA KARAMCI’

Maigirma Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan, GCFR

Page 2: ÔHAR ABADA ZUCIYAR BILADAMA TA KASANCE …victimssupportfundng.org/hausa.pdfBabu wata alÕumma da bata daba dandana rikici ba. Amma a matsayinmu na mutane da Ubangiji Ya halitta,

2 Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa

Page 3: ÔHAR ABADA ZUCIYAR BILADAMA TA KASANCE …victimssupportfundng.org/hausa.pdfBabu wata alÕumma da bata daba dandana rikici ba. Amma a matsayinmu na mutane da Ubangiji Ya halitta,

HAKKIN MALLAKA (m) 2014 OFISHING MATAIMAKIN SHUGABAN KASA NA MUSAMMAN KAN BINCIKE DA

TATTARA MUHIMMAN BAYANAI, ABUJA

Ba a yarada da juyin wannan littafin domin kasuwanci, ko bayar da aronsa ta kowace fuska ba. Duk yadda ake bukatar juya littafin ba

daidai ba ne, face da yardar mawallafa ba. Haka kuma duk yadda aka so yin amfani da shi, tilas a nemi rubutacciyar yarda daga mawallafa,

tare da bin dokokin dab’i.

3

Page 4: ÔHAR ABADA ZUCIYAR BILADAMA TA KASANCE …victimssupportfundng.org/hausa.pdfBabu wata alÕumma da bata daba dandana rikici ba. Amma a matsayinmu na mutane da Ubangiji Ya halitta,

“AN SAMAR DA MU NE DOMIN NUNA WA JUNA SO DA KAUNA MARA

MISALTUWA; AN HAIFE MU DOMIN MU GINA AL’UMMA, AMMA BA DON

MU RASA TA BA”

4 Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa

Page 5: ÔHAR ABADA ZUCIYAR BILADAMA TA KASANCE …victimssupportfundng.org/hausa.pdfBabu wata alÕumma da bata daba dandana rikici ba. Amma a matsayinmu na mutane da Ubangiji Ya halitta,

JawabinMaigirma Shugaban Kasa Goodluck Ebele Jonathan, GCFR.

a wajen bikin Kaddamar daKwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda

Hare-haren Ta’addanci ya shafa

a Fadar Shugban Kasa – Abuja.Laraba 16 ga Yuli, 2014

5

Page 6: ÔHAR ABADA ZUCIYAR BILADAMA TA KASANCE …victimssupportfundng.org/hausa.pdfBabu wata alÕumma da bata daba dandana rikici ba. Amma a matsayinmu na mutane da Ubangiji Ya halitta,

6 Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa

Inayi muku barka da zuwa wannan taro mai

muhimmanci na kaddamar da Kwamitin Kafa Asusun

Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa.

Mun taru ne a wannan wuri a yau domin fara gabatar

da shirin gwamnati na taimakawa mutanenmu da

ayyukan ‘yan ta’adda ya shafa ta kowace hanya a kasar

nan. Wannan taron ba irinsa muke addu’ar gani ba.

A matsayin Nigeria na matashiyar kasa mai cike da

buri, naso ace a yau ina kaddamar da kwamiti akan

dabarun cigaba. Amma munsami kanmu a cikin wani

yanayi na takaici saboda ayyukan ashsha mara kan gado

na wasu ‘yan tsirari da suke zubarda jinin mutanen da

basu ji ba basu gani ba a wannan kasa tamu.

Yakamata, kuma yana da muhimmanci mu tunawa

MCYWPCPOW�VCTKJK�MCǣP�OWEK�ICDC��0KIGTKC�FCK�DCVC�taba samun kanta a haka ba. A lokutan baya, gaskiya

ne, munyi fama da rikice-rikicen kabilanci dana addini.

Babu wata al’umma da bata daba dandana rikici ba.

Amma a matsayinmu na mutane da Ubangiji Ya halitta,

munyi kokari mun zauna da juna dai-dai da yadda

zamu iya tare da fuskantar kalu-balen dake gabanmu

sannan kuma munyi aiki tukuru domin karfafa dankon

haduwarmu.

“ABIN SANI SHI NE BABU AL’UMMAR DA TA FI KARFIN FADAWA CIKIN BALA’I DA

FITINTINU“

Page 7: ÔHAR ABADA ZUCIYAR BILADAMA TA KASANCE …victimssupportfundng.org/hausa.pdfBabu wata alÕumma da bata daba dandana rikici ba. Amma a matsayinmu na mutane da Ubangiji Ya halitta,

7

Idan muka sabawa junanmu, nan da nan muke

UCUCPVCYC�� OWMG� EKICDC� FC� \COC� VCTG� EKMKP� NCǣ[C��Bamu taba aikata ta’addanci ba a duk lokutan da muke

rikicinmu na bambamci. Amma wannan halin rayuwar

namu ya sami nakasu a ranar 25 ga watan Disamba

na shekarar 2009, a lokacin da wani dan Nigeria mai

shekaru 23 yayi kokarin kunna wani makamashi dangin

nakiya daya boye a cikin suturassa da yake sanye da ita

a cikin Jirgin Saman Northwest Airline mai lamba 253,

dake kan hanyarsa daka Amsterdam zuwa garin Detroit

na Jihar Michigan, a kasar Amurka.

Koda yake burinsa bai cika ba kuma an kubutar da

rayukan fasinjojin 289, amma kuma wannan shirin

nasa ya tabbatar da cewa ashe dai akwai wasu tsirarin

‘yan Nigeria da suka rungumi ta’addanci a matsayin

tsarinsu na rayuwa.

A halin yanzu zamu daina musun cewa waita’addanci

ya shigo kasarmu tare da mummunan sunadaransa.

5JGMCTCT������ VC�DWFG�YCPK� UJCǣ�OCK� VCMCKEK��$QMQ�Haram, wata kungiyar mutane marasa tausayi, ta

daura damarar tada zaune tsaye a kasarmu. Wannan

tsari nasu yayi sanadin mayarda Mata sun zama Masu

takaba kuma Yara kanana sun zamo Marayu.

>> CI GABA A SHAFI NA GABA

Page 8: ÔHAR ABADA ZUCIYAR BILADAMA TA KASANCE …victimssupportfundng.org/hausa.pdfBabu wata alÕumma da bata daba dandana rikici ba. Amma a matsayinmu na mutane da Ubangiji Ya halitta,

8 Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa

Sun kashe, sun raunata kuma sun saka tsoro a cikin

zukatun mutane. Sun rusa kauyuka, sun lalata dukiyar

mutane kuma sun ruguza hanyoyin neman abincin

mutane da yawa. Sun daura damarar yaki maras ma’ana

da jami’anmu na tsaro wanda ya jawo asarar rayuka da

dukiya da suka wuce misali.

Gaskiyar magana itace a yanzu muna fuskantar wasu

mutane da zuciyarsu ta karkata zuwa yarda da yadda

aka koya musu su yarda cewa aikin Ubangiji suke.

Ina mai tabbatar da cewa karya fure take bata ‘ya’ya.

Makiya jama’a ne kawai zasu dinga zubar da jinin

mutane babu gaira babu dalili kuma su dinga fakewa

da halayen mutanenmu na zamantakewa wajen watsa

ra’ayinsu da cusa musu wannan ra’ayin domin su karbi

OCPWHQǣPUW�MWOC�UW�FKPIC�COHCPK�FCUW�C�C[[WMCPUW�na kashe jama’a.

Ba zamuyi kasa a gwiwa ba wajen ganin cewa mun

tabbatar da anyi hukuncin da ya dace ga dukkan wanda

[CMG�FC�JCPPW�YCLGP�CKMCVC�NCKǣ�IC�LCOCƷC��

Su kuma wadanda suke da sha’awar ganin mutane a

cikin yanayin ban tausayi da radadi, kuma ana kaca-

kaca da sassan jikin mutum, jini na kwarara ta ko wace

“SUNA TA KASHE WADANDA BA SU JI BA, BA SU GANI BA, BA TARE DA LA’KARI DA HAKKI BA.

KUMA YAWANCI MASU RAUNI NE, WADANDA KE BIN DOKA DA ODA TA KASA”

Page 9: ÔHAR ABADA ZUCIYAR BILADAMA TA KASANCE …victimssupportfundng.org/hausa.pdfBabu wata alÕumma da bata daba dandana rikici ba. Amma a matsayinmu na mutane da Ubangiji Ya halitta,

9

hanya a duk lokacin da aka kaddamar da harin ta’adda,

to muna sheda muku cewa babu inda zaku buya. ‘Yan

Nigeria zasu tona muku asiri. Mutane nagari sun

tsaneku dukkan inda kuka je a fadin duniyar nan.

Muna godiya saboda goyon bayan da muke samu daga

kasashen waje da kuma hadin kai da muke samu daga

makwabtanmu. Wannan yana kara mana kwarin gwiwa

kuma muna da tabbacin cewa kwanakin Boko Haram a

kirge suke. Lokaci kawai muke jira.

Yakin da mukeyi da ta’addanci yana nan daram. Idan

mutane suka karanta labarin tashin bomb a kafar

yada labarai, zai zama kamar tatsuniya ce ga wadanda

babu ruwansu da abinda ya faru. Wata tsohuwar karin

magana tana cewa idan mutum ya hangi makarar gawa

zai dauka kamar daurin itace ne.

Amma mu a wajenmu iyaye maza da mata da kuma

iyalan mutanen da harin ta’addancin ya shafa, labarin

yasha bambam.

Wadan can mutanen ‘Ya’ya ne, Kanne ne maza da mata,

Iyaye ne maza da mata ko kuma ‘Yanuwane na kusa

dana nesa ! ‘Yan Nigeria ne nagari masu kishi da fatan

alheri da kaunar kasarsu.

>> CI GABA A SHAFI NA GABA

Page 10: ÔHAR ABADA ZUCIYAR BILADAMA TA KASANCE …victimssupportfundng.org/hausa.pdfBabu wata alÕumma da bata daba dandana rikici ba. Amma a matsayinmu na mutane da Ubangiji Ya halitta,

10 Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa

Ina kira ga dukkan ‘Yan Nigeria da su tashi su hada

kai domin taimakawa jami’anmu na tsaro akan yaki da

ta’addanci. Suna aiki ba dare ba rana a cikin wani yanayi

mai wahala. Wani abin takaici shine idan jami’anmu na

tsaro suka hambarar da shirin kawo harin abokan gaba

‘yan ta’adda sau 1000, to nasarar da ‘yan ta’adda suka

samu guda daya (1) ce zata zama kanun labarai kuma

zata nuna cewa kamar jami’anmu na tsao basa kokari.

Wannan yana daya daga cikin abubuwan da zamu

maida hankalinmu akai domin mu magance su. Muna

da nauyin ‘Yan Nigeria a kanmu na ganin cewa mun

sami nasara akan ta’addanci. Muna bada muhimmanci

ga rayuwar ko wane dan Nigeria kuma zamu cigaba

da aiki tukuru babu dare balle rana domin muga mun

murkushe masu wannan tayar da kayar baya.

Manyan baki mata da maza, dukkan wadanda wannan

ta’addanci ya shafa suna bukatar taimako. Bazamu iya

musanya rayuwar yaron da aka salwantar da ita ba.

Bazamu iya musanya rayukan maza da matan da aka

kashe ba. Ba zamu iya mayarda karyayyun kasusuwan

sassan jama’a kamar yadda suke ba. Bazamu iya dauke

jimami da radadin halin kunchi da aka saka jama’a a

ciki ba.

Tunanin da aka sakasu a ciki abin al’ajabi ne domin

wasu har iya tsahon rayuwarsu kuma akan abinda basu

“MUHIMMAN MUTANE MASU MUTUNCI A IDANUN DUNIYA, SUN YI TIR DA KU”

Page 11: ÔHAR ABADA ZUCIYAR BILADAMA TA KASANCE …victimssupportfundng.org/hausa.pdfBabu wata alÕumma da bata daba dandana rikici ba. Amma a matsayinmu na mutane da Ubangiji Ya halitta,

11

san hawa ba basu san sauka ba. Iyakar abinda zamu

iyayi a wannan lokacin shine mu basu gudummawar

abinda zai sanya su kishin-gida akai sannan mu mika

musu hannayenmu na ‘yan-uwantaka mu nuna musu

cewa muna tayasu takaici da bakin ciki.

Shi wannan Kwamiti na Kafa Asusun Taimakawa

wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa yana daya

daga cikin tsare-tsaren da mukeyi na kawo karshen

wannan annoba. Gwamnati ta daura damarar kawo

karshen wannan rikici.

Ayyukan ta’addanci sun zamo annobar data haifar da

daya daga cikin kalu-balen da gwamnatocin kasashe

da yawa a duniya suke fama da ita. ‘Yan ta’adda suna

kawo cikas ga rayuwar jama’a ta yau da kullum. Suna

saka tsoro da fargaba ga jama’a kuma suna kawo cikas

ga ayyukan gwamnati. Amma basu taba yin nasara ba.

Basu sami nasara ba a Gabas ta Tsakiya, a Amurka, a

Sin (China), a Colombia, a Italiya, a Ingila da Kenya

da sauransu. Kuma baza suyi nasara ba a Nigeria.

Da taimakon dukkan ‘yan Nigeria, zamu tabbatar da

basu sami nasara a Nigeria ba. Dole ne Alheri yayi

nasara akan Mugunta.

5CDQFC�JCMC�PG�OWMC�VCVVCTQ�YCUW�ǣVCVVWP�ƶ[CP�0KIGTKC�

>> CI GABA A SHAFI NA GABA

Page 12: ÔHAR ABADA ZUCIYAR BILADAMA TA KASANCE …victimssupportfundng.org/hausa.pdfBabu wata alÕumma da bata daba dandana rikici ba. Amma a matsayinmu na mutane da Ubangiji Ya halitta,

12 Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa

a karkshin Dattijon da ake girmamawa kuma Gwarzon

namiji, General Yakubu Danjuma, wanda zai sami

taimakawar kwararren ma’aikaci Fola Adeola. Zasu

sami taimakawar wasu kungiyoyin taimakon jama’a na

duniya da kuma wasu muhimmman ‘yan Nigeria da

aka fadi sunayensu tunda farko. Zamu tabbatar da cewa

mun agazawa wadanda suka shiga uku babu gaira babu

dalili sanadin ayyukan ‘yan ta’adda.

Yanzu zanyi wani takaitaccen bayani akan wadannan

muhimman ‘yan Nigeria da suka amince suyiwa kasarsu

aiki a wannan kwamiti. Bayanin tarihin rayuwarsu ya

nuna cewa sun tserewa sa’oinsu. Amincewarsu suyi

aiki a wannan kwamiti ya nuna babbar sadaukarwa.

Wadannan hamshakun ‘yan kishinkasa sun amince su

UCFCWMCT� FC� NQMCEKPUW� FC� MCTǣPUW� FQOKP� VCKOCMQP�mabukata. Sun yarda su bada gudummawar lokutan

da yakamata ace sunyi amfani dashi wajen bunkasa

kasuwancisu ko kula da iyalansu ko shakatawa. Sun

COKPEG� UW� DCFC� NQMCEKPUW� FC� MCTǣPUW� IC� DCDDCT�kasarmu Nigeria.

Muna Godiya kwarai.

Gwamnati tana kara tabbatarda shirinta na taimakon

mutanen da ayyukan ta’addanci ya shafa domin rage

“AL’UMMAR NIJERIYA NA DA HAKKI A KANMU, KUMA MUN YI ALWASHIN CIKA MUSU WANNAN

HAKKIN, WATO YAKI DA TA’ADDANCI”

Page 13: ÔHAR ABADA ZUCIYAR BILADAMA TA KASANCE …victimssupportfundng.org/hausa.pdfBabu wata alÕumma da bata daba dandana rikici ba. Amma a matsayinmu na mutane da Ubangiji Ya halitta,

13

musu radadin ciwon da ‘yan ta’adda suka janyo.

Zamu basu kulawa ta musamman domin su kara

amincewa da cewa akwai mutanen kirki na gari a

YCPPCP�FWPK[C�DC[CP�OCUW�OWIWP�PWǣ�

Shugaba, manyan baki maza da mata, zuciyar dan

Adam mai tausayice kuma mai taimako ce. Ina kira ga

‘yan wannan kwamiti dasu garzaya suje su kwankwasa

MQHQǣP�\WEK[CT�OWVCPG�FC�MWPIK[Q[KP�FC�UWMC�MCOCVC��Ina da tabbacin cewa zaku tara dukkan abinda ake

bukata domin taimakawa wajen gyara karayar da muka

samu a halin zamantakewarmu.

Akwai mutanen kirki da basu amince da akidar da

‘yan ta’adda ba wadanda suka maida kashe mutane da

nakasasu shine halin rayuwarsu kuma suna tunanin zasu

lalata tafarkin tunaninmu na alheri, to muna tabbatar

musu da cewa zamu tashi tsaye domin murkushesu.

Mun kafa wannan kwamiti ne domin a sami hanyar

da dukkan mutane da kungiyoyin da suke da niyyar

taimakawa zasu bada taimako domin ‘yan uwanmu

maza da mata domin rage radadin halin kaka-nikayi da

suka sami kansu babu dalili.

Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-

>> CI GABA A SHAFI NA GABA

Page 14: ÔHAR ABADA ZUCIYAR BILADAMA TA KASANCE …victimssupportfundng.org/hausa.pdfBabu wata alÕumma da bata daba dandana rikici ba. Amma a matsayinmu na mutane da Ubangiji Ya halitta,

14 Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa

haren Ta’addanci ya shafa zai taimaka wajen shirya

gangami domin hada kaya da sauran gudummawar da

za’a taimakawa wadanda ta’addancin ya shafa. Ina kira

gu dukkan ‘yan Nigeria na gari da kuma wadanda ma ba

‘yan Nigeria ba, da sauran jama’a da kungiyoyi dasu bada

gudummawarsu ga wannan asusu. Wadannan mutane

suna neman taimakonmu da tausayinmu. Yakamata mu

nuna cewa muna tausayawa kuma bazamu sake wasu

masu wata manufa suyi sami nasara ba.

Zamuyi dukkan abinda yakamata muyi domin taimakon

mutanenmu da suke cikin bukata. Amma fa wannan

jan aiki ne. Gwamnati ita kadai bazata iya ba. Zanyi

amfani da wannan lokaci domin na godewa dukkan

‘yan Nigeria dake gida da waje da kuma kungiyoyi na

duniya saboda taimako da gudummawar da suke bamu

a wannan halin da muke ciki.

a lokacin da muka shiga halin kaka-nikayi, taimako da

gudummawar da muka samu sun kara mana kwarin

gwiwar cewa akwai alamar nasara kuma kwanan nan

komai zai zamo tarihi. Nigeria hadaka ce ta makwabta,

‘yan-uwa da abokai a dunkule a waje daya. A ko wane

lokaci muna bukatar juna. Nigeria gaba daya iyali

daya ne.

“DUKKANIN WADANDA SUKA FADA CIKIN WANNAN BALA’I, SUNA MATUKAR

BUKATAR KULAWA”

Page 15: ÔHAR ABADA ZUCIYAR BILADAMA TA KASANCE …victimssupportfundng.org/hausa.pdfBabu wata alÕumma da bata daba dandana rikici ba. Amma a matsayinmu na mutane da Ubangiji Ya halitta,

15

Saboda haka, Ina kira ga dukkan ‘yan Nigeria –

Dalibai, Matasa, Samari da ‘Yanmata, Maza da Mata

– da suyi karatun tanatsu suyi tunanin halin da

wadannan mutane suka sami kansu kuma su taimaka

musu. Wannan kalubalen bana masu kudi bane kawai.

Gudummawa bata yawa bata kadan kuma za’a yabawa

dukkan gudummawar da aka bayar. Ina kira ga ‘yan

Nigeria dasu taimaka koda ta hanayar amfani da wayar

VCPICTCJQP�VCǣ�FC�IKFCP�EG�VC�UCNWNC�

Shugaba, ayyukan wannan kwamiti sune kamar haka:

a. A lalubo hanyoyin da za’a kafa isasshen asusun

da zai taimakawa wadanda ayyukan ta’addanci ya

shafa.

b. A kafa ginshikin madafun da za’ayi amfani dasu

wajen kafa asusun.

c. A binciko mutane, yankunan jama’a, kayyayki da

kadarorin da ayyukan ta’addanci ya shafa.

d. A tantance kuma a lissafa irin taimakon da

yakamata a baiwa dukkan wanda abin ya shafa.

e. A ajiye, a rarraba kuma a dinga gudanarda asusun

>> CI GABA A SHAFI NA GABA

Page 16: ÔHAR ABADA ZUCIYAR BILADAMA TA KASANCE …victimssupportfundng.org/hausa.pdfBabu wata alÕumma da bata daba dandana rikici ba. Amma a matsayinmu na mutane da Ubangiji Ya halitta,

taimakon da aka samu domin wadanda abin ya

shafa kamar yadda yakmata.

f. A fuskanci dukkan wani kalubale da zai iya tasowa

kuma ayi maganinsa kamar yadda yakamata.

g. A baiwa gwamnati shawara akan dukkan wata

matsala da zata iya tasowa dangane da ko akan

CDKPFC� [C� UJCǣ� VCKOCMQP� YCFCPFC� C[[WMCP�ta’addanci ya shafa.

Manyan baki maza da mata, wannan wata dama ce da

muka samu da zamuyi amfani da ita wajen nunawa

duniya cewa ramin karya kurarre ne. Wannan dama ce

da zamu tabbatarwa da mutane cewa mu duka ‘yan-

uwan juna ne. An haifemu mu kaunaci juna amma ba

muki juna ba. An haifemu mu gina amma ba mu rusa

ba. An haifemu mu tallafawa rayuwa amma ba mu

kashe ba. An haifemu mu kare amma ba muyi ta’adi ba.

Na gode muku da kuka saurari wannan jawabi nawa

cikin natsuwa. Allah Ubangiji Yayiwa kasarmu Nigeria

albarka.

Nagode muku.

“ALKAWARIN ALLAH NE ZAI TAIMAKI GASKIYA, KUMA YA KARYA SHAIDANU”

16 Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa

Page 17: ÔHAR ABADA ZUCIYAR BILADAMA TA KASANCE …victimssupportfundng.org/hausa.pdfBabu wata alÕumma da bata daba dandana rikici ba. Amma a matsayinmu na mutane da Ubangiji Ya halitta,

17

“INA KIRA GA ‘YAN NIJERIYA DA SU KAWO GUDUNMAWARSU HAIKAN

DON TALLAFAWA WADANNAN BAYIN ALLAH, KAI KO DA TA HANYAR

WAYOYINSU NA GSM NE”

Page 18: ÔHAR ABADA ZUCIYAR BILADAMA TA KASANCE …victimssupportfundng.org/hausa.pdfBabu wata alÕumma da bata daba dandana rikici ba. Amma a matsayinmu na mutane da Ubangiji Ya halitta,

18 Kwamitin Kafa Asusun Taimakawa wadanda Hare-haren Ta’addanci ya shafa

MEMBONIN KWAMITIN

(1) Gen. Theophilous Danjuma (Rtd), GCON - Shugaba

(2) Mr. Fola Adeola - Mataimakin Shugaba

(3) Alh. Mohammed Indimi - Memba

(4) Alh. Abdulsamad I. Rabiu - Memba

(5) Alh. Sani Dauda - Memba

(6) Mrs. Folorunsho Alakija - Memba

(7) Mr. Cosmas Maduka - Memba

(8) Mr. Jim Ovia - Memba

(9) Mr. Wale Tinubu - Memba

(10) Air Marshal J. Wuyep (Rtd) - Memba

(11) Toyosi Akerele, Mai wakiltar Youth/Civil Society - Memba

(12) Alkasim Abdulkadir, Mai Wakiltar Youth/Civil Society/) - Memba

(13) Chief Uche Secondus, Mataimakin Jam’iyyar PDP na Kasa Shiyyar (Kudu) - Memba

(14) Alh. Tijani Tunsah, Mataimakin Jam’iyyar PDP na Kasa Shiyyar (Arewa) - Memba

(15) Alh. Balarabe Musa, Mai Wakiltar Gamayyar Jam’iyyun Adawa (CNPP) - Memba

(16) Alh. Sani Sidi, Shugaban Hukumar Tallfawa ta NEMA - Memba

(17) Farfesa Ben Angwe, Babban Sakataren Hukumar Kwato ‘Yancin Dan Adam ta

NHRC - Memba

(18) Cif (Mrs.) Nkechi Mba, Mai Wakiltar Kungiyar Mata Ta Kasa (NCWS) - Memba

(19) Wakilan Majalisar Koli Ta Musulunci (NSCIA) - Memba

(20) Wakilan Kungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN) - Memba

(21) Air Vice Marshal Tony Omenyi, Mai Wakiltar Hukumar Tsaro Ta Kasa - Memba

(22) CP Salisu Fagge, Mai Wakiltar Rundunar ‘Yan Sanda - Memba

(23) Mr. Sayana Yusuf, Mai Wakiltar Jami’in Binciken Cikin Gida (SSS) - Memba

(24) Wakilan Majalisar Dinkin Duniya - Memba

(25) Wakilan Hukumar DFID - Memba

(26) Wakilan Hukumar USAID - Memba

(27) Wakilan Hukumar Red Cross ta Duniya - Memba

(28) Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF) - Sakataren Kwamiti

Page 19: ÔHAR ABADA ZUCIYAR BILADAMA TA KASANCE …victimssupportfundng.org/hausa.pdfBabu wata alÕumma da bata daba dandana rikici ba. Amma a matsayinmu na mutane da Ubangiji Ya halitta,

19

MEM

BON

IN KW

AM

ITIN

Page 20: ÔHAR ABADA ZUCIYAR BILADAMA TA KASANCE …victimssupportfundng.org/hausa.pdfBabu wata alÕumma da bata daba dandana rikici ba. Amma a matsayinmu na mutane da Ubangiji Ya halitta,